Sakonnin Masu Karatu (2019) (13)

Yadda Na'urar Tauraron Dan Adam ke Aiki

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na ranar Jumma’a, 27 ga watan Satumba, 2019.

78

Salamun alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya.  Ni ma’abocin karanta shafinka ne, amma ban taba rubuto tambayata ba sai yau.  Ina son in san ta yaya nau’in tauraron xan adam na sadarwa yake aiki ne wajen nuna tashoshin talabijin? Saboda abin yana bani mamaki ne.  Daga Abubakar Sa’idu Xankanjiba: 08136346418

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abubakar.  Mun daxe muna kwararo bayanai kan ma’ana da tarihi da tsarin gudanuwar tauraron xan adam, sama da shekaru bakwai da suka gabata, a wannan shafi mai albarka.  Cikin bayanan da muka yi mun nuna akwai nau’ukan tauraron xan adam, wanda daga ciki aka samu na harkar sadarwa.  Tauraron xan adam ne da aka harba shi sama, watsa bayanan sadarwa na sauti ko hoto mai motsi, watau bidiyo kenan.  Waxannan nau’ukan taurarin xan adam su ake kira: “Communication Satellites”.  Kuma su ne suke cilla shirye-shiryen gidajen talabijin na tauraron xan adam, wato “Satellite TV Channels” daga qasashen da ake harba ko watsa su.

Waxannan shirye-shirye dai ana loda su ne daga cibiyar watsa shirye-shiryen, sannan a haska su ta amfani da waxannan taurarin xan adam da aka riga aka harba su tun da jimawa, suna shawagi a cikin falaki ko sararin samaniya.  Duk shirin da aka loda, ana saita masa lokacin da tauraron zai nuna shi, da ranar da ake son shirin ya bayyana ga masu kallo.  Misali, shiryen-shiryen talabijin din Hausa na Sunnah TV misali, ana cilla su ne daga tashar watsa shirye-shirye dake qasar Nijar.

A halin yanzu dai akwai taurarin xan adam masu dimbin yawa a cikin sararin samaniya, waxanda aka cilla su don aiwatar da ayyuka daban-daban.  Akwai na gano bijire, waxanda galibin manhajar taswirar duniya ke amfani dasu, irin su: “GPS” na qasar Amurka, da “GLONASS” na qasashen Turai da dai sauransu.  Bayani kan haqiqanin yadda abin ke faruwa ko aukuwa kuma, wannan wani darasi ne mai zaman kasan.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

Assalamu Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya. Don Allah idan mutum ya saci Pin dinka na katin banki, shin, zai iya sace kuxinka ba tare da ya sami katin ATM ko wayarka ba? Ka huta lafiya. Daga Misbahu Ibrahim Musa Fagwalawa: 08079903302

Wa alaikumus salam, Malam Misbahu barka ka dai.  Masu irin wannan mummunar dabi’a suna da hanyoyi da dama da suke bi wajen aiwatar da badakalarsu.  Kamar yadda Malam bahaushe ne kan ce: “Mai son kayanka ya fi ka dabara”.  Abu ne mai yiwuwa tabbas wanda yasan PIN din katinka na ATM ya iya sace maka kuxi ba tare da ya samu katinka na ATM ba, kuma ba tare da ya san lambar wayarka ba.  Wato a wannan zamani na sadarwa, su bayanan da suka shafi mutum suna da alaqa ne da junansu.  Misali, idan mutum yasan adireshinka na Imel, ko sunan da kake amfani dashi wajen hawa shafinka na Facebook, to, zai iya kirdadon kalmar sirrinka, wato: “Password” kenan, iya gwargwadon abin da ya sani dangane da rayuwarka.

A bangaren barayin banki ta kafafen sadarwa na zamani, ko ba’a samu katinka na ATM ba, ana iya kera makamancinshi cikin sauki.  Wannan shi ake kira: “ATM Card Cloning”; kamar ayi wani abu makamancin naka, amma kuma asalinsu daban-daban ne.  Abin da zai hada alaqa tsakaninsu kawai shi ne bayananka na banki.  Misali, lambar taskar bankinka, wato: “Account Number”, ko lambar katin ATM dinka, wato: “ATM Serial Number”.  Idan nace lambar katin ATM ba ina nufin “PIN” dinka bane.  A a.  waxannan dogayen lambobin nan guda 16 ko 14 dake kan katinka na ATM.  Suna da amfani matuka a wajen dan dandatsa.  Domin ko hajoji za ka saya a kafafen sadarwa na zamani, da waxannan lambobin ne ake iya gane cewa kana da taskar ajiya a wani banki, kuma akwai kuxi a ciki, da waxannan lambobin ake iya tuntubar bankinka don su ba da umarnin a cire kuxi daga taskar ajiyarka.  Shi yasa, idan ka taba aiwatar da cinikayya ta hanyar amfani da katinka na ATM, za ka ga bankinka ya aiko maka wasu lambobi da ake son ka shigar a inda kake son biyan kuxi.

A taqaice dai, abu ne mai yiwuwa a iya sace kuxin mutum daga taskar bankinsa ba tare da an sace katinsa na ATM ba.  Kawai ya danganci irin bayanan da barawon ya samu ne dangane da taskarka ko katinka na ATM.  Shi yasa bankuna suke wayar mana da kai a kullum, cewa, baza su taba aiko maka saqo don ka basu lambar taskarka na banki ba (don suna dashi kuma sun sani), ko katin sirrin ATM dink aba (don basu buqatan wannan bayanin wajen magance maka wata matsala), ko lambar katin ATM dink aba (don sun sani, kuma suna da shi).  Duk sadda ka samu saqo ta waya ko Imel dake cewa ka aika bayanan katinka na ATM ko lambar taskar bankinka ga wata lamba ko wani adireshi na Imel, ko ka matsa wata rariyar lixau (Internet link) don shigar da waxannan bayanai a wani shafi na musamman, to, ka san cewa wannan saqo ne na bogi.  Kuma idan ka bayar, duk abin da ya sameka na asarar kuxi da mutumci, ba ruwansu.

Da fatan za a kiyaye.  Wannan shi ne dan taqaitaccen jawabin da zan iya baka a yanzu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.