Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (2)

Misalan Fasahar “AI” a Intanet da Wayar Salula

Akwai manhajoji da tsare-tsare birjiki a wayoyinmu na salula, kuma tuni mun daɗe muna amfani da manhajoji ko wasu na’urorin dake ɗauke da wannan fasaha. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 12 ga watan Janairu, 2024.

19

Misalan Fasahar “AI” a Intanet da Wayar Salula

Tuni an fara amfani da wannan fasaha a aikace, kamar yadda na san masu karatu zasu iya shaidawa daga misalan dake tafe a wannan sashe.  Akwai manhajoji da tsare-tsare birjiki a wayoyinmu na salula, kuma tuni mun daɗe muna amfani da manhajoji ko wasu na’urorin dake ɗauke da wannan fasaha.  Ta ɓangaren sadarwa, wanda shi ne yafi yaɗuwa, akwai manhajoji masu fasaha (Intelligent Apps) a wayoyinmu na salula ko kwamfuta, masu ɗauke da wannan tsari.

Misali, wayoyin iPhone na kamfanin Apple, suna ɗauke da wata manhaja mai suna: “Siri”, wacce ke iya fahimtar dukkan abubuwan da kake gudanarwa a wayarka, da wuraren da kake ziyarta, da sadda kake fita gida da sadda kake dawowa aiki, da mutanen da kake yawan kira, da waɗanda kake aika musu sakonnin tes, duk tana tantance su.  Haka idan akwai wasu abubuwa da ka rubuta su a kalandar waya don gudanar da wasu abubuwa, da zarar lokacin ya yi, nan take za ta tunatar dakai ta hanyar murya. Idan wani kake son kira, da zarar ka umarceta da yin hakan, da kanta za ta kira maka shi kai tsaye.  Idan ka tambayeta inda ya kamata kaci abinci, nan take za ta yi nazarin inda kake, ta lalubo maka wuraren cin abinci a unguwar da kake.  Abubuwan da take yi suna da yawa.

Daga cikin ire-iren waɗannan ƙananan manhajoji masu fasaha akwai na kamfanin Microsoft mai suna: “Cortana”, wacce ke iya gudanar da irin wadancan ayyuka na “Siri”.  Duk da cewa kamfanin Microsoft ya da dakatar da amfani da wannan manhaja a shekarar 2023, sai dai duk ɗabi’unsu ɗaya ne; komai kake yi a kwamfuta ko wayarka tana lura dasu, kuma da zarar ka nemi wasu bayanai, nan take za ta gabatar maka.  Idan ma bata samu ba, za ta sanar dakai.  Idan wata kalma ce kake son a nemo maka ma’anarta, nan take za ta hau Intanet ta nemo maka.  Idan so kake ta baka shawara, abu ne mai sauƙi.  Za ka iya yin hira da ita tsaf, kamar yadda kake hira ko zance da abokinka.

- Adv -

A ɓangaren kamfanin Google, akwai manhajar “Google Assistant” ko “Google Voice Search”, wacce ita ma ke da ire-iren waɗancan dabi’u, har ma da ƙari.  Wannan manhaja mai fasaha na Google, kasancewar kamfanin Google uwa ce a fannin zaƙulo bayanai da sarrafa su, ɗabi’unta suna da ban mamaki.  Tana iya tambayarka abin da kake son yi, cikin sautin mace ko namiji. Idan kace mata so kake ka karanta jaridu, nan take za ta nemo maka waɗanda ke ƙasarka, ko inda kake ko duk inda kake so, ta baje maka su.  Ba wannan kaɗai ba, tana ma iya taya ka karanta su.

A ɓangaren neman bayanai kuma, manhajar “Google Search” gaba ɗayanta tana dogaro ne da wannan tsari ta shahararriyar hanyar da ake kira: “Recommendation System”, wato tsarin dake iya hasashen abin da kake nema, tare da shawarta maka ko bijiro maka da abin da ke da alaƙa da wanda kake nema.  Idan kai ɗan Najeriya ne misali, sai ka buɗo shafin Google daga https://www.google.com, da zarar ka fara rubuta kalma ko jumlar da kake son neman bayanai a kai, nan take manhajar za ta hankalci abin da kake rubutawa, tana haɗa alaƙa tsakaninsa da abin da wasu ko kai, a baya, ka taɓa rubutawa.  Idan sun dace, kafin ka gama rubutawa ta aiko maka cikakken jumlar ko kalmar da kake son tambayowa, tare da wasu kalmomi ko jumloli masu kama dasu.  Wannan duk aikin Fasahar AI ne.

Kamfanin Amazon, babban shagon sayar da kayayyaki mafi girma a Intanet a duniya, yana da nau’in manhaja mai fasaha mai suna: “Alexa”.  Wannan manhaja tana ɗauke ne a shafinsa na Intanet da manhajarsa ta wayar salula, sannan a wasu na’urorin sadarwa da yake dashi masu suna: “Amazon Kindle”.  Kana iya amfani da muryarka wajen bata umarni, ka saurari labarai da bayani kan yanayi da sauransu.  Wannan manhaja, da shi kanshi gidan yanar sadarwar na Amazon, a maƙare suke da wannan Fasaha ta AI.

Idan muka koma dandalin Facebook ma haka lamarin yake.  A taƙaice ma dai, wannan mahalli a cike yake da wannan fasaha.  Dandalin Facebook an gina shi ne ta dukkan ɓangarorinsa da wannan fasaha ta AI.  Wannan tsari na girke ne a cikin babban injin da ke sarrafa Dandalin Facebook mai suna: “Facebook Algorithm.”  Shi yasa ma da zarar ka gama rajista, a matsayinka na sabon mamba, nan take sai kaga an bijiro maka da hotuna da sunayen mutanen da ka sansu a zahirin rayuwa; watakila ma anguwarku ɗaya, ko kunyi makaranta ɗaya, da dai sauransu.  Ba maita bane, injin na amfani ne da bayanan da ka bayar, sai ya gina hasashe a kan cewa, “Tunda makaranta kaza kayi, kuma a gari ko ƙasa kaza aka haifeka, to, ba makawa za ka sanin wane da wance da suke mazauna garin ko suka halarci makarantar da ka halarta.”  Kashi 90 cikin 100 na abubuwan da kake gani a dandalin facebook na bayanai, duk wannan inji mai suna: “Facebook Algorigthm” ne ke sarrafa su.  Tun daga tallace-tallace, da zauruka da ake bijiro maka (Suggested Groups), har zuwa labaran da kake gani idan ka hau shafinka na Facebook, duk wannan injin mai suna Facebook Algorithm ne ke aiwatar dasu.

A ƙarshe, galibin wayoyin salula da kwamfuta yanzu suna zuwa ne da fasahar tambarin yatsu (Biometric Lock/Fingerprint), wacce da zarar ka shafa ɗan yatsanka sai kawai ta buɗe, ba sai ka yi ta hanƙoron shigar da kalmar sirri ba.  Haka akwai masu zuwa da fasahar buɗe kwamfuta ko wayar salula ta amfani da fuska (Facial Lock/Unlock).  Galibin wayoyin salula na zamani a yau ana ƙera su ne da waɗannan nau’ukan fasahohi na kariya. Suna iya tuna mutanen da kafi yawan kiransu, ko aika musu saƙon tes ko Imel cikn sauƙi.  An ɗabi’antar da wayar ne tun asali da irin wannan siffa, ta amfani da wani tsarin koyo-mara-‘yanci da ake kira: “Supervised Learning”, ƙarƙashin fannin “Machine Learning” da bayaninsa ya gabata a baya.  Dukkan waɗannan tsare-tsare sun samu ne ta hanyar wannan fasaha ta “Artificial Intelligence”, wato: “AI”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.