Hanyoyin Cin Gajiyar Fasahar “Artificial Intelligence” (4)

Asalin bayani shi ne inda manhajar ta ciro ko ta markaɗo amsar da ta baka.  A farkon bayyanan waɗannan manhajoji, kai tsaye kawai suke ba ka amsar tambaya, babu marji’i.  Ma’ana, ba za ace maka ga daga inda aka ciro asalin bayani ko amsar ba.  Amma daga baya ƙorafin jama’a da tsoron tuhumar satar fasaha (Copyright infringement) yasa suka fara ishara ga inda asalin bayani da inda suka markaɗo amsar, kai tsaye. – Jaridar AMINIYA, 5 ga Watan Afrailu, 2024.

13

Na Biyu:  Me Kake Nema?

Hanyar cin gajiyar wannan fasaha na biyu shi ne, iya tantance abin da kake nema na bayanai.  A cikin doguwar maƙalar da muka gabatar mai take: “Hanyoyi 9 Da Fasahar AI ta Sauya Duniyar a Shekarar 2023”, mai karatu ya fahimci cewa, su waɗannan manhajar fasahar AI da ake kira: “AI ChatBot”, suna markaɗo bayanan da suke bayarwa ne daga tarin bayanan da aka koya musu tsarin samar da bayanai a kai tun sadda ake gina su.  Amsar da fasahar za ta baka ya danganci irin bayanan da ka bata ne lokacin da kake mata tambaya.

Don haka, kafin ka fara auna mata tambayoyi ko umarni, zai dace kasan me kake bukatar wannan manhaja ta samar maka?  Kana iya zama ka jera bukatunka a rubuce kafin ka doshi inda take.  Idan littafi kake son rubutawa, zai dace ka zayyana dukkan taken babukan da kake son su kasance a littafin, tare da ƙananan take (Sub-headings).  Haka duk wani abu da kake nema na bayani, ka gama tattaro shi a zuciyarka tukun, in ma ba za ka rubuta a takarda ba, kafin ka fara jefa tambayoyin don samun amsa.

Na Uku: Gabatar Da Kanka

Kamar yadda yake a al’adar rayuwa, mutumin da ya sanka sosai, shi yafi dacewa ka nemi shawararsa kan abubuwan dake da alaƙa da kai.  Kafin ka fara ma’amala da ire-iren waɗannan manhajoji na fasahar AI, zai dace ka gabatar da kanka gare su kai tsaye.  Wannan zai sa baka bayanai ta la’akari da yanayinka, ko aikinka, ko rayuwarka, ko irin abin da kake ta’ammali dashi a lokacin da kake neman bayanan.  Misali, idan da manhajar ChatGPT ne za ka yi ma’amala, akwai inda za ka je wajen tsare-tsaren manhajar, ka rubuta tarihinki, da aikin da kake yi, da abubuwan da kake sha’awa, tare da irin tsari ko salon da kake son manhajar ta riƙa amsa maka tambayoyi idan ka yi.

Idan ba da manhajar ChatGPT za ka yi amfani ba, kana iya ƙirƙirar sako na musamman a karon farko idan ka hau manhajar, mai ɗauke da waɗannan bayanai, don bai wa manhajar daman saninka sosai.  Wannan zai taimaka wajen amsar da za a riƙa baka, kuma musamman idan akwai wani salo na musamman da kake son a riƙa kiyayewa wajen ba da amsar.

Na Huɗu:  Kyautata Umarni

Waɗannan manhajoji dai na karɓar buƙatarka ne ta hanyar wasu saƙonni na musamman da ake kira: “Prompts” a harshen Turanci.  Ba wani abu bane illa tambaya ko umarnin da kake son bai wa manhajar, wanda ke ɗauke da buƙatarka.  Iya yadda ka kyautata wannan umarni, tare da dukkan abin da ya kamata manhajar ta sani na bayani, iya yadda za ka samu amsa mai gamsarwa, cikin sauƙi.

- Adv -

Na Biyar: Neman Ƙarin Bayani

A duk sadda kayi tambaya, manhajar za ta aiko maka amsa nan take.  Idan baka gamsu ba, kana iya neman ƙarin bayanai kai tsaye.  Kuma za a duba buƙatarka, kamar dai yadda ka san ɗan adam kanyi.  Neman ƙarin bayani na iya zama ta fuskoki da dama.  Kana iya cewa faɗaɗa tambayarka, ko ka ƙara tsuke tambayar.  A ɗaya ɓangaren kuma, ta yiwu amsar ma da aka baka ba ta da alaƙa da tambayar.  Nan take sai ka sake jadda tambayar, da nuna cewa kai fa ga abin da kake nufi.

Na Shida: Bibiyi Asalin Bayani

Asalin bayani shi ne inda manhajar ta ciro ko ta markaɗo amsar da ta baka.  A farkon bayyanan waɗannan manhajoji, kai tsaye kawai suke ba ka amsar tambaya, babu marji’i.  Ma’ana, ba za ace maka ga daga inda aka ciro asalin bayani ko amsar ba.  Amma daga baya ƙorafin jama’a da tsoron tuhumar satar fasaha (Copyright infringement) yasa suka fara ishara ga inda asalin bayani da inda suka markaɗo amsar, kai tsaye.

A duk sadda aka cillo maka amsa, kana dubawa za ka ga alamar lambobi da ake saki zuwa can ƙasa, don menan ƙarin bayani. In kaga dama ma, kana iya cewa a haɗo maka amsarka da asalin marji’in da aka yi amfani dashi wajen kalato maka bayanai.  Wannan zai taimaka maka wajen faɗaɗa bayani kai tsaye, musamman idan kana haɗa bayanai ne don binciken ilimi ko gabatarwa a gaban jama’a.

Na Bakwai:  Kula Da Shirmen AI

Dukkan manhajar samar da bayanai ta fasahar AI na ɗauke da wata ɗabi’a da ake kira: “AI Halucination”.  Kamar kace: “Shirmen AI”.  Wannan ba wani abu bane face shirme ɗin, kamar dai yadda kaji kalmar.  Hakan na faruwa ne idan ka rubuta tambaya, sai a cillo amsa mara alaƙa da tambayar.  Ko a cillo maka rabin amsa.  Ko ma ace maka ai babu amsa, alhali tambayar da kayi ba ta da alaƙa da wani abu na haramci a ƙa’idar tsarin ma’amala da manhajar ba.  Idan kaga haka, to, alamar shirme ce daga manhajar.  To me yasa hakan ke faruwa?

Tun asalin samar da waɗannan manhajoji har zuwa yau, kamfanonin basu gushe ba wajen faɗakar da mutane cewa su fa waɗannan manhajoji ba allan-misiru bane.  Na’urori ne na sadarwa da aka ɗabi’antar dasu wajen iya fahimta da nazari da naƙaltar ma’anoni daga tarin dandazon bayanai.  Kuma da zarar ka musu tambaya, nan take suke ƙoƙarin hararo amsar tambayar, sannan su baka.  To a galibin lokuta, ba kowane lokaci ake dacewa su hararo daidai ba, sai su kwaso maka shirme.

A ƙarshe dai, waɗannan su ne mahimman hanyoyin da mai karatu zai iya bi wajen ganin ya ci gajiyar wannan fasaha in Allah Ya yarda.  A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.