Hanyoyin Cin Gajiyar Fasahar AI (1)

Fasahar AI a Duniyar Yau

Bayan samuwar wannan fasaha a gine cikin na’urori da hanyoyin sadarwar zamani, a halin yanzu manyan kamfanonin sadarwar zamani sun ƙirƙira tare da gina manhaja ta musamman dake iya fahimtar umarnin da za ka bata – rubutu ne, ko hoto ko sauti, ko bidiyo – don samar maka da irin bayanan da kake buƙata cikin sauki.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 22 ga watan Disamba, 2023

60

Fasahar AI a Duniyar Yau

Duk da cewa wannan fasaha ta samo asali ne shekaru 50 da suka gabata, sai dai samunta a aikace don amfani da ita a zahirin rayuwa bai samu ba sai cikin wannan lokaci da muke ciki.  Fasahar “Artificial Intelligence” ko AI a gajarce, tsari ne da ake amfani dashi wajen koya wa na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani yin tunani, da hangen nesa da kuma yanke hukunci ta amfani da dandazon rubutattun bayanai, da sauti, da hotuna da kuma bidiyo.  Wannan fasaha dai a halin yanzu tana kan bunƙasa ne, kuma da wahala ka samu wata na’urar sadarwa ta zamani – tun daga kan kwamfuta, da wayar salula, da manyan nau’ukan wayar salula irin su iPad, da Tabs, da ƙananan na’urorin amfani masu iya aiwatar da sadarwa irin su agogo da na’urorin dafa abinci da sauransu – wacce babu ɗarsasin wannan fasaha a tare da ita.

A ɗaya ɓangaren kuma, kusan dukkan hanyoyin sadarwa na zamani suna ɗauke da wannan tsari na AI a gine a cikinsu.  Hanyoyin dai galibi ba wasu bane illa irin su fasahar Imel, wacce ake aikawa da kuma ƙarban saƙonni ta cikinta, da sauran kafafen sadarwa irin su manhajojin gidan yanar sadarwa da ake kira “Web Apps”, da dai sauransu.

Manyan Jiga-Jigai: ChatGTP da Bard

Bayan samuwar wannan fasaha a gine cikin na’urori da hanyoyin sadarwar zamani, a halin yanzu manyan kamfanonin sadarwar zamani sun ƙirƙira tare da gina manhaja ta musamman dake iya fahimtar umarnin da za ka bata – rubutu ne, ko hoto ko sauti, ko bidiyo – don samar maka da irin bayanan da kake buƙata cikin sauki.  Wannan nau’in fasaha na AI da ake kan ginawa yanzu dai ana kiransu “Large Language Models” ko “LLMs” a gajarce.  Tsari ne dake karɓan umarni da a harshen sadarwa ake kira: “prompts”, don sarrafa umarnin da miƙo amsar abin da umarnin ke buƙata kai tsaye, cikin ƙanƙanin lokaci.

Shahararu cikin waɗannan nau’ukan fasahohi da aka gina dai su ne: Fasahar ChatGPT wanda kamfanin OpenAI ta haɗin gwiwa da kamfanin Microsoft.  Sai kuma Fasahar Bard na kamfanin Alphabet (Google Inc.), wanda shi ma a makon jiya (Laraba, Disamba 13, 2023) aka ƙara inganta shi ta hanyar wata sabuwar fasaha mai suna Google Gemini, wanda a cewar kamfanin Google, ta shallake dukkan sauran sa’o’inta wajen iya fahimtar saƙo, da sarrafa shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Fa’idoji

- Adv -

Waɗannan hanyoyin sarrafa bayanai dake maƙare cikin waɗannan nau’ukan fasahar AI sun samar da wata sabuwar hanya fa’idantuwa da hanyoyi da na’urorin sadarwa ne.  Kamar yadda masu karatu suka sani ne, su hanyoyi da na’urorin sadarwa suna taimakawa ne wajen samar da hanyoyin warware matsaloli da ƙalubalen da ɗan adam ke fama dasu wajen ci gaban rayuwarsa ne. Ga kaɗan cikin fa’idojin da suke samarwa a taƙaice:

A ɓangaren karatu, saɓanin shafukan yanar sadarwa (Websites) da za kaje ne karanta abin da ka tarar mai shafin ya zuba, a fasahar ChatGPT ko Bard, hira za ka yi da manhajar, kai ka ɗauka wani mai baka shawara ne. Ka tambayeta duk irin tambayar da kake da ita.  Ita kuma za ta baka shawara.  A ɓangaren neman ilmi, za ka iya neman kan kowane fanni; ta hanyar tambaya, ko ta hanyar neman ƙarin bayani.  Haka idan akwai wani littafi da kake son a taƙaita maka shi don fahimtar saƙon dake cikinsa cikin sauƙi, sunan littafin kawai za ka ambata. Nan take zata rairayo maka abin da littafin ko maƙalar ko jawabin ya ƙunsa.

A ɓangaren hotuna kuma, kana iya loda mata hoto don neman ƙarin bayani kan abin da hoton ya ƙunsa, ko ta nemo maka hoto makamancinsa, ko kuma, ta maka rubutu na musamman kan hoton; duk tana iyawa.  Har wa yau, fasahar na iya ƙirƙiro maka hoto na musamman.  Misali, idan kana son rubuta maƙala ta musamman kan wani maudu’i, amma ba ka son zuwa Intanet neman hoto mai alaƙa da maudu’in maƙalar, kuma kai ba ka da hoto kan haka. Da zarar ka siffata mata maudu’in da cikakken bayani, za ta ƙirƙiro maka hotuna masu alaƙa da maudu’in da yawa; sai ka zaɓi wanda kaga ya fi dacewa da abin da kake son yin rubutu ko magana akai.

Ga ɗaliba da malaman jami’a da sauran makarantu kuma, wannan fasaha tana iya musu abubuwa na ban al’ajabi.  Kana iya siffata mata maudu’i na musamman da kake son ta maka rubutu akai, da tsarin da kake so, da yawan kalmomi ko haruffan da kake son maƙalar ta taƙaitu dasu, da ɓangarorin da kake son maƙalar ta ƙunsa.  Nan take za ta rubuta maka cikin ƙanƙanin lokaci.  Wani abin sha’awa ma shi ne, za ta iya kawo maka maƙaloli kamar uku – kamar yadda Fasahar Bard ke yi – ka zaɓi wanda kake so daga ciki.  Haka idan aikin gida aka ba ɗalibi a jami’a ko makarantar sakandare.  Wannan fasaha na iya rubuta masa komai yake buƙata.  Ba zallar rubutu kaɗai wannan fasaha ta ƙware a kai ba, har da lissafi.   Kana iya rubuta mata wata mas’ala ta lissafi, nan take za ta warware maka ita cikin sauƙi.  A taƙaice dai, a ɓangaren rubutawa da karantawa da fahimtar rubutu da tsara karatu, wannan fasaha na iya ƙoƙarinta.

A ɓangaren sauti kuma, wannan tsari ko fasaha na AI na iya fahimar sautin da aka loda mata, sannan idan ana buƙata, tana iya maka sharhi har da kanun labaru kan abin da sautin ya ƙunsa.  Bayan haka, tana iya naɗe maka sautin zuwa rubutu.  Wannan tsari shi ake kira: “Transcription.”  Aikin ta bai tsaya a nan ba kaɗai, tana iya fassara maka – iya gwargwadon yarukan da aka koya mata –  abin da ke ƙunshe cikin sautin sannan ta aiko maka kai tsaye.

A ɓangaren saƙonnin bidiyo kuma, fasahar AI na iya ƙera maka fina-finai daga umarnin da ka bata, cikin sauƙi.  Sannan tana iya saurara da karance maka dukkan saƙon dake cikin saƙon bidiyon da ka loda mata, ta kuma maka sharhinsa baki ɗaya.  Ba nan aka tsaya ba, hatta manhajar wasanni (Games app) tana iya ƙirƙira maka kai tsaye.

A ɓangaren ƙirƙirar bayanai zalla kuma, wannan fasaha na taimakawa wajen samar da rubutattu kuma ƙirƙirarrun labarai, da waƙoƙi, da manhajoji ma, da kuma ƙirƙirar wani tsari da babu shi, wanda za a iya siffata mata a rubuce.  Misali, wajen dafe-dafen abinci, kana iya lissafa mata nau’ukan kayan haɗin abinci, kace ta baka shawaran, abinci nau’i nawa za a iya yi da su?  Nan take za ta baka.

A makon gobe za mu bayani kan hanyoyin da mai karatu zai bi wajen fa’idantuwa da wannan fasaha ta AI, musamman fasahohi irin su ChatGPT da Bard.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.