Saƙonnin Masu Karatu (2022) (15)

An buga wannan maƙala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 25 ga watan Nuwamba, 2022.

397

A yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu kamar yadda muka faro makonni 12 da suka gabata.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

—————————

Assalamu alaikum Baban Sadiƙ, da fatan kana lafiya kuma yaya aiki?  Tambayata ita ce: Don Allah waye ya fara tafiya duniyar wata?  Saƙo daga Muhammad Leren Bauchi: 09048028711.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Muhammad.  Shekaru uku da suka gabata ne aka yi bikin cika shekaru 50 na waɗanda suka fara zuwa duniyar wata daga wannan duniya tamu.  Dangane da haka ne ma sashen Hausa na DW dake Jamus suka tattauna dani na tsawon mintuna wajen 10 don yin sharhi kan mahimmancin wannan rana ko shekara, da irin ci gaban da aka samu tun sannan, da kuma darasin da ƙasashe masu tasowa musamman ƙasarmu Najeriya za ta iya ɗauka.  An kwashe tsawon watanni ana tarurruka da bukuwa kan hakan, farawa daga ranar Talata, 16 ga watan Afrailu, 2019 zuwa Janairu na shekarar 2020.

An fara zuwa duniyar wata ne a ranar 16 ga watan Yuli na shekarar 1969, sadda hukumar Cibiyar Binciken Sararin Samaniya na ƙasar Amurka wato NASA, ta harba kumbo ɗauke da motocin ziyara a sararin samaniya (Lunar Rovers) guda 3, don aika ƙwararru su gano abin da Allah ya tanada a duniyar wata, wato tauraron wannan duniyar tamu kenan.  Wannan tawaga na mahaya dai ta kwashe tsawon kwanaki huɗu ne bayan tashinta daga cibiyar da aka harba ta zuwa sararin samaniya, ta kuma isa duniyar wata a ranar 20 ga watan Yuli, shekarar 1969.  Wannan ke tabbatar da cikan shekaru na 50 kenan da faruwar wannan lamari.

Tun daga wancan lokaci ƙasashe suka fara gasa da juna wajen zuwa duniyar wata da shuka taurarin ɗan adam don manufofi daban-daban.  Bayan ƙasar Rasha ta aika kumbonta ɗauke da wani ƙwararren mahayin kumbo mai suna Yuri Gagarin, mutum na farko da ya fara shiga sararin samaniyar wannan duniya tamu a shekarar 1961, sai ƙasar Amurka ta aika da tawagar farko ɗauke da su Neil Armstrong da Buzz Aldrin da kuma Michael Collins, zuwa duniyar wata a shekarar 1969.  Daga nan aka samu ƙasashe da dama irin su Burtaniya su ma suka aika nasu.  Abin da ya fara daga zuwa duniyar wata, wanda shi ne tauraron wannan duniyar tamu, ya zuwa yanzu an kai ziyara zuwa duniyoyi guda 6, da kuma duniyar watanni guda 3.

- Adv -

Dangane da haka hukumar NASA ta ƙasar Amurka ta shirya waɗancan bukukuwa da tarurruka da bitoci kan wannan al’amari, wanda ta fara tun cikin watan Afrailu na shekarar 2019, ya kuma zarce har zuwa watan Janairu na shekarar 2020.  Duk wannan don ƙara faɗakar da jama’a ne mahimmancin dake cikin wannan al’amari.  Ba hukumar NASA kaɗai ba, kafafen yaɗa labarai na gwamnatocin ƙasashe da masu zaman kansu, da jaridu da mujallu musamman na kimiyya da sararin samaniya, duk sun rubuta maƙaloli da dama don nuna murna da zagayowar wannan rana.  Daga cikin kafafen yaɗa labaru na rediyo da talabijin da suka baiwa wannan rana da lokaci mahimmanci akwai kafan sadarwa ta BBC dake ƙasar Burtaniya, da tashar DW Radio dake ƙasar Jamus.

A taƙaice dai, wanda ya fara zuwa sararin samaniya ta hanyar kumbo shi ne Yuri Gagarin ɗan ƙasar Rasha a shekarar 1961.  Waɗanda kuma suka fara zuwa duniyar wata, kamar yadda ka tambaya, su ne Neil Armstrong da Buzz Aldrin da kuma Michael Collins; dukkansu ‘yan ƙasar Amurka ne, kuma wacce ta ɗauki nauyin wannan aiki ita ce hukumar NASA na ƙasar Amurkan.  Da fatan ka gamsu.

Assalamu alaikum Baban Sadik, ni dalibi ne mai bibiyar shafinka a jaridar AMINIYA.  Ina so nayi karatu in zama fasihi kamar ka. Don Allah ka bani shawarar yadda zan bi. Na gode.  Daga Ibrahim Idris Auwal Jos, Plateau State. 07034506123.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ibrahim.  Wannan na cikin maimaitattun tambayoyi da ake mini.  Kuma shawarar da nake bayarwa dai ita ce a dage, a kuma samu tsari na musamman.  Abin da wannan ke nufi shi ne, na farko ya zama kana da sha’awan fannin da kake son ƙwarewa a kai.  Na biyu kuma a dage da karatu.  Zuwa makaranta ko shagaltuwa da aikata abin da aka koya a aikace, suna cikin abubuwa masu tasiri.  Sannan sai naci da juriya.  Shi karatu don ƙwarewa a wani fanni na ilmi yana buƙatar haƙuri da juriya ne.  Sai kuma naci, da rashin gazawa.  A wasu lokuta za ka ga kamar aikin banza kake yi.  Ko kuma abin da kake karantawa ba shi da amfani, watakila saboda yadda mutane suka shagala da wasu abubuwa masu ɗaukan hankali da ake samun kuɗi ko shahara a kansu.  Idan wannan yasa ka bar abin da ke gabanka ka tsallaka wancan ɓangare, sai a samu matsala.

Bayan haka, shi ilimi a wannan fanni na kimiyya da fasahar sadarwa yana buƙatar aikatawa a aikace.  Hakan kuma ba ya yiwuwa sai ta hanyar mallakar mahallin da zai taimaka maka wajen kwatanta abin da kake karanta.  Misali, idan kana sha’awar koyon yadda ake gyaran wayar salula ne, kuma kana ta karatu kan hakan.  Ka sani, wannan bazai wadatar dakai ba, ba kuma zai sa ka zama ƙwararre ba sai ka mallaki na’urorin da ake buƙata wajen aikin gyaran waya, sannan ka riƙa kwatanta abin a aikace, musamman ma idan ba wani bane ke karantar dakai.

A ƙarshe, dole a haɗa da addu’a.  Kamar yadda na sanar a baya ne, shi karatu yana da gundura.  Wasu lokuta za ka ji kamar ma ka watsar da komai.  Amma idan ana haɗawa da addu’a, sai Allah Yasa maka ɗabi’ar jajircewa, da son abin fiye da komai.  Yana cikin abubuwan da ban gushe ba ina wa Allah godiya a kansu, shi ne, tun ina ɗan firamare Allah Yasa mini son karatu da rubutu.  Waɗannan ɗabi’u biyu sun taimaka mini matuƙa wajen samun kaina a matsayin da nake a halin yanzu.

Wannan shi ɗan abin da zan iya cewa.  Ina maka fatan alheri. Allah ya cika maka burinka da dukkan ‘yan uwa baki ɗaya, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.