Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (8)

Microsoft Copilot

Idan ka mallaki wannan fasaha ta Copilot Pro, tana iya rubuta maka duk abin da kake son rubuta na rubutu kai tsaye a manhajar sarrafa bayanai na Word.  Idan nazarin bayanai kake son yi mai tsayi, tana iya maka nazarinsa. Ta taƙaita maka shi, sannan ta baka mahimman saƙonnin dake ɗauke cikin rubutun, duk tsayinsa kuwa. – Jaridar AMINIYA, 23 ga Waran Fabrairu, 2024.

60

Na 6: Bayyanar Fasahar Microsoft Copilot

Abu na shida da yayi tasiri a duniyar fasahar sadarwa a duniya cikin shekarar 2023 shi ne bayyanar da Fasahar AI mai suna: “Microsoft Copilot”, wanda kamfanin Microsoft ya fitar a watan Satumba.  Wannan fasaha ta Copilot dai manhaja ce makamanciyar ChatGPT da Google Bard.  A tare da cewa kamfanin Microsoft ya ƙara inganta manhajar neman bayaninsa mai suna “Bing”, inda ya ɗora mata fasahar AI ta musamman, don bata damar zaƙulo bayanai cikin sauƙi, sai dai, fitar da Fasahar Copilot ya daɗa sauya fasalin samar da bayanai cikin sauƙi da basira ga masu amfani da kwamfutocin dake ɗauke da babbar manhajar Windows.

Wannan fasaha ta Copilot dai an samar da ita ne nau’i daban-daban. Akwai wacce ke ɗauke kan babbar manhajar Windows, wacce har yanzu take kan zubin gwaji (Preview).  Da wannan manhaja kana iya umartan kwamfutarka ta buɗo maka wuraren da bayananka ke ajiye a cikin kwamfutarka.  Haka kana ina neman bayanai kai tsaye daga Intanet.  Sannan, har wa yau akwai wannan fasaha akan manhajar burauza na Microsoft Edge.  Kana iya sa fasahar Copilot ta maka nazarin bayanan dake kan shafin da ka buɗo cikin sauƙi.  Haka ma idan wata jakar bayani ka buɗo mai tsayi, kana iya sa ta taƙaita maka bayanan dake don fahimtarsa cikin sauƙi. Sannan a karon ƙarshe, tana ɗauke da siffofin Fasahar ChatGPT 3.5, da zubi na 4 ma.

Ana shiga watan Nuwamba sai kamfanin Microsoft ya narkar da manhajar Bing Chat cikin Microsoft Copilot kai tsaye.  Daga nan ne aka samu ƙaruwan nau’in Copilot uku.  Na farko ita ce Fasahar Copilot na gama-gari, wadda ke ɗauke a shafi na musamman dake: https://copilot.microsoft.com.  Kana iya mallakar wannan fasaha cikin sauƙi idan kana da adireshin Imel na kamfanin Microsoft; Hotmail, ko Outlook.  Idan ba ka dashi, kana iya yin rajista kyauta.  Sannan ko akan wayar salula ne kana iya zuwa shafin kai tsaye a wancan adireshi da na zayyana.  Idan kuma manhajar Fasahar Copilot kake buƙata ta wayar salula, kana iya zuwa cibiyar manhajoji na Play Store idan wayar Android kake amfani da ita. Ko kuma Apple Store, idan kana amfani da wayar iPhone ne.  Kawai ka rubuta: “Copilot”, nan take za a cillo maka ita, sai ka sauke ka loda wa wayarka.

- Adv -

Nau’i na biyu ita ce Fasahar Copilot Pro, wacce ke ɗauke da dukkan siffofin Fasahar ChatGPT 4.  Sai dai wannan na kuɗi ne.  Sai mai dala zai mallaketa.  Wannan nau’i tana ɗauke da abubuwan al’ajabi masu ɗimbin yawa, musamman ga wanda ya iya ko ya saba amfani da manhajar sarrafa bayanai na Microsoft, wato “Word”, ko na lissafi da ƙididdigar, wato: “Excel”, ko na gabatar da bayanai, wato: “PowerPoint”.  Haka ma, idan ka saba amfani da manhajar gudanar da tarurruka na Microsoft mai suna “Microsoft Teams”, za ka ga abin al’ajabi idan ka mallaki Copilot Pro.  Ga mai buƙata, dala 30 ne a duk wata.  Kusan naira dubu talatin da biyar kenan a canjin Najeriya.

Idan ka mallaki wannan fasaha ta Copilot Pro, tana iya rubuta maka duk abin da kake son rubuta na rubutu kai tsaye a manhajar sarrafa bayanai na Word.  Idan nazarin bayanai kake son yi mai tsayi, tana iya maka nazarinsa. Ta taƙaita maka shi, sannan ta baka mahimman saƙonnin dake ɗauke cikin rubutun, duk tsayinsa kuwa.  Haka idan bayanai aka aiko masu alaƙa da kuɗaɗe, kamar cinikin kamfani, ko bayanan sayayya da cinikin shago, ko adadin yawan abubuwa, duk wannan fasaha tana iya markaɗa maka su, ta fitar maka da mahimman bayanai kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba.  Idan gayyatarka aka yi wani taro don gabatar da jawabi kan wani maudu’i na ilmi, watakila ba a sanar dakai ba sai cikin ƙurewar lokaci.  Wannan fasaha ta Copilot Pro na iya ƙirƙiro maka bayanai a yanayin da za ka iya gabatar dasu cikin sauƙi ta amfani da manhajar PowerPoint.  Har da hotuna masu alaƙa da bayanan dake kan kowane shafi, duk za ta iya kawo maka.  Ya rageka a matsayinka na wanda yasa me zai gabatar, ka ƙara ko rage abin da kake ganin babu ko bai kamata ya shiga cikin abin da ake son ka gabatar ba.  Haka idan taro kake son gudanarwa ta hanyar manhajar Microsoft Teams, duk yawan masu halartar wannan taro, ba ka buƙatar rubuta me kowa da kowa ya faɗa.  Kawai ka kira ta kafin ku fara.  Duk tattaunawar da kuka yi, a ƙarshe tana iya taƙaita maka abin da kowa ya faɗa.  Idan ma akwai waɗanda aka ɗora musu alhakin gudanar da wasu abubuwa a taron, duk za ta tantance su, sannan ta rairayo maka mahimman abubuwan da taron ya ƙunsa.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, sharaɗin mallakar wannan fasaha shi ya zama ka sayi ko kana amfani da manhajar Microsoft 365, ko “Personal” ko “Family”.  Wannan manhaja ita ce mafi sabunta, kuma sai kana da ita za ka iya fa’idantuwa da fasahar Copilot akan manhajar Word, da Excel, da PowerPoint, da Teams da sauran makamantansu.  Farashin Microsoft 365 dai daga dala saba’in ne ($70) idan tsarin “Personal” kake so na shekara guda, ko dala bakwai ($7) a duk wata, idan biyan na shekara ya maka yawa.  Idan kuma nau’in “Family” kake so, a shekara dala ɗari ne ($100), ko dala goma ($10) a duk wata.  Amma wanda ke da Microsoft Office (Word, da Excel, da PowerPoint) 2016, ko 2013, ko 2010, ko 2007 duk ba za su ɗauka ba.  Ko da kuwa gangariya ne daga kamfanin Microsoft ka saya ko dillalansu.  Domin an gama yayinsu tuni.

Sai nau’in Copilot na kamfanoni ko hukumomi.  Wannan shi suke kira: “Copilot 365 for Business”, ko “Ko Microsoft Copilot for Microsoft 365”.  Wannan an tanade ta ne ga kamfanonin da ma’aikatansu suka ɗara 300.  Kowanne daga cikin ma’aikatan na iya mallaka da kuma amfani da wannan fasaha a manhajar Microsoft 365 (irin su Word, da Execel, da PowerPoint).  Bayan amfani da ita wajen rubutu da nazari, wannan fasaha tana iya ƙirƙirar hotuna sama da 100 a yini guda idan kana buƙata.

A taƙaice dai, bayyanar wannan fasaha na cikin abubuwan da suka sauya duniya da tsarin samarwa da ta’ammali da bayanai a duniya baki ɗaya, cikin shekarar 2023.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.