Sakonnin Masu Karatu (2021) (6)

Bayani Kan Manhajar "Podcast"

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 26 ga watan Fabrairu, 2021.

674

Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan alkairi a gareka. Don Allah ka mini karin bayani akan wannan manhaja ta “Podcast”.  Sako Daga Aminu Adamu Malam-Madori A Jahar Jigawa. – ahmedadamummr@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aminu.  Ina godiya matuka.  Abin da Kalmar “Podcast” ke nufi shi ne: tsari ne na gabatar da shirye-shiryen rediyo cikin sauti, wanda mai sauraro zai iya saukewa don saurare a kowane lokaci yake bukata.  Wannan shi ne ma’anar “Podcast”.  Ka iya cewa nau’i na tashar rediyo (mai rajista ko mara rajista) da mutum zai iya budewa don yada ilmantarwa, ko fadakarwa, ko nishadantarwa ga jama’a a Intanet.  Wato dole ne tashar ta zama a Intanet take.  Kuma shirye-shiryen na iya zama a kullum ko duk sadda mai tashar ya samu damar gabatarwa.  Kamar yadda Shirin na iya zama kai tsaye (Live Podcast), ko kuma wadanda ake tarawa don saurare a kowane lokaci.  Zai iya zama na kudi ne (Premium Podcast), ko na kyauta (Free).

Bayan haka, akwai manhajojin Podcast na wayar salula, wanda mai karatu zai iya saukarwa don sauraren shirye-shiryen da suke dauke dasu, kyauta.  Galibi cikin harshen Turanci ne ko wasu yaruka.  Ire-iren wadannan tashoshi cikin harshen Hausa basu yadu sosai ba.  Galibin manyan tashoshin gidajen rediyo da talabijin da shahararrun kamfanonin jaridu na duniya duk sun mallaki manhajoji da tashoshin yada shirye-shirye na musamman a tsarin Podcast.  Tashar BBC, misali, tana da tashoshin Podcast da dama da mai saurare zai iya saukarwa ya amfana dasu.  Daga ciki akwai manhajar “BBC Documentary”, da “BBC Inquiry”.  Hatta kamfanin Google shi ma yana da nasa manhajar mai suna: “Google Podcasts”, wanda ke kunshe da tashoshin Podcast na wasu daban, ba wai na kamfanin Google din ba.  Wadannan guda ukun da na zayyana duk ina amfani kuma ina amfana dasu.  Sai na hudu cikin wadanda nake amfani dasu, shi ne: “CastBox”.  Wannan manhaja ta “CastBox” dai hadaka ce ta tashoshin Podcast masu dimbin yawa; jakar magori ce, a takaice.  Kusan dukkan tashoshin Podcast da ake ji dasu dai a yanzu tana dauke dasu.  Don haka, idan kana bukatar madauki guda da zai gamsar dakai, kana iya saukewa.

A karshe, Podcast na dauke ne da shirye-shirye da ake gabatar dasu kan mau’du’i daban-daban.  Ya Allah na siyasa ne, ko lafiya, ko raha, ko tattalin arziki da dai sauransu.  Wasu ma zaka samu suna dauke ne da wani fanni takaitacce, kuma bayan mai Shirin yana gabatar da bayanan, zuwa wani lokaci sai kawai ya rufe tashar.

Wannan, a takaice, shi ne abin da zan iya cewa dangane da manhajar Podcast.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alkhairi kuma yaya aiki? Don Allah ina son ayi min cikakken bayani akan 5G Network. Da kuma:  Menene 5G network?  Shin, a yanzu haka ana amfani da shi a duniya? Wace irin waya ce za ta iya amfani dashi? Sannan, wannan fasaha yana da illa ga lafiya ko babu?  Yaya yanayinsa yake da kasarmu Nigeria? Mene ne bambancinsa da 4G?  Sannan akwai 1G da 2G?  Sako daga Idris Ghali Abdu Bichi kano state: idreesghaliabdu@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Idris.  Saboda tsawon lokaci da na dauka ban waiwaye akwatin wasiku ba, wanda hakan yasa na kasa cin karo da wannan sako naka, ina sanar dakai cewa tuni na gama bayanai kan wannan sabuwar fasaha.  Kuma makalolin sun bayyana ne a wannan shafi, wanda ina sa ran tuni ka amfana da abin da ya samu.  Idan ba a sa’ar kaci karo makalolin ba, nan da makonni biyu masu zuwa zan gama dora makalolin dake kasa zuwa kan shafin sadarwa na musamman da na gina don adana dukkan rubutun da nake gabatarwa a wannan shafi, mai suna “Taskar Baban Sadik”.  Da zarar na dora ragowan makalolin dake kasa, wanda ciki har da na fasahar 5G, zan sanar, don a samu damar ziyarta da amfanuwa da dan abin da ya samu.

Da fatan za a mini uzuri saboda tsaiko da aka samu.  Allah sa mu dace baki daya, amin.  Na gode.

Assalamou alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Sunana Moussa daga Maradi. A gaskiya ina jin dadin karatutukanka.  Allah ya kara basira.  Don Allah idan ba damuwa zan so ka turo mini kasidun da ka rubuta kan dabarun yan dandatsa. – Touré Moussa: tm3495579@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Moussa.  Kamar yadda na sanar a lokutan baya, yanzu na daina aika makaloli ta hanyar Imel, saboda akwai inda na tanadi dukkan makalolin kuma za a iya kaiwa gare su cikin sauki, musamman ma kai da kake wajen Najeriya.  Ina godiya da bibiyarmu da kake yi tsawon shekaru.  Allah bar zumunci, amin.  Kana iya riskar makalolin dake da alaka da bukatarka a wannan adireshi dake Taskar Baban Sadik, wato: https://babansadik.com/mu-leka-duniyar-yan-dandatsa-hackers-1/.  Idan ka gama karanta wannan Makala, a can kasa za ka ga ci banta.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.