Sakonnin Masu Karatu (2021) (8)

Tsarin Adana Bayanai a Intanet

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 12 ga watan Maris, 2021.

640

Assalamu Alaikum Baban Sadik.  Don Allah ina son kasida kan nau’in kudin da ake kira:  “Cryptocurrency” ko inda zan samu cikakken bayani.  Na gode.  Daga Musa Hamisu

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Hamisu Musa.  Har yanzu ban rubuta wata Makala ta musamman kan wannan sabuwar fasaha mai dauke da sabon nau’in kudi ba.  A takaice ma dai, wannan shi ne maudu’in da zan ci gaba da rubutu a kai da zarar na gama amsa tambayoyin masu karatu da nake aikowa a halin yanzu.  Kafin nan, zai dace idan har baka fara mu’amala da wannan sabon nau’in kudade ba, ka dan dakata har sai ka yi karatu ka kuma fahimci yadda tsarinsa yake tukun.  Domin akwai wasu nau’ukan kasuwanci na karya da ake danganta su da wannan nau’in kudi na Cryptocurrency a Najeriya da sauran kasashe masu tasowa.  Kada ka rudu da abubuwan da wasu za su nuna maka cewa riba ce suka samu sanadiyyar “zuba jari” da suka yi a wannan bangare, musamman idan wani ne suka bashi kudi kuma yake aiko musu da kudade a duk mako ko karshen wata.

In Allah Yaso, nan da makonni uku masu zuwa zan fara bayani filla-filla kan asali da tarihin nau’in kudaden da ake ta’ammali dasu a Intanet da kuma tsarin hada-hadar kudi ta kafafen sadarwa na zamani.  Ba bayani bane da za a iya yinsa a mako guda a fahimta.  Don haka, kana iya jinkiri ko kuma idan ka dauki shawarar da na baka, ka kutsa cikin duniyar Intanet don neman Karin bayani da gamsarwa.  Allah sa mu dace baki daya, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Tambayata ita ce, shin mutum zai iya adana bayanai ko karatuttukan sauti na tafsiri da wakoki a akwatinsa na Imel?  Ko dai sai ta tashar Youtube kadai?  – Ahmad Abubakar, Jigawa: 09013709952

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ahmad.  Dangane da tambayarka cewa ko mutum zai iya adana sakonnin sauti ta akwatin Imel ko sai ta Youtube, wannan ai ba mahallinsu bane.  A kafafen sadarwa na Intanet komai yana da mahallinsa, musamman a wannan zamanin da abubuwa suka habbaka sosai.  Ita manhajar Imel an yi ta ne don aika rubutattun sakonni da hotunan da mizaninsu ba shi da girma sosai.  Wadannan su ne nau’ukan bayanan da galibi ake adana su ta hanyar aikawa da karba, a wannan manhaja.  Aika sakonnin sauti masu nauyi ko adana su ta Imel, ba abu bane mai kayatarwa.  Domin idan sakon na da nauyi, ba lalai bane ya hau kan manhajar.  Domin akwai iya mizanin nauyi da aka tanadar wa kowane irin sako ne da kake son Makala shi a Imel.

Don haka, idan kana son adana sakonnin bidiyo ne ko dai ka ajiye su a kan wayarka, ko ka samu ma’adanar filash, ko kuma ka bude tasha a Youtube don adana su jama’a su kalla, idan don jama’a ne.

- Adv -

Idan kuma yin hakan zai baka wahala, kana iya yin rajistan adireshin Imel na Gmail idan ba ka dashi.  Yin rajistan adireshin Gmail zai baka damar mallakar ma’adanar bayanai mai mizanin 15GB, ta hanyar manhajar Google Drive.  Sai ka sayi data kawai, ka dora dukkan bayanan da kake dasu na sauti ko na bidiyo a wannan manhaja.  A duk sadda ka tashi bukata sai kawai kaje can ka dauko ko ka saurara.  Haka duk wasu bayananka da ka mallaka, kana iya dora su a wannan manhaja.  Kai tsaye za ka iya riskarsu a duk sadda kake bukata, muddin kana da data a wayarka.

Wannan shi ne dan bayanin da ya sawwaka.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban sadik,barka da warhaka.  Sunana Abdulhamid Baba Alkali.  Ni dalibi ne mai karatu a kan fannin fasahar na’ura mai kwakwalwa (Computer Science).  A gaskiya ni mutum ne wanda Allah ya sa wa sha’awar bincike akan fannin Computer, musamman ma akan fannin tunani akan yadda ake kirkirar manhajar waya da ta kwamfuta.   To amma ina fuskantar wasu matsaloli da na kasa gano kansu kamar haka: (1) Shin, ta yaya mutum zai iya yin tunanin kirkiro wata manhajar da babu ita?  (2) Shin, ta yaya mutum zai iya juyar da matsalolin rayuwa na dan adam zuwa manhajar kwamfuta?  (3) Ta wace hanya masana gina manhajar kwamfuta ke tafiyar da aikinsu bai daya?  Na gode, Allah kara lafiya da tsawon kwana da kuma sani.  – Abdulhamid Alkali: alkaliabdulhamid@gmail.com 

Wa alaikumus salam, barka da Malam Abdulhamid.  Ina maka fatan alheri.  Na fahimci kana da sha’awar fannin gina manhajar kwamfuta ne, wato: “Programming” ko kuma “Software Engineering”, daga irin salon tambayoyin da ka mini.  Da farko dai, tunda ka ce kana karantar fannin Kwamfuta ne, wato “Computer Science”, na tabbata akwai kwas na musamman da ya kamata ana muku kan wannan maudu’i.  Duk da haka, shi tunani kan yadda ake kirkirar manhajar kwamfuta na samuwa ne ta hanyar nazarin bangaren da dalibi ke da sha’awa a fannin.  Sannan da bibiyar ayyuka ko manhajoji makamantan wadanda kake sha’awar samarwa.  Sannan ka kalli al’ummar da kake rayuwa cikinta kaga ta wace hanya za ka iya samar da wani abin da wani bai taba samarwa ba, na ci gaba?  Ko kuma ta wace hanya za ka iya inganta wani abin da aka samar wa al’umma wanda ke dauke da wata nakasa?  Wadannan su ne hanyoyin da ake bi wajen samar da fikira mai inganci don gina manhaja mai ma’ana da manufa.  Sannan ta hakan ne zaka samu damar juya amsoshin wadannan tambayoyi da tunani zuwa manhajar kwamfuta ko wayar salula.  Abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Wannan shi ne amsar tambayarka ta farko da ta biyu.

Dangane da tambayarka ta uku kuma kan hanyoyin da magina manhajar kwamfuta ke bi wajen tafiyar da ayyukansu, wannan kuma wani fanni ne mai zaman kanshi.  Shi ma, kamar na farkon, duk yana cikin abubuwan da suka kamata a koya muku.  Wannan fanni shi ake kira: “Project Management”, kuma mafi ingancin hanyar da ake amfani da ita yanzu ita ake kira: “Agile”.  Bayani kan hakan abu ne mai fadi.  Kana iya bincikawa a Intanet don samun Karin bayani.

Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.