Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (4)

Na 1:  Bayyanar Fasahar “ChatGPT 3.5”

Fasahar ChatGPT na farko da aka ƙaddamar ita ce zubi na 3.5 – ChatGPT 3.5 – cikin watan Nuwamba, 2022 kamar yadda bayani ya gabata a sama.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 26 ga watan Janairu, 2024.

299

Na 1:  Bayyanar Fasahar “ChatGPT 3.5”

Duk da cewa an ƙaddamar da fasahar ChatGPT ne a watan Nuwamba na shekarar 2022, duniya bata hankalci tasirin fasahar ba sai farkon shekarar 2023.  Ba wai fasahar AI ce ba a sani ba, sai dai yadda aka yi amfani da ita sauya akalar samar da bayanai, da sarrafa su, da kuma juya su daga asalinsu zuwa wani sabon asali da har yanzu masana basu tantance mai haƙƙi ba.  A baya ana amfani da fasahar AI ne wajen gadar wa na’urorin sadarwa tsarin tunani ta ɗan adam. Fasahar ChatGPT ma haka take, amma nata tsarin ya sha bamban.  Manhaja ce da zaka iya ma’amala da ita ta hanyar rubutattun umarni, tana baka amsa.  Tana iya baka shawara kan abin da ka tambayeta, kuma tana iya samar da bayanai daga babu.  Kuma maimakon kaje shafin Google kana neman bayani kan wani abu, kawai tambayi ChatGPT, za ta kawo bayanin a sigar hira da zance, har ma ta maka ƙarin bayani.

Fasahar ChatGPT na farko da aka ƙaddamar ita ce zubi na 3.5 – ChatGPT 3.5 – cikin watan Nuwamba, 2022 kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Wannan fasaha dai an samar da ita ne ta hanyar koya mata tsarin tunani da ganewa, da nazari, da hankalta, da kuma fahimtar bambancin dake tsakanin bayanai – sauti, ko rubutu, ko hoto, ko bidiyo ko zane – da fahimtar alaƙarsu, da iya haɗa alaƙar da ta fahimta a tsakaninsu, da kuma yin hukunci daga abin da ta fahimta na waɗancan ƙa’idoji.  Abincin ta dai ba komai bane illa tarin bayanan da kamfanin ya samar daga Intanet, ya taskance mata su, kuma akansu take nazari.  Don haka, idan ka umarceta ta kawo maka tarihin duniya misali, tuni daman ta daɗe da yin nazari kan tarin bayanan da aka koya mata tsarin tunani a kai.  Sai kawai ta rairayo maka tarihin duniya daga bayanan da ta saba karantawa waɗanda aka horar da ita a kai.  Haka idan kace ta baka labari, sai kawai tayi amfani da abin da ta koya daga irin labaran da aka tara mata aka horar da ita akai, sai ta tsara maka labarin da babu wanda ya taɓa rubutawa a duniya.  Idan ma ɗalibin jami’a ne kai aka baka aikin gida ko nazari kan wani maudu’i na ilimi.  Kana shigar mata da tambayar, ka tsara shi yadda kake son amsar ya kasance, cikin ƙasa da minti guda za ta cillo maka amsa; kai tsaye.  Tana gama turo maka amsa kawai sai dai ka karanta ko ka kwafa, ka canza shi iya yadda kake so ko zai dace da yanayin da malaminka ke so.  Wannan shi ne abin da fasahar ChatGPT tazo dashi.

Wannan yunƙuri na kamfanin OpenAI dai ya ta da ƙura a duniyar fasahar sadarwa a lokacin.  Nan take hankalin kamfanin Google ya dugunzuma; sun ɗauki hakan a matsayin wani yunƙuri ne na kashe babbar manhajar neman bayanai na Google Search.  Daga nan fa gasa ta buɗe tsakanin manyan kamfanonin sadarwa na duniya kan wannan sabuwar fasaha ta samar da bayanai kai tsaye.

- Adv -

Cikin watan Fabrairun 2023, sai ga kamfanin Google da tasa sabuwar fasahar da ya sanya wa suna: “Google Bard”.  Kai tsaye, ya barɓi ƙalubalen da kamfanin OpenAI ya masa ne.  A tare da cewa fasahar Google Bard ko kusa bata kai na ChatGPT ba, sai dai masana a lokaci suka ce lokaci ne kawai.  Domin kamfanin Google na da damammaki da yawa da zasu taimaka masa wajen haɓaka wannan sabuwar fasaha.  A taƙaice ma dai, gaba ɗayan bayanan dake giza-gizan sadarwa na duniya, wato: “World Wide Web”, suna tafin hannunsa ne.  Abin nufi, manhajar Google na iya rairayo kusan dukkan bayanan dake Intanet don amfani dasu wajen inganta wannan fasaha tasa ta Google Bard.

Cikin watan Fabrairun 2023 ne har wa yau shi ma kamfanin Microsoft ya samar da tasa fasahar mai suna: “Microsoft Bing Chat.”  Duk da cewa shafin Microsoft Bing shafi ne dake ɗauke da manhajar neman bayanai (Search Engine), amma sabo da alaƙar dake tsakanin kamfanin Microsoft da kamfanin OpenAI da ya samar da fasahar ChatGPT, cikin sauƙi Microsoft ya samar da wannan fasaha. Wannan ma ya daɗa sauya tsarin samar da bayanai a duniya a Intanet a wannan shekara.  Nan take duniya ta ɗauka. Saboda yadda fasahar AI ta buɗe wani sabon shafi a tarihin samar da bayanai a Intanet.

Wannan gasa tsakanin manyan kamfanonin sadarwa na duniya kan wannan sabuwar fasaha ta samar da bayanai na AI (Generative AI) dai, shi ne abu na farko da ya fara sauya tunanin duniya kan tsarin samar da bayanai a Intanet.  A tare da cewa waɗannan fasahohi na AI da aka samar – tsakanin OpenAI da Google da Microsoft – suna da naƙasa ta wani ɓangare.  Misali, kana iya mata tambaya kan wani abu, amma ta baka amsa kan wani abu daban.  Ko ɗauki rubutun da kaine ka rubuta, ba ɗauko shi kayi ba daga Intanet, kace mata: “Shin, wannan rubutun dake ƙasa, ke ce kika rubuta shi?”  Nan take za ta ce maka “Eh, lallai nine na rubuta waɗannan bayanai.”  A tare da cewa ƙarya ce.

Wannan yanayi na rafkanuwa ko shirme, shi ake kira: “AI hallucinations”.  Kuma an ta samun hakan daga kusan dukkan fasahohin da aka samar guda ukun farko da bayaninsu ya gabata.  Wannan ne ma yasa kamfanonin duka basu gushe ba wajen ƙoƙarin inganta fasahohin nasu.

Ana shiga watan Maris, sai kamfanin Google ya ƙaddamar da wata fasaha da ya kira da suna: “Google Gemini”, wanda nau’i ne na fasahar AI da yake son ya tsofa a fasaharsa mai suna Google Bard.  Kamfanin ya sanar da wannan sabuwar fasaha ne a taronsa na shekara da yake gudanarwa mai suna: “Google I/O”.  Wannan ya ƙara ƙaimin gasar dake tsakanin waɗannan kamfanoni.  Daga nan hukumomi da masana a jami’o’i suka fara nazarin tasirin wannan gasa, da abin da zai iya wakana idan ire-iren waɗannan fasahohi suka yawaita, kuma suka basirarsu wajen tantancewa da samar da bayanai suka ƙara ƙarfi da kaifi.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Ahmad Said Muhammad says

    Assalamu Alaikum Warahmatullah gaskiya ina matukar ƙaruwa da wannan maƙalolin Allah ya saka da mafifincin Alkhairi Allah ya ƙara basira.

    1. Baban Sadik says

      Amin. Mun gode sosai. Allah sa albarka cikin abin da ake fa’idantuwa dashi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.