Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (7)

Haɗarin Fasahar AI

A farkon lokacin da aka samar da waɗannan fasahohi a shekarar 2023, bayanai sun nuna cewa an horar dasu ne daga tarin dandazon bayanan da kamfanonin da suka sama dasu suka fara.  Wannan shi ake kira: “Training Data”.  – Jaridar AMINIYA, 16 ga watan Fabrairu, 2024.

51

Na 4: Haɗarin Fasahar AI

Bayyanar zubin Fasahar ChatGPT 4 ke da wuya sai wasu gungun masana da duniya ke ji dasu wajen kimiyya da fasahar sadarwa su dubu ɗaya (1,000) suka rubuta takardar koke don kira ga hukumomin ƙasashen duniya da su dakatar da cibiyoyin bincike kan fasahar AI, daga ci gaba da bunƙasa wannan fasaha.  Wannan ya faru ne a watan Maris, jim kaɗan bayan fitar da zubin ChatGTP 4, da bayyanar Google Bard na kamfanin Google, da kuma manhajar zaƙulo bayanai na kamfanin Microsoft mai suna: “Microsoft Bing Chat”, wanda aka gina da ƙa’idojin fasahar ChatGPT.

Ƙorafin nasu na neman hukumomin duniya ne da su dakatar da ci gaba da bincike kan wannan fanni, musamman kafin fitowar zubin ChatGPT 5, da dukkan abin da zai biyo baya na ci gaba a wannan fanni.  Suka ce daga abin da ya fara bayyana na fasahar ChatGPT, da irin kaifin basirar da kwamfutoci ke samu saboda ci gaba a fannin ƙarawa da samar da masarrafar bayanai na kwamfuta da na’urorin zamani, nan gaba za a samu matsala idan na’urorin sadarwa suka fara tunani irin na ɗan adam, da ƙwarewa wajen gudanar da ayyuka fiye da ɗan adam.  Suka ce me zai faru idan kwamfutocin dake sarrafa makamai da madatsun wutar lantarki, da sauran abubuwan da rayuwar duniya gaba ɗaya suke dogaro akansu, suka fi ɗan adam basira kuma suka fara sarrafa kansu ta hanyar da za ta jefa rayuwar duniya cikin haɗari?

Waɗannan masana sun buga takardar kokensu ne a shafin cibiyar gudanar da binciken al’amuran da suka shafi rayuwar duniya mai suna: “Future of Life Institute”.  Wannan cibiya ta Future of Life dai manufarta shi ne taimakawa wajen rage haɗarin dake tattare da ci gaban da ake samu a duniya daga manyan fannonin kimiyya guda uku:  kimiyyar Nukiliya da yaɗuwarsa a duniya da tasirisinsa, da Fasahar AI, da kuma Fasahar sauya tsarin ɗabi’ar sinadaran jikin ɗan adam, wato: Biotechnology kenan, kamar yadda muka gabatar a maƙalarmu mai take: “Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Ɗan Adam a Duniya”.

Shahararru daga cikin waɗanda suka sa hannu kan wannan takarda dai sun haɗa da: Steve Wozniak, wanda suka yi haɗin gwiwa da Steve Jobs wajen samar da kamfanin Apple a shekarar 1977.  Da Elon Musk, shahararren mai kuɗin duniya, ɗan asalin ƙasar Afirka ta Kudu kuma Ba’amurke a yanzu, mai kamfanin ƙera motoci nau’in Tesla.  Sai kuma Andrew Young, tsohon ɗan majalisar Amurka, Marc Rotenberg, ɗaya daga cikin shararrun masana kan fasahar AI kuma shugaban cibiyar bincike na AI mai suna: “Center for AI and Digital Policy”.  A cikin buƙatarsu suka ce dole ne duniya ta dakatar da ci gaban bincike a wannan fanni na tsawon watanni shida. Wannan tazara na lokaci ne suka ce zai ba da damar tattaunawa don samar da hanyoyin kariya daga haɗarorin da wannan fasaha ke ɗauke dashi.

- Adv -

Wannan ƙorafi da waɗannan masana suka gabatar ya ja hankalin duniya sosai matuƙa.  ‘Yan jarida da masana a harkar fasahar sadarwar zamani sun yi ta sharhi kan dacewa da rashin dacewar ƙorafin.  Ko yiwuwa da rashin yiwuwar abin da suke kira gareshi.  Musamman ganin cewa wannan cibiya da suka gabatar da kokensu ta hancyarta ba ta da wani ƙarfi na zartarwa wajen sauya tsaren-tsaren duniya a aikace.  Wannan kira ya haifar da cece-kuce matuƙa a duniya, kuma yana cikin abubuwan da suka sauya tunanin ƙasashe kan wannan fasaha a shekarar 2023.  Bayan ci gaban da ake hasashen wannan fasaha zai samar, ƙasashe na ta yunƙurin samar da dokoki da ƙa’idojin ma’amala da fasahar, don kuɓutar da al’ummarsu daga haɗarorin dake tattare da ita.

Na 5: Fasahar ChatGPT da Bard Na Iya Ta’ammali da Intanet Kai Tsaye

A farkon lokacin da aka samar da waɗannan fasahohi a shekarar 2023, bayanai sun nuna cewa an horar dasu ne daga tarin dandazon bayanan da kamfanonin da suka sama dasu suka fara.  Wannan shi ake kira: “Training Data”.  Ire-iren waɗannan bayanai sun haɗa da bayanan dake shafukan Intanet, da waɗanda ke killatattun wurare irin su Dandalin Quora, da shafukan matattaran magina manhajar kwamfuta irin su Stackoverflow, da GitHub, dai sauran wurare makamantansu.  An tara bayanan ne a ma’adanar kwamfutoci da aka tanada, aka gina manhajar dake iya ta’ammali dasu, aka ɗora mata ƙa’idojin da za ta riƙa tantancewa, da ganewa, don ba ta damar ƙirƙira da yin nazari kan bayanai makamantansu.

An ƙaddamar da fasahar ChatGPT da Google Bard ne a kan wannan tsari.  A duk sadda kaje shafinsu, ka gabatar da tambaya rubutacciya, manhajar kan tuntuɓi wancan dandazon bayanai ne da aka karantar dashi a kansu, don tsara jawabin da zai baka.  Shi yasa ma, har yanzu idan kana amfani da Fasahar ChatGPT 3.5, ka mata tambaya kan abin da ya shafi shekarar 2022, ko 2023, za ta sanar dakai cewa iya watan Satumba na shekarar 2021 ne kaɗai ilminta ya taƙaita.

To amma daga zubin ChaptGPT 4, da Google Bard an samu sauyi farawa daga watan Mayu lokacin da kamfanin OpenAI ya sanar da cewa an samu sauyi.  Kamfanin ya samar da wasu ƙananan manhajoji dake taimaka wa fasahar ChatGPT jonuwa da shafukan Intanet don nemo ƙarin bayanai dake da alaƙa da lokaci da tarihi.  A ɗaya ɓangaren kuma, kamfanin Microsfot ya ƙara inganta Fasahar neman bayanai na Bing don taimaka wa fasahar ChatGPT zaƙulo bayanai daga Intanet kai tsaye, a duk sadda aka mata tambaya mai alaƙa da tarihi ko lokacin da yake na kusa.  Hakan ya taimaka wa mutane hanyoyin neman tikitin jirgi, da bayanan yanayi, da ɗakunan otal ga matafiya cikin sauƙi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.