Hanyoyin Cin Gajiyar Fasahar AI (2)

Manyan Haɗurran Fasahar AI

Fasahar samar da bayanai na AI tana iya ƙirƙirowa tare da kwaikwayon muryar mutane kala-kala.  Kana iya ɗaukan muryarka a waya ko a makirfon, ka loda mata, ka samar da rubutu, kuma ta karanto maka rubutun da muryarka cikin sauƙi, kai tsaye. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 29 ga watan Disamba, 2023.

61

Haɗurran Dake Tattare da Fasahar AI

A makon jiya masu karatu sun fahimci da yawa cikin ƙudurorin da wannan fasaha ta AI take ɗauke dasu, wajen iya fahimtar ma’anoni daga dandazon bayanai, da yin nazari kansu, da tsintar maudu’i daban-daban da za ta iya samar da bayanai a kai tiryan-tiryan.  Sannan mun tabbatar da cewa wannan tsari na AI da ake kira: “Generative AI”, wato fasahar samar da bayanai ta AI, irin su ChatGPT da Bard, tana iya ƙirƙirar abubuwa da yawa, ba wai fahimtar ma’anonin bayanai kaɗai ba.  A taƙaice dai, akwai abubuwa da yawa da wannan sabuwar fasaha ke iya gudanar dasu cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, sama da yadda ɗan adam ke iyawa a rayuwa ta al’ada.

Wannan yasa a farkon wannan shekara ɗaya daga cikin masana fasahar AI a duniya dake aiki a kamfanin Google, ya fito fili yace idan ba a ɗauki ƙwararan matakan kariya ba, nan da shekaru kaɗan wannan fasaha ta AI za ta haddasa illoli masu girman gaske a duniya.  Domin za ta iya baiwa nan’urorin mutum-mutumi (Robot) masu amfani da fasahar AI, iko akan jinsin ɗan adam baki ɗaya.  Wannan zance da yayi ya ta da ƙura matuƙa, inda cikin ‘yan kwanaki kafafen yaɗa na duniya suka yi ta sharhi tare da hira da masana kan harkar, wajen yiwuwar hakan ko rashinsa.  A taƙaice dai, wannan fasaha ta AI takobi ne mai kaifi biyu.  Ko dai ka iya sara dashi, sai ya amfaneka.  Ko kuma in baka iya ba, sai ya sare ka.

Kafin muje bayani kan hanyoyin da mai karatu zai iya cin gajiyar wannan fasaha ta AI, zai dace muyi bayanin haɗurran dake tattare da ita, tare da bayanin abin da masana suke hange ko hasashe na abin da zai je ya dawo, cikin shekaru ko zamunnan dake tafe.

Satar Fasaha da Wankiya

Tun bayyanar fasahar Intanet da shafukan sadarwa na zamani (Internet), aka samu ƙarin yaɗuwar satar fasaha tare da wankiya a ɓangaren ilimi.  Satar fasaha shi ake kira “Piracy” – wato mutum ya ɗauki fasahar da ba tasa ba ya mallaketa.  Wankiya kuma, a ɗaya ɓangaren, shi ake kira: “Flagiarism”.  Ya ƙunshi ɗaukan wasu bayanai ne na ilmi mallakin wani, ya mallaka wa kanka ta hanyar shigar dashi cikin rubutunka, ba tare da ambaton mai asalin rubutun ba.  Fasahar Samar da Bayanai na AI, wato “Generative AI” na sawwaƙe aukuwar waɗannan matsaloli cikin sauƙi. Kana iya umartanta da rubuta maka maƙala ta musamman kan wani maudu’i, sai ta tattaro bayanan wasu dake Intanet, ta markaɗa maka, sannan ta aiko maka. Da yawa cikin mutane kawai ɗauka suke su rattafa sunansu akai.

Satar Murya

- Adv -

Fasahar samar da bayanai na AI tana iya ƙirƙirowa tare da kwaikwayon muryar mutane kala-kala.  Kana iya ɗaukan muryarka a waya ko a makirfon, ka loda mata, ka samar da rubutu, kuma ta karanto maka rubutun da muryarka cikin sauƙi, kai tsaye. A halin yanzu akwai ‘yan dagajin Intanet dake satan muryar mutane suna ƙirƙiran shafukan yanar sadarwa na kamfanonin dake da masu muryar, da karkatar da mutane zuwa waɗannan shafukan bogi da suka buɗe, don cutarsu, da zummar su ne asalin ma’aikatan wancan kamfani.

Waƙoƙin Bogi

A halin yanzu mawaƙa na cin kasuwarsu da tsinke.  Lokaci na nan zuwa da cikin ɗan ƙanƙanin lokaci za ka iya umartan wannan fasaha ta AI ta ƙirƙiro maka waƙoƙin mawaƙa daban-daban, da muryarsu da komai, amma kalmomin ne kawai mabambanta.  To, a yanzu idan anje kotu, wancan waƙar na mawaƙan ne, ko naka kai da kayi amfani da fasahar samar da bayanai na AI wajen ƙirƙirosu?  Murya dai ta mawaƙin ce.  Yaya za ayi kenan?  Wannan na cikin manyan ƙalubalen da har yanzu masana ke ƙoƙarin gano hanyoyin warwaresu kafin lokaci ya ƙure.

Makamai Masu Sarrafa Kansu

Fasahar AI na ba da dama wajen ƙirƙirar na’urori masu sarrafa kansu wajen gudanar da ayyukan da ɗan adam ke yi a al’adar rayuwa ta yau. Akwai shagunan cin abinci a ƙasar Jafan dake amfani da ire-iren waɗannan na’urori wajen kai wa mutane abincin da suka yi oda a inda suke zaune.  Kana ma iya magana da na’urar har ta baka amsa.  Bayan nan akwai makaman yaƙi kala-kala masu sarrafa kansu wajen gudanar da ayyukan da aka gina su akai.  Waɗannan makamai da ake kira da suna: “Drones”, suna amfani ne da fasahar AI wajen gano bigiren da mai laifi ko wanda ake son dirkakewa yake, da alamomin dake bambance mata ɗan adam da sauran halittu da dai sauran hikimomin gano abubuwa. Tambayar ita ce, shin nan gaba idan ire-iren waɗannan na’urori na ƙara samun “wayewa” da “ƙwarewa”, kamar yadda waɗancan masana ke cewa, nan gaba ba za su iya mallake duniya ba?  Wannan tambaya ce da me karatu zai ji kamar akwai hauka a ciki, amma akwai ma’ana mai ƙarfi.  Musamman idan kana rayuwa ne a ƙasashen da ake wannan zance, inda wannan fasaha taci gaba kenan.  A taƙaice dai, tun su ne suka fi amfani da wannan fasaha, su suka fi kowa sanin yanayin ci gaban da ake samu, sannan su ne suka fi cancantar yin hasashe kan me zai je ya dawo.

Holoƙon Makarantu

Daga cikin abubuwan da ake tsoron faruwarsu idan wannan sabuwar fasahar samar da bayanai ta AI ta ƙara haɓaka a duniya dai akwai gushewar makarantu da jami’o’i nan da ɗan lokaci kaɗan.  Domin waɗannan manhojin samar da bayanai da aka gina su da fasahar AI suna iya maka kusan dukkan wani abin da malamin aji zai maka – na bayanai dall-dalla, da koya maka abu cikin raha da nishaɗi, da fahimtar yanayinka don koyar da kai ta la’akari da yanayinka.  Kai, hatta koyon harshe da yaruka duk kana iya yi ta amfani da wannan fasaha ta AI.  Ba wannan kaɗai ba, hatta koyon lissafi, da haɗa kalmomi, da fahimtar sauti, da tantance abubuwa masu tsauri cikin sauƙi da dai sauransu, duk wannan fasaha na iya yi, cikin ƙwarewa mai ban al’ajabi. Mafi girma cikin abubuwan haɗari da wannan fasaha ke ɗauke dashi a cewar masana, shi ne iya adanawa, da iya tuna baya, da kuma tantance tsakanin abubuwa.  Idan kayi hira da manhajar a yau.  Gobe ka sake dawowa kayi hira da ita.  Jibi ka sake komawa.  A rana ta huɗu za ka sha mamaki idan ta fara baka bayani kan ɗabi’unka dalla-dalla.

Waɗannan kaɗan ne cikin abubuwan haɗari da masana ke hasashen nan gaba za su iya kawo farmaki ga wannan duniya tamu.  Saura dame?  Wajibi ne mai karatu ya san wasu hanyoyi zai iya bi wajen cin gajiyar wannan fasaha cikin sauƙi, kafin wannan lokaci.  Wannan shi ne abin da za mu yi magana akai mako mai zuwa in Allah Yaso.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.