Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (9)

Tsoron Wankiya

A taƙaice dai, abu na bakwai daga cikin abubuwa tara da fasahar AI ta zama dalili wajen sauya duniya a shekarar 2023 shi ne, tunanin cewa waɗannan fasahohi na AI dake samar da bayanai kai tsaye suna iya tasiri wajen rage wa ɗalibai himma ta hanyar samar musu da maƙaloli da rubutu na musamman da suka shafi karatunsu, wanda hakan zai sa a rasa inganci da nagartar ilmi.  – Jaridar AMINIYA, 1 ga Waran Maris, 2024.

8

Na 7: Tsoron Wankiya

Daga cikin manyan dalilan da suka sa masana yin ɗari-ɗari da fasahar samar da bayanai ta AI (Generative AI) musamman fasahar ChatGTP, akwai tsoron rushe ƙimar ilimi da mayar da jami’o’in duniya zuwa kango.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, kasancewar wannan fasaha ta AI na iya rubuta wa ɗalibi maƙala da ƙasida da bincike na musamman da ake son ɗalibin ya gabatar kafin samun shedar kammala karatun jami’a, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, yasa ake ganin nan gaba idan tafi tafi nisa, malaman jami’a ba za su iya tantance tsakanin rubutun da ɗalibi yayi da kansa, bayan gudanar da bincike ba, daga rubutun da manhajar fasahar AI (irin su ChatGPT, ko Google Gemini, ko Microsoft Copilot) suka antayo masa ba.  Idan aka zo wannan lokaci kuwa, ko tantama babu, ƙimar ilimi ya narke.  Komai ya lalace kenan. Ɗaliban za suyi zaman dirshan ne a makarantu; ba karatu, sai dai wankiya (Plagiarism).

Gab da ƙarshen shekarar 2023 ne wani malamin jami’a mai suna Fafesa Jared dake jami’ar A&M ta Jihar Texas na ƙasar Amurka yayi kwarmato, cewa gaba ɗayan ɗaliban da yake karantarwa suna amfani da fasahar ChatGPT ne wajen samar da bayanan karatunsu.  Hakan ya faru ne kuwa sadda ya kwafi samfurin rubutun da suka aiko masa, ya loda a shafin fasahar ChatGPT don ta tantance masa, shin ɗan Adam ne ya rubuta ko kuwa fasaha ce mai ƙirƙirarriyar basira ta rubuta?  Nan take manhajar tace masa ai dukkan abin da ya kwafo mata, ba ɗan adam bane ya rubuta, na’ura ce mai basira.  Nan take ya tsala ihu, duk duniya ta ɗauka, cewa ɗaliban jami’a sun fara amfani da manhajar fasahar AI wajen samar da bayanai na bincike, ba su suke rubutawa da kansu ba.  Wannan bai da banbanci da wanda aka bashi aikin gida, ko aikin gudanar da bincike na musamman, sai kawai ya ɗauko littafi na musamman da aka rubuta kan maudu’in, ya kwafo komai da komai yake buƙata, ya miƙa wa malami.

Wannan kwarmato da wannan Malamin jami’a yayi ya haifar da cece-kuce a duniya nan take.  Kafafen sadarwa da yaɗa labaru suka ɗauka nan take. Ashe ana iya amfani da wannan sabuwar fasaha wajen yin cogen karatu kenan?  In kuwa haka ne, ashe nan gaba ƙimar karatu musamman a jami’o’i zai ragu kenan, in ma bai zube ba.  Sannan, a hankali makarantu za su fara zama kango kenan.  Wannan shi ne babban dalilin da yasa wannan kwarmato na Farfesa Jared ya haifar da cece-kuce a duniya.

To amma bayan wasu ‘yan kwanaki, bincike ta hanyar gwaji da wasu suka gudanar ya tabbatar da cewa wannan fasaha ta ChatGPT da wancan Farfesa yayi amfani da ita wajen ƙoƙarin gano ingancin rubutun ɗalibansa, ba ta iya tantancewa tsakanin rubutun da tayi, da wanda ɗan adam ya rubuta da hannunsa.  A wancan lokacin kenan.   Duk da cewa a sadda Malamin ya nemi tantance rubutun ɗalibansa akwai manhajoji dake shafukan Intanet masu iƙirarin tantance rubutun fasahar AI da wanda ɗan adam ya rubuta, don kauce wa coge cikin harkokin rayuwa da kasuwanci.

- Adv -

Don ƙoƙarin tabbatar da gaskiya ko rashin tabbacin wannan iƙirari na cewa fasahar AI ba ta iya tantancewa tsakanin rubutun da ɗan adam yayi da wanda ta rubuta, nan take aka gudanar da gwaji kan hakan. Inda masu gwajin suka zauna suka rubuta maƙala na musamman da hannunsu, sai suka bijiro wa manhajar fasahar ChatGPT, suna masu tambyarta wanda ya rubuta wannan maƙala.  Nan take tace ita ce.  Sai ya tabbata cewa lallai fasahohin AI na samar da bayanai ba sa iya tantancewa tsakanin rubutun da ɗan adam yayi da wanda su suka rubuta da kansu. Wannan gwaji ne yayi sanadiyyar lafawar kwarmaton da Farfesa Jared ya haifar a lokacin.

Gwajin Da Na Gabatar

Don ƙarin tabbaci, ni kaina na gudanar da gwaji makamancin wannan, cikin watan da ya gabata.  Inda na zauna na rubuta maƙala ta musamman na ɗora wa fasahar AI na Google, wato Google Bard, ko Google Gemini, kamar yadda aka sauya sunan a yanzu, don ta tantance mini wanda ya rubuta maƙalar.  Nan take tace mini, tantance marubucin rubutu ta wannan hanya abu ne mai wahala a gare ta, saboda wasu dalilai masu yawa.  Amma, a cewarta, akwai hanyoyin da za a iya bi don gano wasu alamomi da ke tabbatar da marubucin, duk da yake ba ɗari bisa ɗari ba.

Ta sanar dani cewa, rubutun da na’urar AI yana shan bamban da na ɗan adam sosai ta ɓangarori da dama.  Na farko dai, duk abinda fasahar AI ta rubuta ba a cika samunsa da alaƙanta zance da hali ko nasabar zance da lokaci ba.  Wannan shi ne abin da a turanci ake kira: “Context”.  Tana zuba rubutu ne kawai sake waiwai.  Sannan ba a samun alamar tausayi, da fushi, ko raha irin wanda ya keɓanci tsarin zancen ɗan adam a cikin abin da take rubutawa.  Ƙari kan haka, tace a wasu lokuta ana samun alamun “shirme” da “wauta” ko “kuskure” wajen amsar da take rubutawa.  Wannan shi ake kira: “AI Hallucinations”.  Kamar yadda ɗan adam kan yi shirme wajen ba da amsa, musamman idan bai fahimci ma’ana da lafuzzan tambayar da aka masa ba.  Haka ita ma wannan fasaha take; kana iya mata tambaya, amma wajen ba da amsa ta aiko maka wani abu daban da ba shi da alaka da abin da ka tambaya.

Hakan na faruwa ne saboda ba ta iya fahimtar yanayin da kake magana a kai, don ba ɗan adam bace.  Sannan idan ma abin da kake magana akai yana da alaƙa da tarihi, ba lalai bane ta iya tantance wani ɓangare ne na tarihin.

A taƙaice dai, abu na bakwai daga cikin abubuwa tara da fasahar AI ta zama dalili wajen sauya duniya a shekarar 2023 shi ne, tunanin cewa waɗannan fasahohi na AI dake samar da bayanai kai tsaye suna iya tasiri wajen rage wa ɗalibai himma ta hanyar samar musu da maƙaloli da rubutu na musamman da suka shafi karatunsu, wanda hakan zai sa a rasa inganci da nagartar ilmi.  Duk da cewa hakan ba gaskiya bane kai tsaye, amma ci gaba da bincike wajen inganta waɗannan fasahohi nan na iya sa a samu hakan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.