Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (10)

Fasahar ChatGPT Da Masana'anar Hollywood

Wannan yajin aiki na marubutan masana’antar Hollywood ya farkar da duniya matuƙa wajen ƙara faɗaka daga irin abubuwan da waɗannan manhajoji na AI za su iya yi, da kuma haɗarin dake tattare da ƙwarewarsu nan gaba, wajen iya gudanar da galibin ayyukan da mutane ne ke yinsu a yau, wanda hakan na iya zama sanadin rasa ayyukansu, da gurabun neman abincinsu da dukkan abin da ya shafi rayuwarsu.  To mece ce mafita? – Jaridar AMINIYA, 8 ga Watan Maris, 2024.

7

Na 8: Fasahar ChatGPT Da Hollywood

Abu na takwas daga cikin abubuwa tara da suka taimaka wa Fasahar AI wajen sauya duniyar a shekarar 2023 shi ne zanga-zanga da yajin aiki da marubutan kamfanonin Hollywood na ƙasar Amurka suka yi, daga watan Mayu zuwa watan Satumba; tsawon wata biyar kenan.  Wannan zanga-zanga da yajin aiki da marubutan suka yi ya dunƙusar da al’amura a masana’antar baki ɗaya.  To meye dalilin wannan yajin aiki, wanda ake ganin shi ne mafi tsawon lokaci da ma’aikatan suka yi?

Dalilin wannan yajin aiki dai ba nesa yake ba.  Ba wani abu bane face bayyanar fasahar ChatGPT, wato manhajar fasahar samar da bayanai kai tsaye na kamfanin OpenAI, da yadda wasu kamfanoni suka fara amfani da manhajar wajen ƙirƙirar labari, da faɗaɗa shi, tare da zayyana labarin a tsarin fim, kai tsaye ta hanyar wannan fasaha.  Wannan, a cewar ma’aikatan masana’antar, yunƙuri ne na maye gurbinsu da wannan fasaha a kaikaice.  Suka ce yin amfani da wannan fasaha wajen samar da asalin labari, da rubuta shi a tsarin fim, tare da tantance shi, zai mayar da marubutan masana’antar ne ‘yan kallo ne.  A ƙarshe ma su zama ‘yan zaman dirshan; marasa amfani.  A nasu hasashen, suka ce idan aka ci gaba a haka, to, a ƙalla marubuta da ma’aikatan da wannan yunƙuri zai shafa, tare da yin sanadiyyar rasa aikinsu, za su kasance cikin mutane sama da miliyan ɗari uku (300 million) da aka tabbatar wannan fasaha za ta zaftare musu ayyukansu a duniya.

Wannan yajin aiki na tsawon watanni biyar dai ya durƙusar da ayyuka a masanantar Hollywood gaba ɗaya.  Wannan yasa a ƙarshe dai aka zauna don tattaunawa, inda aka yi yarjejeniya tsakanin marubutan da kamfanonin fina-finai kan cewa, kamfanonin za su daina amfani da wannan fasaha ta ChatGPT da sauran makamantanta – irin su Google Gemini, da Perplexity, da Microsoft Copilot – wajen rubutawa da bitan labarun fina-finan da marubutan ke rubutawa.

Sai kuma yarjejeniya ta biyu, cewa daga yanzu kamfanonin da suka mallaki waɗannan fasahohi na samar da bayanai na AI, ba za su riƙa amfani da rubutattun labaran kamfanonin fina-finan Hollywood wajen “koya” wa manhajojinsu tsarin tunani da yadda sigan rubutun labaran suke ba.  Abin da wannan yarjejeniya ta ƙunsa shi ne, dukkan waɗannan fasahohi na AI, a yayin da aka gina su, ana “koyar” dasu yadda ake tunani, da yanke hukunci kan abubuwa, da ƙiraƙirar nau’ukan rubutattun bayanai kan kowane irin maudu’i ne, duk ta hanyar dandazon bayanai dake Intanet ko waɗanda kamfanin ya tara.  Wannan tsarin koya wa na’ura mai basira tunani, shi ake kira: “Training”.  Bayanan da ake ciyar da ita kuma, wanda akansu take aikin nazartan yadda tsarin gina zance yake, da sigan rubuta, da alaƙoƙi tsakanin bayanai da dai sauransu, su ake kira: “Training Data”.

- Adv -

To, abin da wannan yarjejeniya ke cewa shi ne, dukkan bayanan da kamfanonin fina-finan suka mallaka waɗanda marubutan suka rubuta musu, ba za a yi amfani dasu wajen “koyar” da waɗannan manhajoji na AI ba.  Hikimar a nan shi ne, don kada waɗannan fasahohi su ƙware wajen iya rubutawa da tsara labaran fina-finai, ta yadda nan gaba zasu ƙwace wa marubutan aikinsu.  Ƙulla wannan yarjejeniya ne ya kawo ƙarshen wannan dogon yajin aiki da marubutan suka shiga.

Wannan yajin aiki na marubutan masana’antar Hollywood ya farkar da duniya matuƙa wajen ƙara faɗaka daga irin abubuwan da waɗannan manhajoji na AI za su iya yi, da kuma haɗarin dake tattare da ƙwarewarsu nan gaba, wajen iya gudanar da galibin ayyukan da mutane ne ke yinsu a yau, wanda hakan na iya zama sanadin rasa ayyukansu, da gurabun neman abincinsu da dukkan abin da ya shafi rayuwarsu.  To mece ce mafita?

Mafita Daga Wannan Hasashe

Ba damuwa kan ci gaban fasahar AI kaɗai ba, hatta lokacin da kwamfuta ta fara yaɗuwa a duniya, masana sun ta nuna ƙorafi kan yadda amfani da kwamfutoci a wuraren aiki da kamfanoni da masana’antu zai zama sanadiyyar rasa aikin da yawa cikin mutane.  Wannan hasashe an yi shi sama da shekaru 20 yanzu, amma abin da ake tsoro bai faru ba.  Daga baya aka ce yawan amfani da na’urorin mutum-mutumi, wato “Robot” a masana’antu, shi ma zai bayu zuwa ga rasa ayyuka a ire-iren waɗannan kamfanoni da masana’antu.  Wannan hasashe shi ma an daɗe da yinsa.  Amma ga dukkan alamu, abin da ake tsoro har yanzu bai faru ba kamar yadda aka yi hasashensa.  Yanzu kuma ga hasashen kan ƙwarewar kwamfutoci da na’urorin sadarwa na zamani, musamman idan suka fara iya tunanin kamar yadda ɗan adam ke tunani.  Wannan shi ne zamanin da muke ciki yanzu, wanda yake kan haɓaka.  Hasashen da aka yi shi ne nan da wasu ‘yan shekaru, mutane sama da miliyan ɗari uku za su iya rasa aikinsu sanadiyyar na’urorin sadarwa masu basira, wanda fasahar AI ke kan samarwa da haɓakawa.

A ƙarshe, galibin hasashen da ake yi ba ya tabbata.  Idan ma ya tabbata, ba ya kai girma da munin yadda aka yi hasashensa a farkon lamari.  Dalili kuwa shi ne, kowace irin fasaha idan ta bayyana kuma ta fara tasiri a rayuwar mutane, tasirinta na kasuwa zuwa gida biyu ne.  Na farko, shi ne bangaren amfani ko ci gaba, wanda shi ne manufar samar da fasahar.  Na biyu kuma shi ne tasiri mummuna, wanda kan faru saboda yaɗuwa da bunƙar fasahar.  Galibi irin wannan tasirin ba ta gamewa, kuma tana taƙaituwa ne sosai, musamman idan an yi amfani da fasahar yadda ya kamata.

A ɓangaren kyayawawan tasiri akwai damammaki masu kyau da samuwar fasahar ke haifarwa.  Misali, bayyanar kwamfutoci a duniya wajen ayyuka da karatu, ya haifar da damammaki da dama.  Ya haifar da samuwar masu gyaran kwamfuta, da masu sayarwa, sai kuma wasu sababbin ayyukan da sai da kwamfuta ake iya gudanar dasu.  Ire-iren waɗannan ayyukan kuma dama ne ga waɗanda suka iya sarrafa kwamfuta.  To, haka abin yake a ɓangaren wannan fasaha ta AI; duk da cewa za ta karɓe ayyuka da dama a halin yanzu da ɗan adam ke iya gudanar dasu kai tsaye, sai dai kuma a ɗaya ɓangaren, za ta samar da damammaki da yawa ga waɗanda suke iya amfani da ita.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.