Sakonnin Masu Karatu (2012) (3)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

130

Ga kashi na biyu na sakonninku.  A yau za mu fara ne da masu jaje kan abin da ya faru gare ni watanni biyu da suka gabata. Ina mika godiya ga dukkan wadanda suka mini jaje, ta waya ne, ko ta tes, ko ta Imel.  Allah saka da alheri, ya bar zumunci, amin. Na gode. Na gode. Na gode!


Jaje…

Salamun alaikum Baban Sadik, ina yi maka addu’a da Allah ya kiyaye gaba, ya sa kaffara ne, abin da aka rasa kuma Allah ya mayar da mafi alheri.  Su kuma Allah ya shirye su idan masu shiryuwa ne, idan ba masu shiryiwa bane Allah ya tona asirinsu, amin. Daga Sadik Nasidi Sa’al, Kano: 08060302454


Assalaamu alaikum Baban Sadik, Allah ya mayar da mafi alheri na abin da aka rasa, ya kuma kare gaba.  Daga: 08032079425


Assalaamu alaikum Baban Sadik, na samu labari barayi sun shiga gidanka su maka satar kwamfuta, to, ina maka jaje.  Allah kiyaye gaba, ya kuma mayar da mafi alheri.  Su kuma Allah ya tona musu asiri.  Daga: Ali Garba Okene: 08066369653


Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina taya ka jaje kan abin da ya faru da kai.  Allah Ubangiji ya mayar da abin da aka rasa, su kuma Allah ya tona asirinsu.  A huta lafiya.  Daga: Usman Abubakar Lafiya: 08135433503


- Adv -

Baban Sadik, na karanta tsautsayin da ya same ka na barayi, Allah ya mayar da alheri, ya kara maka arziki, ya kuma kiyaye gaba, amin. Su kuma Allah ya tona musu asiri. In kuma masu shiriya ne, to Allah shirye su. Daga: Musa Muhammad ‘Yan Kaba, Bakin Dogo, Kano: 08104001040


Salaamun alaikum bimaa sabartum…Baban Sadik, alhini da takaici ga abin da ya faru na shigar barayi gidanka da ta’asarsu gare ka, Allah ya mayar da mafi alheri, ya kiyaye gaba, amin.  Daga wanda ke amfanuwa da kai a ko da yaushe: Mu’azzam Suleiman Kano: 08179705299


Salaamun alaikum Baban Sadik, muna jajanta maka abin da ya faru da kai.  Allah ya mayar maka da alheri, ya kiyaye na gaba, amin.  Daga: Sunusi Sani Dala: 08036800241


Salaamun alaikum Baban Sadik, alherin Allah ya kai maka da iyalanka.  Na ga labarin cewa barayi sun shiga gidanka sun yi sata.  Na yi alhinin haka, kuma ina addu’a Allah ta’ala ya ninka maka abin da suka sace, ya kuma tsare mana kai da irin tsarinsa, Allah ya hana sake afkuwar haka, amin. Daga: Maman AbdusSamad, Gombe


Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya, Allah ya saka maka a bisa kokari da kake yi na fahimtar da mu, amin.  Ina maka jajen satan da aka maka, Allah ya mayar maka da dubunsa, ya kare ka daga sharrin masharranta, amin.  Daga: Aisha Ibrahim Zaria


Salaamun alaikum Baban Sadik, na rubuto ne domin dubiya a kan masarrarar da ka sha fama da ita.  Allah ya kara karfin jiki.  Kuma dangane da barayi da suka shiga gidanka, Allah ya kiyaye gaba, ya mayar maka da ninkin abin da ka rasa da alheri. Daga: Dalibinka, Abdullahi Tukur Bacha, Kibiya, Kano: 07054848488

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.