Sakonnin Masu Karatu (2021) (2)

Tsarin Ginawa da Adana Gidan Yanar Sadarwa

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 29 ga watan Janairu, 2021.

111

Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce, nakan ga wasu tallace-tallace da wasu kamfanoni ko cibiyoyi ko daidaikun mutane ke yi ga duk wanda yake son a bude masa adireshin yanar gizo na Website, wasu su ce kyauta wasu kuma su ce sai an biya su.  To tambayar ita ce, shin, ana samun masu damfara ne a cikinsu? Da gaske akwai wadanda suke yiwa mutum kyauta kuma babu wani boyayyen caji? Shin mutum zai iya budewa kyauta? Mutum zai iya bude kamar guda biyu ko fiye da haka, misali da na shi da na kungiyarsa? Su wa ake kira ‘Host’ dake karban kudin gudanar da website din mutum ko Blog dinsa a duk shekara? Ka taimake ni da yadda za a yi na bude website nawa na kaina da kuma blog kuma in akwai na kyauta ka turo min da link din da kuma yadda zan yi.  Na gode Allah ya kara basira da daukaka. – Ahmed Ali: ahmedaaly@yahoo.com.

Wa alaikumus salam, barka dai  Malam Ahmad.  Duk da cewa baka yi bayanin a wani wuri ne a Intanet kake ganin ake tallata yadda za a gina wa mutum gidan yanar sadarwa ba, ina kyautata zaton ko dai a tashar Youtube ne, ko kuma ta hanyar tallace-tallacen kamfanin Google ke likawa a gidajen yanar sadarwar wasu, musamman na shafukan jaridu.  A ka’ida dai, ban san wani wuri da ake gina wa mutum shafin Intanet kyauta ba – daga ginawa har tafiyarwa.  Wannan babu shi kuma baza ka taba samu ba.  Dangane da tambayarka na cewa ko ‘yan damfara ne?  Bazan iya ce maka eh ko a a ba.  Domin ban wani shafin Intanet ne kaje kaga irin wancan tallar da kaka ishara gare shi ba.  Idan mahalli ne ingantacce, mu kaddara tallace-tallacen da ake likawa a shafukan jaridun Intanet ko wasu shafuka na kasuwanci, ina iya cewa zance ne suke fada don jawo hankalin mutane zuwa ga hajojinsu.  Idan kaje shafin, za ka samu bayanan dake nuna cewa ba hakikanin kyauta suke nufi ba.  Watakila suce za ka biya kudin adana shafukan (Hosting), amma a gina maka a kyauta.  Ko ka gina da kanka, a adana maka shafukan kyauta don baiwa mutane damar isa ga shafinka, amma da sharadin za a rika dora tallace-tallace a shafukan da kake dorawa, kuma ba za a biya ka ko sisi ba.  Ka ga duk dai ba wanda yake kyauta a ciki.

Masu gina shafukan Intanet ko bayar da damar yin hakan a Intanet, sun kashi-kashi ne.  Akwai inda za a baka damar gina shafinka da kanka, ka dora dukkan bayanan da kake son mutane suyi ta’ammali dashi, duk a kyauta.  Bayan wannan, za a baka damar zaban adireshin da zai riskar da masu ziyara zuwa shafinka kai tsaye.  Amma sai kuma, wannan araha ce da ba ta ado.  Domin idan an baka damar dora bayananka bayan ka gina shafin da kanka, akwai iya ma’adana takaitacce da za a baka. Sannan adireshin da za ka zaba ma, za a dora wasu kalmomi da zasu kara masa tsayi, don nuna cewa ga mahallin da kake amfani dashi.  Sannan idan ka gama dora bayananka, za a rika dora tallace-tallace, don duk masu ziyara su rika gani.  Wannan shi ne farashin da kake biya sanadiyyar baka wannan mahalli kyauta da aka ce maka.  Kamfanonin dake bayar da irin wannan dama dai sun hada da kamfanin Google a shafinka mai suna: “Blogspot”, da “Wordpress”.   A dukkan wadannan wurare za ka gina shafukanka ne tare da dora bayananka ta hanyar shafinsu dake Intanet, kai tsaye. Idan kuma so kake ka samu cikakken ‘yanci ta hanyar mallakar shafinka ba tallace-tallace, kuma da adireshin da kake bukata babu kari, sai ka biya kudi.

- Adv -

Akwai kuma masu zaman kansu dake gina shafukan Intanet a biya su.  Amma ban taba ganin wanda ke gina shafukan Intanet har a dora maka a Intanet, duk a kyauta ba.  Don haka, ka kiyaye.  Ita Kalmar kyauta a Intanet ba ta nufin irin kyautar da ka sani a zahirin rayuwa.  Akwai abubuwa a dunkule a karkashin Kalmar, wadanda sai ka kwankwasa za ka ji su.

Dangane da masu adana shafukan Intanet, wato “Hosting Company” kenan, su ma babu kyauta cikin ayyukansu.  Akwai kamfanoni irin su “GoDaddy” da “Hostgator” da sauran makamantansu.  Aikinsu shi ne, idan ka sayi ma’adana a wurinsu, sai ka gina shafinka na Intanet, ka kuma dora, da kanka, sannan a kaci gaba da lura da shafinka da kanka.  Abin da kawai suke baka shi ne mahalli.  Kamar gidan haya ne.  Za ka lura da gidan da ka kama haya.  Galibi akan biya kudin ajiyan ne a duk shekara.  Amma suna ba da damar biyan na wata guda, ko watanni uku ko watanni shida.  Sannan suna sayar da adireshi idan kana bukata.  Kuma idan kana son wanda zai gina maka shafin Intanet, suna iya hada ka dasu. Amma asalin hajar da suke sayarwa dai ita ce mahallin da za ka adana bayananka don baiwa mutane damar ziyartarsu.  Idan kana bukatar sani da ganin yadda abin yake, kana iya ziyartar shafin GoDaddy dake: https://www.godaddy.com, ko na kamfanin Hostgator dake: https://www.hostgator.com.  Idan kaje za ka ga hakikanin abubuwan da suke tallatawa.  Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya. Hakika ni mai bibiyar shafinka ne dake jaridar aminiya tsawon shekaru. Amma a wannan lokacin abubuwa sunyi mini yawa. Mai kawo mini jarida ya kawo mini har wajen sati 7. Jaridun na nan amma babu damar karantawa. Dan haka nake neman alfarmarka don Allah ka aiko mini da kasidarka da ta gabata kan fasahar 5G ta akwatin Imail dina. Nagode. Daga Mai kaunarka: Abubakar salihu. – asbmashkur@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar.  Duk da cewa na daina aika wa masu karatu makaloli ta hanyar Imel, saboda Taskar Baban Sadik da na bude don zuba dukkan makalolin ga masu bukata, zan aiko maka musamman ganin ban rika na dora makalar da na rubuta kan Fasahar 5G a Taskar ba.  In Allah Yaso, cikin ‘yan kwanakin dake tafe zan dora makalolin dake kasa – sun kai kusan 100 –  a taskar.  Duk mai bukata yana iya ziyartar shafin don karantawa da saukar da dogayen makalolin dake taskance a shafin.  Allah amfanar damu baki daya.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.