Fasahar 5G: Kammalawa

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 15 ga watan Janairu, 2021.

672

Kammalawa

Bayan bayanan da mai karatu yaci karo dasu kan wannan fasaha, da fa’idoji ko amfanin da ake hasashen ribata daga wannan fasaha nan gaba, da siffofinta, da kuma tsarin sadarwar da take dauke dashi mai ban sha’awa da kayatarwa, muddin aka dabbaka su yadda suka kamata, a karshe mai karatu ya ci karo da wasu ra’ayoyi masu rauni da suka shafi jita-jita masu kamshin gaskiya, ko tsagwaron karya kan wannan fasaha.

Da farko dai, na nuna mana cewa babu wani abu na mu’amalar rayuwa wanda ba shi da wani nau’i na cutarwa, komai kankantarsa. Sai dai ace amfaninsa ya dara illarsa, in abu ne da za a iya tantance illarsa, na kusa ko na nesa. Abubuwan ibada, wadanda Allah ya wajabta maka, su ne kadai suke dauke da zallar amfani, babu cutarwa; ta kowane bangare ka kalle su. Don haka, wannan fasaha ta 5G nau’i ne na abubuwan mu’amalar rayuwa, tunda hanya ce ta sadarwa. Kuma tana dauke ne da fa’idoji masu dimbin yawa. Wannan har wa yau ba ya nufin babu wasu nau’ukan illoli tare da ita. Wadannan illoli dai iri daya ne da irin illolin da ake cikinsu a tsarin fasahar 4G da 3G da 2G, in akwai. Ma’ana, iya ingancin wadannan hanyoyin sadarwa da tagomashinsu, iya yadda mutane za su rika shagaltar da kansu dasu, kuma iya yadda yawan shagala dasu ke tasiri wajen lafiyarka, da lokacinka, da mu’malarka da iyalinka, da aikinka ko sana’arka, da addininka ko ibadarka.

A baya na gabatar da doguwar Makala mai take: “Wayar Salula da Tsarin Amfani da Ita.” A cikin wannan Makala, bayan bayani kan siffofi da fa’idojin wayar salula, na kuma kawo mana wasu daga cikin illolin da bayyanarsu da yawaitarsu cikin al’umma ke haifarwa. Wannan ka’idar rayuwa ce. Shi yasa na kawo mana tarihin jita-jita kan hanyoyi da na’urorin sadarwa na baya da na zamanin yau. Don mai karatu yaga cewa duk dai tafarkin daya ce. Kuma al’adar iri daya ce.

- Adv -

Amma karerayin da ake yadawa kan fasahar 5G ita kadai, da wadanda ake ta yadawa kan alakarta da cutar korona, duk karya ce tsagwaronta. Wadanda ke da alaka da makamashin sadarwa mai guba (Ionizing radiation) kuma, har yanzu babu wani bincike ingantacce, amintacce da ya tabbatar da cewa makamashin hasken rediyo da wayar salula ko na’urar yada siginar Intanet ke fitarwa, na hadddasa cutar sankara, ko kashe garkuwan jiki, ko hana haihuwa. Da ace wadannan abubuwa na haddasa wadancan cututtuka, da tuni an samu karuwar yaduwar cutar sankara (Cancer), da karuwar rashin haihuwa (infertility), da karuwar mace-mace akai-akai sanadiyyar kashe garkuwar jikin mutane, a kasashen da suka ci gaba kuma suka fi mu amfani da wadannan na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, nesa ba kusa ba. Amma har yanzu ba a samu karuwar wadancan cututtuka masu alaka da yawan karuwar yaduwa da yawan amfani da wadannan na’urori ko hanyoyin sadarwa ba. Duk da cewa ana samun karuwar cutar sankara a duniya ma baki daya, amma a tsarin bincike ana iya gano dalilin cutar. Har yanzu babu wanda bincike ya tabbatar da cewa suna karuwa ne sanadiyyar hasken makamashin rediyo na wayar salula.

Misali, a kasa mai dauke da mutane miliyan 10, wanda miliyan 8 cikinsu ke amfani da wadannan na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani, dare da rana safe da yamma. Na’urorin nan na girke a gidajensu, da ofisoshinsu, da wayoyinsu na sadarwa. Kuma suka kwashe shekaru 20 suna amfani da wannan hanya ta sadarwa, da wadannan na’urori na sadarwa, ya kamata a ce zuwa yanzu an samu karuwar wadannan cututtuka cikin al’ummar, iya gwargwadon yaduwar hanyoyi da na’urorin sadarwar. Wannan shi ne abin da Cibiyar Binciken Cutar Sankara ta kasar Burtaniya (UK Cancer Research Institute) ta ayyana a shekarun baya sadda ake ta rade-radin cewa sinadaran hasken sadarwar rediyo da wayoyin salula ke fitarwa suna haddasa cutar kansa. Tace har yanzu babu wata alama dake nuna cewa akwai alaka tsakanin wadannan abubuwa biyu. Da akwai alaka tsakaninsu, to, da karuwar amfani da wayoyin salula, da yaduwar hanyoyin sadarwa a kasar Burtaniya sun haddasa karuwar yawan masu kamuwa da cutar sankara a kasar, daidai-wa-daida. Wannan shi ake kira: “Positive Correlation” a ilimin tantance alaka tsakanin abubuwa biyu ko sama da haka, ta hanyar ka’idojin lissafi na zamani.

A daya bangaren kuma, bincike ya gano cewa masu yada wadannan jita-jitan ma suna yin hakan ne don wasu dalilai na harkar tattalin arziki. A cikin shirinsa na musamman mai take: “The 5G Con That Could Make You Sick”, wanda tashar BBC Assignment ta watsa a ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 2020, Tom Wright ya hankado asirin ire-iren wadannan mutane, musamman Dr. Klinhart na kasar Burtaniya, wanda bayan ya gama shirya karerayi kan fasahar 5G, daga baya yazo yace ya samar wa al’umma maganin dukkan wadannan matsaloli. Wannan magani nasa kuwa, wanda ba kwaya bane wanda za a rika sha. Sannan ba hayaki bane da za a rika turarawa. A a, wani surkulle ne a aka nade a ma’adanar bayanai, wato: “Flash Drive.” Shi za ka saya, ka dora a kan kwamfutarka. Wai shi zai tsare ka daga wancan sinadaran makamashin rediyo da na’urar Wi-Fi ke fitarwa.

Farashin wannan “magani” da Dr. Klinhart ke sayarwa a boye dai, ya kai dalar amurka 350. Kwatankwacin N164,500 (Naira dubu dari da sittin da hudu da naira dari biyar) kenan, a canjin Najeriya. Tuni hukumar lafiya ta kasar Burtaniya ta haramta sayar da wannan katin “Flash Drive” a kasar, saboda hukumar dake tantance ingancin kayayyakin da ake samarwa a kasar bata tantance shi ba. Bayan wannan, akwai wanda ya samar da wasu kwayoyi su kuma, wai idan ka sha, za ka samu kariya na har abada daga sinadaran makamashin rediyo na fasahar 5G. Shi ma, kamar na Dr. Klinhart, a boye ake sayar dashi. Domin hukuma ta ce duk wadannan abubuwa sun saba wa ka’idar kimiyya. Don haka ba za su yarda a sayar wa al’umma ba, kada lafiyarsu ta cutu.

A karshe dai, wannan shi ne dan abin da ya samu kan wannan fasaha ta 5G. Saura da me? Mai karatu zai ci gaba da lura da yadda wannan fasaha ke bunkasa, musamman idan aka fara dabbaka ta a Najeriya, da tsarin sadarwata, don samun fa’idojin da ke tattare da ita, da kuma kauce wa mummunar shakuwa da hanyoyi ko na’urorin sadarwa saboda lura da lafiya da lokaci, da iyali, da kuma addini, wanda shi ne jigo.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.