Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (3)

Fasahar “AI” a Fagen Ƙere-Ƙere

Amma a halin yanzu da bayyanar wannan fasaha ta AI, an kintsa musu tunani da ɗabi’un ɗan adam, don basu damar gudanar da ayyukan da suke yi ba tare da wata inji dake jujjuya su ba. Kawai sai dai su riƙa amfani da ƙa’ida da ɗabi’un da aka girka musu cikin ƙwaƙwalwarsu. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 19 ga watan Janairu, 2024.

297

Fasahar “AI” a Fagen Ƙere-Ƙere

Bayan fagen sadarwa da kwamfuta, tuni fasahar AI ta fara maye fannin ƙere-ƙere. Mafi shahara daga cikin na’urorin da aka girka wa wannan fasaha dai ita ce na’urar mutum-mutumi ko kace na’ura mai fasaha, wato: “Robot”. Wannan na’ura an ƙera ta ne a siffa da surar ɗan adam, ko wasu halittu; suna motsi, suna ɗaukan kaya, suna karɓan kaya, suna aika saƙo kuma suna karɓan saƙo, suna tafiya, suna hawa kuma suna sauka. A manyan kamfanonin ƙera motoci ko injina ko jiragen sama, waɗannan na’urori masu fasaha suna da girma. Galibi ma cikin surar babban inji ko wani abin ɗaukan kaya aka yi su, ba a surar ɗan adam ba. A manyan shagunan sayar da kayayyaki kuma dake galibin ƙasashen da suka ci gaba, an ƙera ire-iren waɗannan na’urori ne a siffa da surar ɗan adam ko wasu halittu masu ban sha’awa. Wannan ita ce siffarsu ta asali. Kuma ana amfani da inji ne wajen sarrafa ayyukansu.

A ƙasar Sin (China) ire-iren waɗannan na’urori suna nan birjik ana amfani dasu wajen gudanar da ayyuka da dama ba a fannin ƙere-ƙere kaɗai ba, har da fannin noma, da fannin kiwon lafiya, da fannin ilimi da kuma fannin tsaro. Ana kiran su da suna: “AI Enabled Drones”. Ana amfani dasu wajen ɗaukan kaya daga wannan gari zuwa wancan, ko daga wannan ma’aikata zuwa wancan. Ana amfani dasu wajen ban ruwa da feshi a gonaki. Haka ma ana amfani dasu wajen lura da masu satar jarabawa a makarantun ƙasar. Sannan ana amfani dasu wajen tattaro bayanai ta hanyar ɗaukan hoto da bidiyo da bayanan yanayi – zafi ko sanyi ko tururin dake samuwa a sararin samaniya.

Na’ura Mai Fasaha (AI Robot)

Amma a halin yanzu da bayyanar wannan fasaha ta AI, an kintsa musu tunani da ɗabi’un ɗan adam, don basu damar gudanar da ayyukan da suke yi ba tare da wata inji dake jujjuya su ba. Kawai sai dai su riƙa amfani da ƙa’ida da ɗabi’un da aka girka musu cikin ƙwaƙwalwarsu. Na’urori masu wannan siffa da ɗabi’a su ake kira: “AI Robots” ko “AI Powered Robots” – wato “Na’ura mai fasaha” kenan. A fagen likitanci ma an samu ci gaba a wannan fanni sosai. Na’ura mai fasaha ta farko da ta fara aiwatar da aikin tiyata a jikin wata halitta a duniya ita ce wacce aka ƙera a shekarar 2012. An wakilta wannan na’ura ne don ɗinke cikin wata dabba da aka buɗe saboda wata cuta dake damunta a tumbinta. Nan take ta ɗinke wurin sarai. Masana suka ce ta ɗinke wurin da kyau, fiye da yadda ɗan adam ke ɗinke ciwo a jikin mara lafiya.

- Adv -

Daga bayyanar cutar COVID-19 zuwa yau an samu ƙaruwar kamfanoni da shaguna masu amfani da ire-iren waɗannan na’urori masu fasaha don sawwaƙe ayyuka da ƙara tabbatar da kariya. Misali, a wani kantin cin abinci dake ƙasar Jafan, idan ka ba da odar abin da za a kawo maka na abinci, da zarar an gama haɗawa, irin wannan na’urar ce za ta ɗauko abincin, tiryan-tiryan ta kawo maka inda kake zaune, ta ajiye maka a kan tebur, sannan ta juya ta tafi. Idan wani ma ya buƙata, haka za a masa. An tanade ta ne don tabbatar da kariya daga kamuwa da cutar korona. A shagunan sayar da kayayyakin masarufi kuwa, ana amfani dasu wajen ɗauko kayayyaki masu nauyi, ko taimaka wa masu sayan kaya ɗaukan abin da suka saya zuwa inda za su biya kuɗi, kafin su wuce. Wannan kaɗan ne cikin dubunnan misalai da ake dasu a aikace, a warwatse a sanannin duniya.

Mota Mara Matuƙi (Driverless Car)

Bayan waɗannan na’urori masu fasaha, wannan fanni na AI ya sawwaƙe hanyar samar da motoci masu tuƙa kansu ba tare da direba ba. Wannan nau’in mota ita ake kira: “Driverless Car”. Kusan dukkan kamfanonin ƙera motocin zamani a duniya a yau sun ƙera, ko suna kan ƙerawa ko suna da ƙudurin ƙera ire-iren waɗannan nau’ukan motoci. Kamfanin Tesla babban kamfanin ƙera motoci da na’urorin zamani ne dake kasar Amurka. Shi ne kamfanin shahararren mai kuɗin nan ɗan asalin kasar Afirka ta Kudu mai suna Elon Musk ya mallaka. Tuni wannan kamfani ya fara ƙera motoci mara matuƙi. Bayan kamfanin Tesla, akwai kamfanin Google shi ma tuni yayi nisa wajen ƙera mota mara matuƙi.

Wannan nau’in mota dai ana gina mata ɗabi’un ɗan adam ne, wajen fahimtar titi, da masu tsallaka titi, da tazarar da za ta iya baiwa motar dake gabanta, da fahimtar yanayin mahalli, da yadda za ta taka birki idan tazo bakin danja, da yadda idan danja ta ba da hannu, za ta iya ganewa kuma taci gaba da tafiya, da yadda za ta iya sarrafa kanta idan tazo shataletale (Roundabout), duk yawan motocin dake wurin kuwa. Tirƙashi! Wani aikin sai ilimi.

Dukkan wannan nau’in ci gaba da fasahar AI ta samar ta ɓangaren na’urori sun shafi ɓangare guda ne. Ba wai iyakan abin da wannan fasaha ke iya yi ba kenan, ko iya abin da za a iya gudanarwa da ita ba kenan. Me aka yi ma tukun? Wai mahaukaciya ta shiga gaɗa sau tara. A taƙaice ma iya cewa wannan shi ne ɓangaren amfani da fasahar AI na gama-gari, har zuwa watan Nuwamba na shekarar 2022. A watan Nuwamba ne tunanin duniya ya fara sauyawa kan wannan fasaha ta AI. Lokacin da kamfanin OpenAI, tare da kamfanin Microsoft suka samar da wata manhaja mai iya ƙirƙirar rubutattun bayanai, ko yin nazari kan bayanan da aka shigar mata, ko ba da shawara, duk ta hanyar hira da ita. An samar da wannan manhaja ne ta amfani da fasahar AI mai suna “Generative AI”, wato Fasahar Samar da Bayanai ta AI. Samuwar wannan nau’in fasaha daga watan Nuwamba ta shekarar 2022, shi ya sauya tunani da tsarin duniya a fannin ilimi, kasuwanci, likitanci, haƙƙin mallaka, tsaro, kariyar bayanai da sauransu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.