Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (11)

Korar Sam Altman Daga Kamfanin OpenAI

Watarana cikin watan Nuwamba, kwatsam aka wayi gari kwamitin zartarwa na kamfanin OpenAI ya kori Sam Altman daga kamfanin baki ɗaya.  Wannan lamari ya ta da hankalin duniya gaba ɗaya. – Jaridar AMINIYA, 15 ga Watan Nuwamba, 2024.

5

Na 9: Korar Sam Altman Daga OpenAI

Tagwayen al’amuran da suka sa fasahar AI, sanadiyyar fasahar ChatGPT, ta sauya duniya a shekarar 2023 su ne, korar Sam Altman, wanda shi ne shugaba kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka samar da fasahar ChatGTP, da kuma kai ƙarar kamfanin OpenAI da shahararren kamfanin jaridar Amurka mai suna New York Times yayi.  Waɗannan tagwayen al’amura dai sun faru ne tsakanin watan Nuwamba da Disamba na shekarar 2023.  Mu fara da korar Sam Altman tukun.

Kamar yadda bayani ya gabata a maƙalolin baya, kamfanin OpenAI ne ya tsara kuma ya samar da fasahar ChatGTP.  Wannan ita ce fasaha ta farko cikin nau’ukan manhajojin samar da bayanai na AI, wato Generative AI ko kuma AI ChatBot.  Shugaban wannan kamfani dai wani shahararren matashi ne mai suna Sam Altman, ɗan ƙasar Amurka, wanda a baya ya shugabanci wasu ƙananan kamfanonin sadarwa masu tasiri a duniya.  Shi ne wanda ya samar da World Coin, ɗaya daga cikin nau’ukan kuɗin zamani a yau.  A matsayinsa na shugaban wannan kamfani, ya samu ƙima sosai a idon duniya gaba ɗaya, ba ma duniyar fannin sadarwa kaɗai ba.  Kuma kamar yadda muka sani, ƙimar shugaba na tabbatar da shahara da ƙimar kamfani a idon abokan hulɗa.  A wannan ɓangare, kusan dukkan masu ta’ammali da fasahar ChatGPT ana ƙiddige su a matsayin abokan hulɗar wannan kamfani ne.

Watarana cikin watan Nuwamba, kwatsam aka wayi gari kwamitin zartarwa na kamfanin OpenAI ya kori Sam Altman daga kamfanin baki ɗaya.  Wannan lamari ya ta da hankalin duniya gaba ɗaya.  Kafafen yaɗa labaru sun ta rubuce-rubuce da sharhi da kuma hira da masana harkar sadarwa a sassa daban-daban na duniya, kan wannan lamari, tare da tasirin hakan wajen karɓuwan wannan kamfani.  Hukumar gudanarwar kamfanin dai bai ba da wani dalili tsayayye kan wannan kora da yayi wa Sam Altman ba.  Duk da cewa daga baya hukumar gudanar da kamfanin ya sanar da cewa wai dalilin korarsa shi ne, Sam yana tafiyar da kamfanin ne a duƙunƙune; ma’ana, ba ya shawartan kowa.  Wanda hakan, a cewar kwamitin, alama ce ta rashin gaskiya.

Sai dai kuma, a ɗaya ɓangaren, duniya bata karɓi wannan uzuri nasu ba.  Shi yasa kwanaki kaɗan da korarshi, nan take kamfanin Micirosoft, wanda shi ma yana da jari a kamfanin OpenAI, ya tallata wa Sam Altman buƙatar ɗaukansa aiki a kamfanin.  Ana cikin haka, sai ma’aikatan kamfanin OpenAI su 500 suka yi wa kwamitin gudanarwar kamfanin bazarar cewa muddin ba a dawo da Sam Altman a matsayin shugaban kamfanin ba, to, za su bar aiki gaba ɗayansu.

- Adv -

Wannan lamari ya haifar da cece-kuce a duniya baki ɗaya.  Ayyuka suka tsaya cak a kamfanin OpenAI, sannan kafafen yaɗa labaru suka yi caa a kan kwamitin gudanarwar kamfanin. Daga mai sharhi, sai mai suka, sai mai barazanar cewa nan da wasu lokuta kamfanin na iya durƙushewa.  Ana cikin hakan ne sai kwamitin gudanarwar ya soke korar da yayi wa Sam, aka dawo dashi matsayinsa.  Har zuwa wannan lokaci da nake wannan rubutu, babu wani bayani tabbatacce kan dalilin korar da aka masa.

Lamari na biyu da ya ɗauki hankalin duniya a ƙarshen shekarar 2023 shi ne sammacin da kamfanin jaridar The New York Times na ƙasar Amurka yayi wa kamfanin OpenAI, kan zargin kamfanin da yin amfani da tarin bayanan da kamfanin jaridar ya wallafa a baya wajen “gwaji” da “koyar” da fasahar ChatGPT yadda za ta gudanar da aikinta, musamman wajen tsara rubutu, da ƙirƙirar samfurin rubutu daban-daban, a lokacin da aka gina manhajar.  Kamfanin jaridar dai yana son a biya shi biliyoyin dala ne sanadiyyar amfani da tarin wallafaffun bayanansa da aka yi ba tare da izni ba.

Kamar yadda bayani ya gabata a baya, dukkan waɗannan manhajoji na samar da bayanai suna iya gudanar da aikinsu ne ta hanyar tarin bayanai da ake ciyar dasu.  Kamar mutum ne kana son ɗabi’antar dashi kan wata ɗabi’a, sai ka riƙa bijiro masa da hotuna ko bidiyo ko bayanan dake ɗauke da siffofin da kake son ya ɗabi’antu dasu.  Wannan taƙaitaccen misali ne. Amma a zahiri abin ya wuce haka.

Wannan labari ya karaɗe duniyar sadarwa gaba ɗaya cikin watan Disamba har zuwa Janairun sabuwar shekarar 2024.  A nasa ɓangaren, kamfanin OpenAI yace wannan zancen banza ne.  Domin da daɗewa yana tattaunawa da kamfanin jaridar kan yadda za a fahimci juna dangane da wannan batu, da kuma yarjejeniyar ma da yake shirin yi dashi don alaƙar kasuwanci nan gaba.  Don haka, cikin lokaci guda, ba tare da sanin shi (OpenAI) ba, aje kotu a cillo masa takardan sammaci, ba a masa adalci ba.

Bayan ‘yan kwanaki da karɓan wannan sammaci ne kamfanin OpenAI ya ba da nasa bahasi kan wannan lamari.   Inda yace, in dai kan batun yin amfani da wallafaffun bayanan kamfanin jaridar New York Times ne wajen koyar da wannan sabuwar fasaha tasa, babu wata doka da ya taka.  Domin ya yi amfani ne da irin bayanan da kamfanin ya ɗora don amfanin kowa a Intanet.  Ire-iren waɗannan bayanai su ake kira: “Public available data”, wanda kowa na iya isa gare su ta hanyar da aka saba, ya karantu, ko saukar, ko yin amfani dasu kai tsaye.  Abu na biyu kuma, kamfanin OpenAI yace ba asalin bayanan jaridar bane fasahar ChatGPT ke miƙa wa mutane idan sun tashi buƙata ba.  A a.  Sarrafaffun bayanai ne da aka tace aka samar da ma’anoni daga gare su, sannan aka fitar da wasu bayanai sababbi ɗauke da wancan ma’ana da aka tace daga waɗancan bayanai na asali.

A ƙarshe dai, har yanzu kotu bata fara sauraren wannan ƙara na kamfanin jaridar The New York Times ko ba.   Sai dai kuma, ga dukkan alamu babu inda wannan shari’a za ta je.  Domin hujjojin da kamfanin OpenAI ya bayar na cewa ya daɗe yana tattaunawa da kamfanin jaridar kan al’amura masu alaƙa da wannan zance, yana nuna akwai daɗaɗɗiyar alaƙa a tsakaninsu.  Sannan, bayanan da kamfanin jaridar ke cewa anyi amfani dasu ba tare da izni ba, su ne dai sauran kamfanonin da suke ƙirƙirar manhajojin samar da bayanai na AI, irin su ChatGPT ɗin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.