Bitar Maƙalolin Da Suka Gabata a Shekarar 2022 (2)

Idan Allah Ya kaimu marhala ta gaba, wacce za mu shiga nan da makonni biyu dake tafe, za mu buɗe ne da yin sharhi kan irin ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere, cikin shekarar da ta gabata. – Jaridar AMINIYA, ranar Jumma’a, 13 ga watan Janairu, 2023.

312

Nazari Kan Fasahar “Web 3.0”

A cikin watan Maris ne muka fara sabon nazari kan sabuwar fasahar giza-gizan sadarwa na duniya nau’i na uku, wato: “Web 3.0”, wanda ita ce sabuwar fasahar dake ɗauke da sabon launin ci gaban dake tafe a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani.  Wannan maƙala mai take: “Web 3.0: Sabon Nau’in Giza-Gizan Sadarwa na Duniya Zubi na Uku”, an buga ta ne tsakanin watan Maris zuwa ƙarshen watan Yuni; daga kashi na ɗaya zuwa kashi na goma sha uku.  Kasancewar fannin na ɗauke ne da manyan ɓangarori guda 4, mun yi sharhi kan 3 ne daga cikinsu kawai; fasahar AI, da fasahar Blockchain, da kuma fasahar “EDGE Computing”.  Ɓangaren ƙarshe da ya rage shi ne fasahar sadarwa ta 5G, wanda a baya mun yi dogon nazari da bincike a kanta sama da watanni.  A ƙarshen watan Yuni ne muka kawo labarin saye kamfanin Twitter da hamshaƙin mai kuɗin duniya na wancan lokaci, Mista Elon Musk yayi kan zunzurutun kuɗi dala biliyan 44.

Nazari Kan Daftarin Dokar NITDA

Cikin watan Yuli ne hukumar Bunƙasa Fannin Fasahar Sadarwa ta Ƙasa, wato: Nigerian Information Technology Development Agency (NITDA), ta fitar da wani daftari na sabuwar dokar hanyoyin ma’amala da kafofi da na’urorin sadarwa na zamani, musamman kafofin sada zumunta.  Wannan ya bamu damar zama don yin nazarin wannan doka na musamman, inda muka kwashe makonni 7 muna nazari a kai.  Makonni uku na farko kan asalin daftarin dokar ne.  Taken maƙalar shi ne: “Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya”.  Bayan nan sai muka yi nazari kan dalilan dake sa hukumomi ƙayyade waɗannan kafafe na sadarwa, da kuma hanyoyin da su kansu kafofin ke bi wajen ƙayyade masu ta’ammali da kafafensu.  Taken maƙalar farko shi ne: “Me Yasa Hukumomin Ƙasashen Duniya ke Ƙayyade Tsarin Ma’amala da Kafafen Sadarwa na Zamani?”.  Na biyun kuma: “Hanyoyin da Kafafen Sadarwa Na Zamani Ke Bi Wajen Ƙayyade Masu Amfani da Shafukansu”.  Bayan waɗannan maƙaloli biyu waɗanda sharhi ne don fahimtar da masu karatu dalilan da suka sa Hukumar NITDA fitar da wannan daftari, sai muka ɗauki makonni biyu kuma wajen faɗakar da hukuma kan abubuwan lura dake cikin wannan daftari na doka, cikin maƙala na musamman mai take: “Abubuwan Lura Cikin Sabuwar Dokar NITDA”.  Wannan ya kawo mu tsakiyar watan Agusta.

Sharhi Kan Ƙarin Harajin Kuɗin Kiran Waya

Cikin watan Agusta ne Ministan Kuɗi ta Ƙasa Hajiya Zainab Zaituna ta sanar da ƙarin kuɗin haraji ga kamfanonin sadarwa na ƙasa.  A daidai lokacin ne sashin Hausa na BBC dake nan Abuja yayi hira dani kan tasirin wannan ƙari, musamman ta la’akari da halin hauhawan farashin kayayya da jama’a ke fama dashi.  Wannan yasa naga dacewar naƙalto wa masu karatun wannan shafi mai albarka abin da muka tattauna dasu akai, don sanin halin da ake ciki.  Taken maƙalar da na kawo kan haka shi ne: “Nazari kan Ƙarin Harajin Kuɗin Kiran Waya Da Na Data”.  Cikin wannan lokaci ne kuma har wa yau wata dambarwa ta kunno kai a kamfanin Twitter, lokacin da Mista Elon Musk ya karɓi ragamar shugabancin kamfanin, bayan saya da yayi.  Na hakaita ma sababbin sauye-sauyen da yayi (ko yake kan yi har yanzu) a kamfanin Twitter, da yadda yayi ta sallamar ma’aikatan kamfanin, wasu kuma na ta barin aiki da kansu, saboda abin da suka kira rashin dacewar sauye-sauyen da yake.  Daga nan muka je hutun rabin lokaci, don amsa tambayoyi da saƙonnin masu karatu.

- Adv -

Sharhi Kan Ci Gaban Kimiyya a Zamanin Yau

Bayan tsawon kusan watanni uku (daga watan Satumba zuwa Nuwamba) muna amsa tambayoyin masu karatu, a ƙarshen marhalar mun karanta sharhi na musamman da na mana mai take: “Ci Gaba a Fannin Kimiyyar Kere-Kere a Zamanin Yau”.  Manufar wannan sharhi shi ne don faɗakar da mai karatu halin da duniya take ciki a yau, inda kusan fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani ya game dukkan ɓangarorin rayuwa.  A taƙaice dai, sharhin yayi nazari ne kan tasirin fannin kimiyyar sadarwa wajen ƙere-ƙere, daga motoci, zuwa babura, da kayayyakin amfanin gida, da dukkan wani abin da ɗan adam ke amfani dashi na rayuwa a yau, akwai yunƙurin amfani da kimiyyar sadarwa wajen sawwaƙe ta’ammali dashi.

Fasahar Saƙon Tes ta Cika Shekaru 30!

Ɓangaren darussanmu na ƙarshe dai ya zo mana ne a watan Disamba, daidai lokacin da wata tsohuwar fasahar sadarwa ke cika shekaru 30 da ƙirƙira.  Wannan fasaha kuwa ita ce fasahar gajeren saƙon waya, ko kace “Fasahar Tes” ko “Fasahar Short Message Service”, ko “SMS” a gajarce.  Mun kwashe makonni uku wajen yin sharhi kan ci gaban wannan fasaha, da sauye-sauyen da aka samu waɗanda suka taimaka mata wajen yin tasiri duk da samuwar wasu hanyoyin sadarwar.  Taken sharhin dai shi ne: “Fasahar “SMS”: Shekaru 30 Bayan Ƙirƙira”.

Kammalawa

Idan Allah Ya kaimu marhala ta gaba, wacce za mu shiga nan da makonni biyu dake tafe, za mu buɗe ne da yin sharhi kan irin ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere, cikin shekarar da ta gabata.  Daga nan kuma sai mu bibiyi wasu daga cikin maƙalolin da bamu ƙare su ba a marhalar baya, don kammala fa’idar dake cikinsu.

A ƙarshe, muna godiya ga Allah maɗaukakin sarki da ya hore mana lokaci da juriya don gudanar da wannan aiki.  Sai kuma kamfanin Media Trust mai buga jaridar AMINIYA da sauran yayyinta, don baiwa jama’a damar ƙaruwa da wayewa a fannonin rayuwa da addini.  Ina godiya har wa yau ga Editan AMINIYA, da mataimakansa, musamman mai lura da wannan shafi naku mai albarka, wajen tsara shafin.  Allah saka musu da alheri.  Sannan ina miƙa godiyata ga masu karatu, musamman masu aiko shawarwari da gyara, har da masu ƙorafi ma. Duk da bazarku nake rawa.  Allah saka wa kowa da alheri, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.