Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (6)

Hotuna Masu Ban Al'ajabi

Yaɗuwar hotunan bogi da ake iya ƙirƙira da fasahar AI, da yaɗuwar bidiyon nau’in Deep Fakes na cikin manyan matsalolin da bunƙasar fasahar samar da bayanai kai tsaye na AI (Generative AI) ta samar tare da taimakawa wajen yaɗuwarsu a duniya a shekarar 2023. – Jaridar AMINIYA, 9 ga watan Fabrairu, 2024.

9

Na 3: Hotuna Masu Ban Al’ajabi

Daga cikin siffofin Fasahar ChatGPT 4 akwai iya ƙirƙira da samar da hotuna, raɗau kuma rau-rau.  Amma kasancewar fasahar bata yaɗu ba a farkon shekarar 2023, musamman ganin ba kowa ke biyan kuɗi don yin rajista da wannan zubi ba, sai ba a hankalci wannan ƙudura mai ban al’ajabi ba.  Har sai lokacin da wani bawan Allah mai suna Pablo Xavier (ba asalin sunansa ba kenan), wani ma’aikacin kamfanin gine-gine dake jihar Chicago ta ƙasar Amurka, ya ƙirƙira wasu hotuna na Fafaroma Francis – babban limanin ɗariƙar katolika na duniya dake birnin Rom. Hotunan sun nuna Fafaroma sanye da doguwar rigar sanyi fara mai sheƙi, cikin yanayin da al’adance bai kamata ace ya zama hakan ba.  Wannan bawan Allah yayi amfani da manhajar ƙirƙirar hotuna ne ta yanar sadarwa mai suna: “Midjourney”.

Bayyanar waɗannan hotuna ke da wuya mutane suka da tsokaci akai. Domin an ɗauka hotuna ne na gaskiya.  Idan ka gansu da wahala kayi zaton ba hotunan gaskiya bane.  Nan take mutane suka fara tsokaci akai, wasu na yabawa wasu na kushewa.  Hatta ɗan jaridar The Guardian na ƙasar Burtaniya sai da yayi dogon tsokaci akai a shafinsa, yana mai nuna rashin dacewar shigar ga babban limanin Katolikan, amma a kaikaice.  Kwamfa!  Bayan yan kwanaki sai ya bayyana cewa waɗancan hotuna duk na bogi ne; daga fasahar AI aka ƙirkire su.

Hakan cikin shekarar 2023 ɗin dai wasu hotuna suka ta da ƙura a ƙasar Amurka da sauran ƙasashen duniya, masu ɗauke da hoton tsohon Shuga Triump na ƙasar Amurka, ‘yan sanda na ƙoƙarin kama shi, shi kuma yana ja dasu ana ta hayaniya. Bayan wasu ‘yan lokuta sai wannan ɗin shi ma ya tabbata cewa hotunan bogi ne, ba na gaskiya bane.

Tun daga wannan lokaci aka fara samun yaɗuwar ire-iren waɗannan hotuna a shafukan yanar sadarwa na duniya.  A halin yanzu abin ya yi ƙamari, ta yadda ake tunanin idan ba a yi hankali ba, yana iya shafan ingancin zaɓuka da za a gudanar a ƙasar Amurka. Domin ‘yan siyasa da dama na ƙirƙirar hotunan bogi na abokan hamayyarsu suna ɗorawa a shafukan sada zumunta, duk don su muzanta su, su kuma su samu ƙarin karɓuwa wajen masu zaɓe.

- Adv -

Har wa yau cikin wannan shekara na 2023 ne manhajojin samar da ire-iren waɗannan hotuna suka fi yaɗuwa da yawaita.  Musamman manhajojin wayar salula. Akwai waɗanda ake amfani dasu wajen gyara hoto. A nan ba wai ƙara kayan kwalliya nake nufi ba (wato Filter), ina nufin canza hoton gaba ɗayansa.  Idan ka gani ma abin da zai sa ka iya gane wanda ke hoton shi ne fuska da yanayin jiki.  Amma daga kayan kwalliyar zuwa inda aka ɗauki hoton duk za ka samu sun sha bamban. Kuma hoto ne na zahiri aka ɗora amma sai manhajar ta sauya tsari da kintsin hoton gaba ɗaya.  Daga cikin manhajojin wayar salula da mutane ke amfani da su wajen ƙayatar da hotuna ta amfani da fasahar AI, akwai manhajar “PhotoLab”.  Galibin ‘yan mata da samari na amfani da wannan manhaja a kafafen sada zumunta don ƙayatar da hotunansu kafin lodawa a shafi.

Bayan waɗannan hotuna da fasahar AI ta sawwaƙe samar dasu, akwai bidiyo da har wa yau ake iya samarwa kai tsaye.  Sannan cikin wannan shekara ta 2023 ne aka samu yawaitar yaɗuwar bidiyon bogi da ake iya samarwa ta amfani da hotuna.  Waɗannan nau’ukan hotuna da bidiyo da ake haɗewa su ake kira: “Deep Fakes”.  A zahiri bidiyo ne zaka gani, na mutumin da ka sani, a inda ka san zai iya kasancewa, yana kuma magana.  Amma zaka ji maganganu ne kan abubuwa marasa daɗi ko dacewa.  Sabo da daman masu haɗa irin wannan bidiyon suna ƙirƙirarsu ne don cin ma wata manufa dake da alaƙa da siyasa.

Yaɗuwar hotunan bogi da ake iya ƙirƙira da fasahar AI, da yaɗuwar bidiyon nau’in Deep Fakes na cikin manyan matsalolin da bunƙasar fasahar samar da bayanai kai tsaye na AI (Generative AI) ta samar tare da taimakawa wajen yaɗuwarsu a duniya a shekarar 2023.  Kuma hakan na kan tayar da ƙura a duniya ma gaba ɗaya, musamman a tsakanin masana harkar shariah, da siyasa, da malaman jami’a, da likitoci, da fannin zane da samar da bayanai.  Ta wace hanya za a iya gane gaskiyar hotunan dake yawo a Intanet?  Domin a halin yanzu matsalar ta fara gamewa.  Hatta a shafin neman bayanai na Google (Google Search), idan kaje neman bayanai masu alaƙa da hotuna, duk za ka samu ire-iren waɗannan hotunan su ma.  Amma ba kowa ke iya gane cewa na bogi bane.

Mafi illa cikin waɗannan hotua da bidiyo su ne waɗanda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta don muzanta wasu ko wani, da manufar siyasa ko garkuwa da mutuncinsu.  Ire-iren waɗannan hotuna da bidiyo sun fi saurin yaɗuwa kamar wutar daji, saboda samuwar hanyoyin aikawa da karɓansu cikin sauƙi, kamar su Facebook Chat ko Messenger, da Facebook Pages, da WhatsApp, da Instagram, da dai sauran hanyoyi makamantansu.  Illa ta biyu kuma, bayan yaɗuwarsu, ba kowa ke iya gane cewa hotuna ne na bogi ba.

A taƙaice dai, fasahar AI ta sauya tunani da mahangar rayuwar al’umma ta ɓangaren hanyoyin ƙirƙira da samar da hotuna da bidiyo, ko dai daga asalin hotuna na gaskiya ko waɗanda ake iya ƙirƙira daga babu, don ruɗi ko wasu manufofi na siyasa ko na ƙashin kai.  Babbar damuwar ita ce, idan irin wannan ɗabi’a ta yawaita sanadiyyar yaɗuwa da take yi a halin yanzu, ta wace hanya za a iya gane gaskiya daga ƙaryar dake ƙunshe cikin waɗannan hotuna?

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.