Sakonnin Masu Karatu (2021) (9)

Fa'idar Farke Wayar Salula (Rooting)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 25 ga watan Yuni, 2021.

609

Kamar yadda muka saba lokaci zuwa lokaci, a yau na dan tsakuro wasu ne daga cikin tambayoyinku, don samun gamsuwa.  Idan mun tabo dan abin da ya samu, sai mu ci gaba da makalarmu kan Fasahar “Digital Currency”.  Karin fadakarwa ga masu aiko sakon tambayoyi ta Imel ko ta sakon Tes, don Allah a rika rubuta cikakken suna da cikakken adireshi.  Sannan a daina amfani da gajerun kalmomi cikin rubutu.  Yin hakan kan sa in kasa gane manufar mai tambaya ko abin da yake son tambaya a kai.  In kuwa haka ya faru, zai yi wahala in ba da amsar da ta dace da tambayar.  Sai a kiyaye.

——————–

Assalamu Alaikum, Baban Sadik barka dai.  Da fatan kana lafiya.  Don Allah mene ne amfanin yi wa wayar salula nau’in Android “Rooting”?  Na gode.  – Omar Mudi Abubakar: omaribnmahmud@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Omar, da fatan kana lafiya.  A baya mun yi bayani mai tsayi kan wannan maudu’i mai mahimmanci a fannin tsarin sadarwar wayar salula.  Kuma kasancewar bamu yi bayani na musamman kan fa’ida da rashin fa’idar wannan tsari na mu’amala da wayar salula ba a wancan rubutu, duk kuwa da tsayinsa, shi yasa naga dacewar amsa wannan tambaya taka.  Don haka, bayan fa’idar yin “Rooting” ga wayar salula nau’in Android, zan yi bayani har wa yau kan wasu daga cikin rashin fa’idar yin hakan.  Kamar yadda muka sani ne a al’adar rayuwa, duk wani abu da yake tsarin mu’amala ne, ba a rasa wani bangaren illa tattare dashi, duk girman fa’idarsa kuwa.

Da farko dai, Kalmar “Rooting” a fannin wayar salula na nufin “Samun damar iya aiwatar da wasu kare-karen ayyuka ne marasa adadi a kan wayar salula, ta hanyar farke kariyar da kamfanin wayar ya sanya mata lokacin kerata.”  Kowace wayar salula na zuwa ne dauke da iko (right) wanda aka baiwa mai wayar wajen sarrafa ta.  Sai dai wannan iko ne tawwayayye.  Domin akwai wasu abubuwa da mai waya bazai iya aiwatar dasu ba.  Misali, ba kowace irin manhaja ce za ka iya cire ta daga kan wayar ba, ko jirkita mata yanayi, ko canza matsa tsari ba.  Sannan ba kowace irin manhaja ce za ka iya dora mata ba.  To amma da zarar ka farke wayar ta hanyar “Rooting”, komai kana iya yi a kanta.  Ga kadan daga cikin fa’idojin farke wayar salula nan.

- Adv -

Fa’idojin Farke Wayar Salula (Rooting)

Daga cikin fa’idar farke wayar salula shi ne, hakan zai baka damar kara mata sauri wajen sarrafa bayanai da umarnin da kake bata; ya zama ta daina saibi wajen bude manhaja ko shafin da ka bukata idan Intanet ne.  Wannan tsari shi ake kira “Overclocking”.  Kamar tsari ne kara wa wayar salula tagomashi ta hanyar masarrafarta (Processor).  Fa’ida ta biyu ita ce, hakan zai taimaka wajen inganta rayuwar batirin wayar.  Tunda wayar na amsa umarni cikin gaggawa, hakan zai sa cikin dan kankanin lokaci ta aiwatar da ayyuka masu yawa, ba tare da cin makamashi mai yawa ba.  Fa’ida ta uku, farke wayar salula na baka damar cire dukkan tallace-tallacen dake dauke cikin manhajojin da kake saukewa daga cibiyar Play Store.  Babu wata manhaja da ake saukewa wacce ba ta dauke da tallace-tallace a kanta. Kuma hakan na haddasa cikas ga mai ma’amala da manhajar.  Manhajojin da ka saya da kudinka ne kawai ake boye maka tallace-tallace daga cikinsu, ba wai babu su bane.  Akwai su.  Amma dukkan manhajar kyauta, akwai talla a kai, kuma da zarar ka fara amfani da ita za su ta bayyana.  Farke wayar salula na baka damar cire su ko hana su bayyana.  Fa’ida ta hudu, farke wayar salula na baka ikon cire duk wata manhaja da wayar tazo dashi, wanda kamfanin ya dasa a kanta, ya kuma like hanyar ake iya cire ta.  Ire-iren wadannan manhajoji dai sun haka da manhajar aika sakon tes, wanda wayar tazo da ita.  Da manhajar taskance lambobin mutane, wacce wayar tazo da ita.  Da manhajar daukan hoto, da taskance bidiyo, wadanda wayar tazo dasu.  Da zarar ka farke wayar salula nau’in Android, duk kana iya cire su cikin sauki.  Cikin fa’idar farke wayar salula akwai samun damar dora wasu manhajojin a asali kamfanin wayarka ya hana ka.  Idan kaga dama ma, kana iya cire babbar manhajar da wayar tazo da ita, ka dora mata sabuwa ko wata daban.  Babbar fa’ida ta karshe ita ce, kana iya isa ga dukkan bayanan da wayar take dauke dasu, kuma cikin ilimi ba jahilci ba, ka sarrafa abin da kake son sarrafawa babu wani kaidi.  Wadannan, a takaice, su ne fa’idojin dake tattare da farke wayar salula nau’in Android, wato: “Rooting”.

Illolin Farke Wayar Salula

Babbar illar da ka iya samuwa wajen yunkurin farke wayar salula ita ce, haukatar da wayar baki daya, da kashe ta kankat!  Wannan zai faru ne idan aka samu kuskure wajen juye mata sababbin bayanai ko manhajar da ake son a dora mata, wanda makerinta bai dora mata ba.  Illa ta biyu, farke wayar salula na kwance mata garantin (Warranty) da kamfanin ya bata yayin da ka sayo ta.  Musamman idan lokacin garantin bai kare ba.  Idan ka farke wayar salula kuma aka samu matsala abin bai yi ba, ko ka mayar da ita shago ko kamfanin da ka sayo, baza su karba ba.  Illa ta gaba ita ce, farke wayar salula na hana maka samun sababbin bayanan da kamfanin wayar ke fitarwa lokaci zuwa lokaci, don kara wa wayar tagomashi da ingancin rayuwa.  Da zarar ka farke wayar, duk sadda tayi yunkurin nemo wadannan bayanai, za a gane cewa tuni an canza mata halitta, don haka, ba za a bata damar saukar dasu ba balle ta amfana dasu.  Sai a kiyaye.

Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.