Sakonnin Masu Karatu (2021) (1)

Tallace-Tallace a Wayoyin Android

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 22 ga watan Janairu, 2021.

157

Bayan gama bayani kan Fasahar 5G, na lura sakonni sun taru.  Don haka, daga wannan mako zuwa abin da ya sawwaka, zan amsa wasu daga cikin tambayoyinku.  Ina kara fadakarwa cewa idan an tashi rubuta tambaya, don Allah a daina amfani da gajerun kalmomi, tunda ba hira muke ba.  A rubuta sako a cike.  Kowace kalma a rubuta ta a cike.  Domin ta haka ne kadai zan iya fahimtar tambayar, sannan cikin dacewar Ubangiji in ba da amsar da ta dace.  Amma idan sakon tambaya bai cika ba, zai iya wahala a iya samun gamsasshen amsa.  Don Allah a kiyaye.  Na gode matuka.

—————

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka dai kuma da fatan ana lafiya.  Don Allah ina son sanin wai meye yasa galibin wayoyi masu dauke da babbar manhajar Android idan kana amfani dasu, sai ka rika ganin wasu tallace-tallace suna bayyana daga manhajar da kake amfani da ita, musamman ma idan ka kunna data din wayarka kana mu’amala da Intanet?  Daga ina suke shigowa, tunda kai dai baka dora su a wayar ba?  Muna godiya matuka da irin hidimar da ake damu.  Allah saka da alheri, ya kuma jikan mahaifa.  – Muhammad Kabir Adam, Kano.

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka da addu’o’inku.  Allah kuma ya saka da alheri, amin.  Akwai dalilai biyu manya dake sa ka rika ganin shafukan tallace-tallace a wayarka masu dauke kan babbar manhajar Android.  Amma kafin nan, zai dace kasan cewa, tunda aka fara kirkirar babbar manhajar wayar salula a tarihin fasahar sadarwa ta wayar salula na zamani, ba a taba kirkirar babbar manhaja irin Android ba.  Babbar manhaja ce mai dauke da sarkakiya sosai.  Kuma a kullum dada kayatar da ita ake yi.  Bayan haka, asalin mai wannan babbar manhaja dai, kamar yadda na bayyana a doguwar makalarmu mai take: “Babbar Manhajar Android”, shi ne kamfanin Google.  Duk wani kamfanin wayar salula da kaga ya dora babbar manhajar Android a wayarsa, to, daga kamfanin Google yake samu lasisin yin hakan.  Sannan duk kamfanin da ya samu lasisin dora Android a wayoyinsa, to, yakan kebance ta da wata Android din dake kan wasu wayoyin da ba na kamfaninsa ba, don manufofi na kasuwanci.  Shi yasa, idan ka kalli wayar Samsung mai dauke da Android, da wayar Huawei ko Tecno mai dauke da Android, a Zahiri sai kaga kamar daban-daban suke.  Ko kadan ba haka bane, duk asalinsu daya ne.  Kyale-kyalen kamfani ne ke bambanta su.

Dalilin farko dake sa kana cin karo da tallace-tallace a wayarka musamman idan ka kunna data, yana ta’allaka ne ga kamfanin da ya kera wayar.  Idan wayar nau’in Tecno ce, ko Infinix, ko kuma Itel, to asali daga kamfanin wayar ne.  abin da wannan ke nufi shi ne, idan kana wayar salula  nau’in Tecno ko Infinix, ko Itel, komai girma da tsadarta, sai ka ta cin karo da ire-iren wadannan tallace-tallace.  Haka wayoyin ke zuwa dasu, a dauke a kansu.  Bayan tallace-tallace ma, akwai manhajoji da yawa wadanda a girke suke a kan babbar manhajar wayar, wadanda kamfanin ya tsofa su a ciki.  Mai wayar bazai iya gane inda asalinsu ma yake ba, balle yayi yunkurin cire su.  To me yasa wayoyin Tecno, da Infinix, da Itel, misali, suke zuwa da wadannnan manhajoji masu dauke da tallace-tallace?

- Adv -

Asalin kamfanin dake kera wayoyin Tecno da Infinix da Itel, duk kamfani daya ne.  Shi ne kamfanin “Transsion” dake kasar Sin (China).  Duk da bambancin sunayensu, da yanayinsu a zahiri, kamfani daya ne ke kera su.  Na san mai karatu yana yaba farashin wadannan wayoyi saboda saukinsu, idan ka hada su da na kamfanin Huawei ko Samsung ko Sony.  Wannan haka yake.  Daman wayoyi ne da ake kera su don kasashe masu karancin arziki.  Shi yasa idan kaje kasashe irin su Amurka ko Ingila, zai yi wahala kaga wayar Tecno ko Infinix a can.  A takaice dai, wayoyin Tecno da Infinix da Itel sun yi araha ne saboda akwai kamfanonin dake biyan kudin tallace-tallace, wadanda ake shigar dasu cikin manhajojin wayar.  Kudin da suke biya ne ke sa kamfanin Transsion ke rage farashin wayoyinsa da ake shigo mana dasu.  Kamar sun ba da tallafi (Subsidy) kenan don saukaka farashinsu.  Shi yasa ake shigar da manhajojin cikin babbar manhajar, ta yadda mai amfani da waya bazai iya cire su ko goge su ba.  Sai dai ka hana su bayyana na dan wani lokaci.  Amma da zarar kamfanin ya sabunta bayanansu ta hanyar “Update”, na take zasu sake bayyana.  Abin  da zai iya sa ka goge su ko cire su dai abu daya ne:  shi ne ka farke wayar, ta hanyar “Rooting”.  Idan ka farke ta, to, babu manhajar da baza ka iya cirewa ba.  Wannan dalilin farko kenan.

Dalili na biyu da ka iya sa kaga shafuka ko manhajojin tallace-tallace a wayarka ta Android kuma na iya samuwa ne daga gare ka.  Abu ne sananne cewa muna saukar da manhajoji daga cibiyar manhaja ta Play Store.  Galibi kuma kyauta ne.  To amma, kamar yadda Bahaushe ne ke cewa, araha ba ta ado.  Manhajojin dake Play Store nau’i biyu ne: akwai na kyauta, wadanda za ka iya saukarwa kayi amfani dasu.  Sannan akwai na kudi, wadanda ake iya baka dandano.  Kowanne daga cikinsu na dauke ne da tallace-tallace.  Idan na kyauta ne ka saukar, suna dauke da tallace-tallace.  Domin hanyar da suke amfani da ita kenan wajen rage zafin hidimar da suka yi wajen gina manhajar.  Idan kuma na kudi ne, amma  ba saya kayi ba, nan ma akwai tallace-tallace a cikinsu.

Don haka, wadannan su ne manyan hanyoyin dake shigar da shafuka ko manhajojin tallace-tallace ga wayar salula ta zamani mai amfani da babbar manhajar Android.  Idan ba ka bukatar ire-iren wadannan tallace-tallace masu harzuka mutum, ko dai ka rika kashe data dinka sadda kake amfani dasu, ko kuma ka sayi na kudi, wanda ba ya dauke da tallace-tallace.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

Barka da safiya, da fatan ka tashi lafiya. Ni masoyin karatun shafinka ne a jaridar Aminiya, kuma dan makaranta ne ma’abocin rubutu cikin harshen Hausa.  Ina son in kware ta wurin rubuce-rubuce da kuma sanin ka’idojin rubutun cikin harshen Hausa. Ko za ka taimaka ka hadani da wanda zai rika koya mini ko ta kafar Intanet ko kafar sada zumunta ne? – Edward David: ed30054@gmail.com.

Barka dai Malam Edward.  Da fatan kana lafiya.  Dangane da bukatarka na son ka kware a bangaren tsari da salon rubutun harshen Hausa, wannan abu ne mai kyau, kuma na yi matukar farin ciki da jin haka.  Ina kuma rokon Allah ya agaza maka wajen cinma burinka.  Abu na biyu shi ne bukatar samun wanda zai rika taimakawa wajen baka horo ta hanyar nazarin rubutun da kake yi da manufar gyara da kuma fadakarwa.  Duk da cewa bazan iya wannan aiki ba saboda dalilai biyu, amma zan yi kokarin tuntubar wanda nake kyautata zaton zai iya taimakawa.  Idan Allah Yasa ya amince, zan sanar dakai in Allah Yaso.  Da fatan za a gafarceni a bisa tsaiko da aka samu wajen amsa bukatarka.   A karshe, ina baka hakuri saboda daga baya na fahimci kamar ka yi ta kokarin kirana amma ban daga ba.  Wannan ya faru ne saboda ba na daga kira a layin wayar dake wannan shafi, sai idan nine nace mutum ya kira ni.  Sakonnin tes kawai nake karba.  Dalili kan haka kuwa na sha maimaita shi a wannan shafi mai albarka.  Na gode matuka.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.