Hayoyin Cin Gajiyar Fasahar “Artificial Intelligence” (3)

Na Ɗaya:  Samar da Dokoki

Hanyar tabbatacciya na cin gajiyar fasahar AI gaba ɗayanta shi ne ƙasashe suyi ƙoƙarin samar da dokokin ƙayyade ma’amala da wannan fasaha.   Dole ne dokokin su shafi dukkan ɓagarorin rayuwar al’umma ko fannonin rayuwa. – Jaridar AMINIYA, 29 ga watan Maris, 2024.

65

Hanyoyin Cin Gajiyar Fasahar AI

A maƙalar farko da ta biyu, munyi bayani kan haƙiƙanin fasahar AI, da haɗarorin da a zahiri take tattare dasu, muddin ba a ƙayyadeta ba.  A wannan karo za mu dubi hanyoyin da mai amfani da wannan fasaha ne, musamman fasahar manhajar Generative AI, irin su ChatGPT, da Google Gemini, da Microsoft Copilot, da Perplexity da dai sauransu.  Waɗannan manhajoji ne da za ka iya yin hira dasu, ka musu tambayoyi, ka nemi shawaransu kan wasu abubuwa da kake da ƙudurin aiwatarwa a rayuwa, su kuma ba ka shawara.  Idan bayanai kake so, nan take za su samar maka da bayanan.  Haka idan hotuna ne ko bidiyo ko sautin waƙoƙi, duk suna iya ƙirƙira sannan su tunkuɗo maka su.

Sai dai kuma  samun abin da muke so, a yadda muke son shi yana buƙatar nazari, da tsari, da kuma tanadi.  Domin waɗannan fasahohi dai ba mutane bane dake iya fahimtar yanayin fuskarka lokacin da kake musu tambaya.  Abin da ka rubuta musu na umarni, ko hoton da ka maƙala ka aika musu, shi suke nazarinsa, sannan su samar maka da abin da kake buƙata.  Don haka, abin da ka basu, shi suke turo maka sakamakonshi kai tsaye.

Don samun kyakkyawar sakamako gare mu ɗaiɗaikun mutane, da cin gajiyar wannan sabuwar fasaha a al’ummance a duniya, ga wasu matakai da suka kamata mu riƙe nan:

Na Ɗaya:  Samar da Dokoki

Hanyar tabbatacciya na cin gajiyar fasahar AI gaba ɗayanta shi ne ƙasashe suyi ƙoƙarin samar da dokokin ƙayyade ma’amala da wannan fasaha.   Dole ne dokokin su shafi dukkan ɓagarorin rayuwar al’umma ko fannonin rayuwa.  Kama daga fannin lafiya, da ilimi, da zamantakewa, da dokoki, da haƙƙin mallaka, da haƙƙin ɗan adam da dai sauransu.  Hakan zai taimaka matuƙa wajen tabbatar da tsari cikin lamarin, da samar da ƙarancin ƙorafe-ƙorafe a tsakanin mutane da kamfanoni, da tabbatar da haƙƙin mallaka ga waɗanda suka mallaki asalin fasahar dake maƙare a Intanet.

- Adv -

Dukkan waɗannan matakai za su taimaka wajen tabbatar da tsaro da kariya ga al’umma daga munanan tasirin wannan fasaha, kamar yadda ake hasashensu a yau.  Sannan za su samar da natsuwa a zukatan al’umma ta hanyar kare musu haƙƙoƙinsu.  Hatta kamfanoni da masu sana’o’i a kafafen Intanet, su ma za su amfana da waɗannan dokoki.  A ɓangaren marasa aikin yi kuwa, za a samu ƙarin hanyoyin dogaro da kai ga wanda ke da sha’awar wannan fanni na AI, sannan akwai kariya daga rasa aikin yi da waɗannan dokoki za su baiwa ma’aikatan dake yin ayyukan da ake ganin nan da wasu ‘yan shekaru wannan fasaha za ta laƙume su.

A halin yanzu dai babu wata gamammiyar doka aka samar a duniya dake ƙayyade wannan fasaha.  Hasali ma dai, ya rage ga kowace ƙasa ta samar da dokokin da take ganin za su kare mata al’ummarta ne daga haɗarin dake tattare da bunƙasar wannan fasaha.  Nahiyar turai (Europe) ce kaɗai a halin yanzu ta fitar da dokoki na musamman kan wannan fasaha ta Artificial Intelligence, waɗanda ake sa ran nan da wasu lokuta sauran ƙasashe da nahiyoyi za su bi sahun wannan nahiya.

Sai dai kafin nan, a ƙasashe masu tasowa galibin gwamnatoci na ƙoƙarin ganin al’ummarsu ta fahimci wannan sabuwar fasaha ne.  Sukan yi haka ta hanyar samar da gurabun karatu a jami’o’i don nazarta da naƙaltar wannan fasaha, da kuma bayar da tallafi ga ƙananan kamfanonin sadarwa (Tech Start-ups) don taimaka musu wajen gudanar da bincike da samar da fasahohin da za su taimaka wajen cin gajiyar wannan fasaha cikin sauƙi.  Wannan, a tunanin waɗannan hukumomi, shi ne matakin farko wajen ganin an fara cin moriyar wannan fasaha.

A nan Najeriya kusan hanyar da gwamnatin tarayya ta ɗauka kenan, ta hanyar hukumar Haɓaka Fannin Sadarwa ta Ƙasa, wato: Nigerian Information Techonology Development Agency (NITDA).  Bayan kwasa-kwasai da hukumar ke ba da tallafin karatu a kansu ta haɗin gwiwa da manyan kafafen ɗaukan karatu a Intanet, irin su Coursera da sauransu, a halin yanzu har tallafin kuɗi hukuma na bayarwa.  Bayan haka, akwai horaswa da hukumar NITDA ke bai wa ‘yan Najeriya a wannan fanni a cibiyoyinta na musamman, amma mazauna Abuja.  Mai karatu zai iya samun bayanai kan waɗannan ayyuka kai tsaye a shafin NITDA dake kafar “X” (Twitter).

A taƙaice dai, samar da dokoki masu ƙayyade tsarin ma’amala da wannan fasaha, tare da shimfiɗa ƙa’idojin ta’ammali da bayanan mutane ga kamfanonin dake samar da waɗannan fasahohi, zai taimaka matuƙa wajen samar da natsuwa ga al’umma, da hukumomin ƙasashe, da kuma su kamfanonin.  Ta wannan hanya ce kowa zai san haƙƙinsa.  Amma idan ƙasashe basu samar da dokoki na musamman don ƙayyade tsarin ma’amala ba, to, nan gaba hargitsi ne kawai za a samu.

Wannan dalilin ne ma yasa a halin yanzu ƙasashe da hukumomi ke samar da dokoki kan fannin Kiripto, wato tsarin hada-hadar kuɗaɗe na zamani da ake samarwa da aikawa da karɓansu ta hanyar kafafen sadarwa na zamani.  Domin idan ba a yi haka ba, ana jin tsoron nan gaba waɗannan kafafe na kuɗaɗen zamani za su bunƙasa har tasirinsu ya shafi bankunanmu da ma fannin hada-hadar kuɗi na zahirin rayuwa.  A ƙarshe kuma a shiga halin ni ‘ya su.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.