Sakonnin Masu Karatu (2021) (7)

Kasuwancin Bitcoin

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 5 ga watan Maris, 2021.

556

Kamar yadda muka faro makonnin baya, a yau ma za mu ci gaba da amsa tambayoyinku ne, saboda sun taru sosai.  Idan muka gama sai mu bude sabon fannin bincike kan fasahar “Cryptocurrencies”.  Hakan na bukatar natsuwa don fa’idantuwa da bayanan da zasu zo, cikin yare mai sauki.  Kafin nan, aci gaba da kasancewa tare damu.

————

Asslamu alaikum Baban Sadik, Allah ya kara basira.  Tambayata ita ce,  akwai wasu ma’aikatan bankina ta Zenith Bank, da suka karbi wasu bayanaina na banki wai za su sayi “Bitcoin” ta amfani da taskar bankina,  amma za su bani nawa rabon N2,000. Abin daga baya ya daure mini kai.  Shi ne nake tambaya; anya babu hadari a wannan al’amarin kuwa?   Allah yasa ka fahimceni.   Musa Yola  – musayola621@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Musa.  Da farko dai, ya kamata ka fahimci cewa, a ka’idar aikin banki a Najeriya (da ma sauran kasashen duniya), babu wani ma’aikacin aikin banki na gari da zai kira ka yace ka bayar da bayanan taskar ajiyarka.  Idan kaji wani ya kira ka yace daga bankin da kake ajiya yake, kuma ana bukatar wasu bayananka don wasu dalilai, wanda kai ka nema ko baka nema ba, to, kasan cewa dan damfara ne; kai tsaye.  Allahumma sai in abokinka ne da ka sani, wanda ya bukaci hakan a mahangar abota don samar da maslaha a gareka.  Shi yasa, idan kana lura da sakonnin da bankinka ke aiko maka  ta hanyar sakonnin tes ko ta Imel, za ka ga suna gargadinka da kada ka sake ka baiwa wani bayanan taskar ajiyarka ta banki, sannan ba za su taba aiko wani daga cikin ma’aikatansu don karban bayananka ba.  Amma idan bankin ne kaje don wata bukata na gyara, ko neman balas, ko karban katin ATM, ko kuma gyara wasu bayananka, to, a nan za su baka fam ne ka cika. In ba wannan yanayin ba, to, a kiyaye.

Sai amsar tambayarka kan za a gudanar da kasuwanci da kudaden da ke taskar ajiyarka don samun riba ko wani abu makamancin wannan, wanda kace wani ma’aikacin bankinka ya bukata.  Ban san yanayin alakarku ba.  Amma ka sani, shi kasuwancin “Bitcoin” wani abu ne mai hadarin gaske, saboda yadda farashin wannan nau’in kudi ke canzawa.

- Adv -

Assalamu alaikum Malam, sunana Moussa daga Maradi.  Ni mabiyin shafinka ne.  Tambayata ita ce, shin, a nan Najeriya akwai jami’a da ake karatun “Hacking”? – Toure Moussa: tm3495579@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Toure dan mutan Maradi.  Ai ba a Najeriya ba ma, babu wata jami’a da aka samar musamman don koyon wannan ilimi na harkar kutse ko dandata, wato: “Hacking”.  Da farko dai ka sani, shi wannan nau’i na ilimi ba shi daga cikin manyan bangarorin ilimin harkar sadarwa na zamani.  Yana karkashin fannin kariyar bayanai ne a Intanet, wato: “Cybersecurity” ko “Computer Security”.  A tare da cewa akwai cibiyoyin koyon ilimin kwamfuta dake karantar da fannin, amma samun jami’a na musamman a duniya kam babu.

Amma duk da haka kana iya koyon ilimin a cibiyoyin koyon ilmin kwamfuta dake Intanet ko kuma ta tashar Youtube.  Sannan, sunan da aka san wannan fanni dash shi ne “Ethical Hacking”, ko kuma “Penetration Testing”.  Na fara jero bayanai kan wannan fanni da irin ilmomin dake cikinsa a shekarar 2018 in ban mance ba, amma sanadiyyar sace kwamfuta ta da aka yi sai na dan dakata.  Wannan shi ne tsarin da a yanzu ake bi wajen koyon wannan ilmi.  Domin bayan ka gama samun horo ta hanyar malami a aji, akwai jarabawa da za ka rubuta irin ta kwarewa, wato: “Professional Exam”, inda za a maka tambayoyi ta hancyar bijiro maka da hanyoyin aiwatar da kutse a aikace ta hanyoyi daban-daban.  Idan kaci nasara, sai a aiko maka da takardar shedar kammala karatu, tare da wani fam da za ka cika mai dauke da alkawarin cewa, ba za ka taba amfani da kwarewarka wajen cutar da jama’a ba ta hanyar aiwatar da kutse a cikin kwamfutoci ko na’urorinsu na zamani.  Wannan alkawari ne da za ka rika sabunta shi a duk bayan shekaru uku, tare da sake rubuta wani sabon jarabawa don ingantawa da kuma sabunta abin da ka karanta a baya.  Daga nan ka zama “Certified Ethical Hacker”.  Duk ran da aka kamaka kana aiwatar da kutse ta hanyar da ta haramta, to, za a soke lasisinka, sannan a hukunta ka.  A takaice dai, yadda kasan fannin likitanci, wajen ka’idoji, haka wannan fanni yake.

Don samun saukin yin karatu a wannan fanni da kammala shi cikin nasara, kana bukatar hakuri da juriya da kuma kayan aiki.  Daga cikin kayayyakin aiki akwai kwamfuta mai kwari da za ka mallaka.  Domin akwai manhajojin koyo da za a baka da za ka rika kwatanta wannan ilimi lokaci zuwa lokaci.  Daga cikin manyan manhajojin da za ka mallaka akwai babbar manhajar kwamfuta ta Linux, wacce ke dauke da jerin manhajojin da kake bukata cikin sauki, don aiwatar da halattaccen kutse.  Wannan babbar manhaja ita ake kira: “Kali Linux”, kuma kyauta ake iya mallakarta a Intanet.  A madadinta kana iya mallakar babbar manhajar nau’in Linux mai suna “Ubuntu”, domin ta fi saukin sha’ani.

A karshe dai, kamar yadda na sanar a farko ne, babu jami’a nan kasar dake koyar da fannin “Hacking”.  Kuma hatta a wasu kasashen ma, bance akwai ba.  Sai dai cibiyoyin koyon ilmin kwamfuta dake Intanet ko zahirin rayuwa.  Amma kana iya hawa tashar Youtube don bincike da sanin yadda wannan fanni yake.  Idan ka hau, ka tambayo” “Ethical Hacking Free Course”.  Ko kuma kayi amfani da kalmomin “Cours gratuit de piratage éthique”, a harshen faransanci kenan.  Daga nan za ka fahimci yadda abin yake, kuma hakan zai baka damar sanin daga inda za ka fara.

Ina maka fatan alheri a kodayaushe.  Allah sa a dace, kuma yasa a samu mai amfani, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.