Hanyoyi 9 Da Fasahar AI Ta Sauya Duniya a Shekarar 2023 (5)

Fasahar ChatGPT 4.0

Bayan dukkan waɗannan ƙudurori na basira da wannan zubi na ChatGPT 4 ta ƙunsa, tana iya ƙirƙiro maka abubuwa da dama, ba wai yin nazari kan abin da ka loda mata kaɗai ba.  Misali, tana iya rubuta maka waƙa, sannan ta waƙe maka shi cikin sauti. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 2 ga watan Fabrairu, 2024.

51

Na 2: Bayyanar “ChatGPT 4.0”

Abu na biyu da ya sauya duniyar sadarwa a shekarar 2023 shi ne fitar da sabon zubin fasahar ChatGPT 4 da kamfanin OpenAI yayi.  Hakan ya faru ne a watannin farko na shekarar, bayan kamfanin Google da Microsoft sun mayar da martani.  Wannan yunƙuri ya ƙara razana da yawa cikin masu lura hanyoyin kariya daga ci gaban da fasahar AI ke samu, ta la’akari da irin matsalolin da ci gaban zai jawo nan gaba.  Fasahar ChatGPT 3.5 a farkon bayyana tana iya ta’ammali da rubutattun bayanai ne kaɗai.  Ma’ana, ka bata umarni ta hanyar rubutu, sai ta aiko maka jawabi. Idan shawara ce, ta baka shawara;  duk wannan a rubuce ne.

Amma da fasahar ChatGPT 4 ta bayyana, sai wannan tsari ya sauya.  Ba rubutattun bayanai kaɗai ba, hatta hotuna da sauti da bidiyo duk kana iya loda mata, nan take za ta karance su, sannan baka jawabi kan tambayar da kayi mata. Haka ma, kana iya loda mata kundin rubutattun bayanai, wato: “Text file”.  Za ta karance shi tsaf, sannan ta maka bayanin abin da rubutun ya ƙunsa.  Haka ma idan littafi ne ka loda mata. Misali, akwai bincike da na gabatar lokacin da nake yin Digiri na biyu akan harkar hada-hadar kuɗi a tsarin Musulunci – Islamic Banking and Finance – yayin da nake wannan rubutu na gudanar da wasu gwaje-gwaje ta amfani da wannan sabuwar fasaha ta ChatGPT 4.  Na loda mata kundin binciken da na gabatar mai shafuka 126, sannan nace ta min bayani a taƙaice, meye binciken ya ƙunsa gaba ɗaya?  Cikin ƙasa da minti guda ta aiko min jawabi filla-filla, kar har ma da ƙarin shawarwari.

Bayan dukkan waɗannan ƙudurori na basira da wannan zubi na ChatGPT 4 ta ƙunsa, tana iya ƙirƙiro maka abubuwa da dama, ba wai yin nazari kan abin da ka loda mata kaɗai ba.  Misali, tana iya rubuta maka waƙa, sannan ta waƙe maka shi cikin sauti.  Kana ma iya zaɓan irin nau’in kayan kiɗin da za ta yi amfani dashi idan ta tashi waƙe maka waƙar.  Kuma abu ne ƙirƙirarre, ba wai daga wani shafi na musamman ta kwafo maka shi ba.  

Mai karatu zai yi mamakin jin cewa abin da wannan zubi na ChatGPT 4 tafi ƙwarewa a kai, shi ne iya samar da rubutattun manhajar kwamfuta, cikin yaren gina manhaja, wato “Programming Language”.  Kusan ta ƙware a fagen kowane yaren gina manhaja, musamman irin su C, da C++, da Java, da Python, da C# da dai sauransu.  Za ta iya rubuta maka matakan da za bi wajen ƙirƙirar manhajar kwamfuta ko na wayar salula, sannan ta rubuta maka umarnin da zai samar maka da manhajar, tare da jakan bayanan da za ka ƙirƙira (Code file structure) don adana kowanne, da kuma shawarwarin da za su taimaka maka wajen yin komai da ya shafi manhajar.

- Adv -

Bayan wannan, tana iya rubuta maka cikakken littafi kan kowane irin maudu’i ne.  Tana iya ƙirƙiro maka shirin fim, ko wasan kwaikwayo, sannan juya maka shi a aikace, cikin bidiyo.  Tana iya ƙirƙiro maka labari shi ma cikin kowane fannin rayuwa, ta rubuce maka shi tsaf, ka mayar dashi a matsayin littafi. Ko dai ka ɗabba’a shi a zahiri ka sayar. Ko ɗora shi a matsayin littafi a shafin yanar sadarwa (eBook).

A wani yanayi mai ban mamaki kuma, wannan fasaha tana iya taimaka maka wajen rubuta kundin kammala karatu, ko kundin bincike a ilmance, wato: “Academic research paper”, tun daga farko har ƙarshe.  A taƙaice ma dai, wannan fasaha na iya taimaka maka wajen zaɓan taken maƙalar, da abin da dukkan babukan rubutun za su ƙunsa, da bayanan da kowane ɓangare na rubutun zai ƙunsa; komai ita za ta samar maka.  Sannan tana iya ƙirƙiro maka hotunan da zaka ɗora masu alaƙa da rubutu ko maudu’in da kake rubutu akai.  Idan rubutu kake ɗorawa a shafin yanar sadarwa a kowane mako ko wata ko yini, wannan fasaha na iya rubuta maka maƙala cikakkiya kan kowane maudu’i, ta samar maka da hoto mai alaƙa da maƙalar don ɗorawa a shafin.

Dukkan waɗannan abubuwa tana gudanar dasu ne sanadiyyar wasu ɗabi’u masu alaƙa da basira da aka koya mata lokacin da ake gina ta.  An koya mata saurin tuna abubuwan da ta taɓa cin karo dasu a baya, da saurin tunani wajen ƙirƙirar abubuwa, da saurin karancewa da fahimtar duk hoto ko bidiyon da ta gani nan take, da kuma saurin haddacewa da tunawa da kuma iya fahimtar abin dake ɗauke cikin wani sauti da ta taɓa saurare.  Sannan sai iya karɓan ƙarin bayanai daga wanda ke hira da ita, da iya masa tambayoyi don neman ƙarin bayani.

Kamar yadda bayani ya gabata a baya, wannan sabon zubi na fasahar ChatGPT, wato “ChatGPT 4.0”, ya sha bamban da tsohon zubin “ChatGPT 3.5” da aka fara fitarwa wajen abubuwa da dama.  Wannan yasa kamfanin ya killace sabon zubin ga masu hali.  Ita kuma na farkon aka barta ga gama-garin mutane.  Don haka, idan kana son amfani da zubin ChatGPT 3.5, ita ce za ka fara cin karo da ita da zarar ka yi rajista.  Idan kuma kana son ƙarin basira da ƙarin hanyoyin loda bayanai don gudanar da abubuwa masu yawa, da samun saurin karɓai jawabi, tare da iya amfani da manhajar a kowane lokaci ne, to, sai ka biya dala 20 a kowane wata don samun sabon zubin ChatGPT 4.0.   Masu buƙatar wannan manhaja ta ChatGPT, kana iya saukar da ita daga cibiyar manhajojin wayar Android mai suna Play Store, ka rubuta: “ChatGPT” kawai, za a ɗauko maka ita, sai ka saukar ka loda wa wayarka.  Bayanai kan hanyoyin kariya daga kurakuran da za ka iya cin karo dasu yayin ta’ammali da wannan fasaha kuma, suna nan tafe in Allah Ya so.

A ƙarshe, bayyanar wannan zubi na ChatGPT 4 shi ne abu na biyu cikin abubuwa tara da suka ƙara sauya mahangar rayuwa a duniya a fagen sadarwa da samar da bayanai, da dokokin haƙƙin mallaka a duniya cikin shekarar 2023.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.