Waiwaye Adon Tafiya (9): Bitar Darussan Baya (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 21 ga watan Janairu, 2022.

458

Shahararrun Makaloli (2)

Daga cikin sababbin nau’ukan fasahohi da ke kan game duniyar fasahar sadarwa a yau, da ma kere-kere, akwai fasahar AI, wato: “Artificial Intelligence”.  Wannan fasaha na dauke ne da tsarin shigar da dabi’un dana dam – irin su fasaha, da hazaka, da fahimta, da kwarewa, da gwanancewa, da kuma tunani – cikin na’urorin sadarwa na zamani.  Mun kawo jerin makaloli guda 4 masu take: “Fasahar AI a Fannin Kere-Kere”.  Wannan fanni na bukatar karin bayani da fahimta ga masu karatu, don samun wayewa.  Domin a halin yanzu muna mu’amala da na’urori masu dauke da wannan fasaha – irin su wayar salula, da kwamfuta, da talabijin.  Sanin yadda abin yake zai taimaka wa mai karatu wajen karuwar ilimi da wayewa a wannan zamani; musamman wajen sanin girman kudura da karfin mulkin Allah.

Gama makalar fasahar AI ke da wuya, sai muka sake tsunduma cikin wani fanni mai sarkakiya a wannan zamani namu.  Wannan fanni kuwa shi ne irin ci gaban da ake samu wajen hada-hadar kudade a kafofi da na’urorin sadarwa na zamani.  Kuma shi ake kira: “Financial Technology” ko “FinTech” a gajarce.  Na gabatar da makaloli masu take: “Bayani Kan Digital Currency, da Virtual Currency, da kuma Cryptocurrency”, daga kashi na 1 zuwa kashi na 11.  Mun dakata ne kan bayanin “Manyan Matsalolin Cryptocurrency.”  Kuma in Allah Yaso a marhalar karatunmu na gaba, za mu ci gaba.  Ana iya riskar makalolin baya a: https://babansadik.com/category/fasahar-digital-currency.

Hakan ya zo ne daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta hana amfani da fasahar Twitter, sanadiyyar dakile shafin Shugaban Kasan Najeriya da kamfanin yayi.  Wannan yasa muka dubi tasirin hakan a fasahance, cikin gajeren sharhi mai take: “Tasirin Dakatar da Twitter a Najeriya.”  Sai kuma muka koma bangaren yadda kafafen sada zumunta ke samun kudaden shigansu.  Na dade ina samun tambayoyi kan hakan.  Masu karatu na mamakin yadda wadannan shafuka ke baiwa mutane damar aiwatar da sadarwa kyauta, ba tare da sun biya kudi ba, a tare da cewa kullum kuma kara inganta tsarin suke yi.  Wannan yasa na gabatar da sharhi na musamman har tsawon makonni 4, mai take: “Hanyoyin Da Kafafen Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga.”  Daga nan kuma muka bibiyi wannan sharhi da fadakarwa kan munanan tasirin labaran bogi a kafafen sadarwa.  Taken makalar shi ne: “Yaduwa da Munanan Tasirin Labaran Bogi a Kafafen Sadarwar Zamani”.

Daga cikin manyan tsaren-tsaren gwamnatin tarayya a fagen inganta hada-hadar kudade, akwai samar da nau’in kudin zamani da za a rika amfani dashi a kafafen sadarwa na zamani.  Wannan nau’in kudi shi ake kira: “Digital Currency”, kamar yadda a baya nayi bayani cikin makalar “Cryptocurrency”.  Tsarin gwamnatin tarayya, wanda babban bankin Najeriya (CBN) ya kaddamar, shi ne: eNaira.  Akan haka nayi rubutu na tsawon makonni 4 don wayar mana da kai.  Taken wadanna makaloli dai shi ne: “eNaira: Ma’ana, da Fa’idojin Dake Cikinsa.”  Wannan na daga cikin makalolin da suka shahara sosai, musamman ga wadanda suke bibiyar rubuce-rubucen da nake yi a kafar Facebook.  Daga lokacin da wannan tsari ya habaka sosai, akwai fa’idoji masu dimbin yawa da za a ribata daga gare shi.

- Adv -

Bayan makalar eNaira, na yi sharhi takaitattu kan wasu sababbin al’amuran ci gaba da aka samu a fannin kimiyyar sararin samaniya.  Musamman yunkurin da ake yi na ganin an samar da makwafin fasahar Intanet irin wanda muke dashi a wannan duniyar, a duniyar wata, don baiwa masu ziyara damar aiwatar da sadarwa a tsakaninsu, ba tare da sun dogara ga masu lura da shawaginsu daga nan duniya ba.  Sai kuma sharhi na musamman kan wasu nau’ukan wayoyin salula guda 52 da kamfanin Facebook (ko Meta) ya sanar da cewa zuwa karshen shekarar da ta gabata, manhajar WhatsApp za ta daina amfani ko aiki a kansu.

A karshe, wannan marhala ta karkare ne da fassarar rubutun Al-Khalili, wanda dan uwa Mudassir ya dauki tsawon makonni 7 yana fassara mana, kan irin ci gaban da aka taba samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere a duniyar musulmai a baya, da kuma irin shawarwarin da ya kawo a karshe, kan yadda za a iya dawo da wannan martaba a kasashenmu na yau.

Kammalawa

Idan Allah Ya kaimu marhala ta gaba, wacce za mu shiga nan da makonni biyu dake tafe, za mu bude ne da yin sharhi kan irin ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar kere-kere, cikin shekarar da ta gabata.  Daga nan kuma sai mu bibiyi wasu daga cikin makalolin da bamu kare su ba a marhalar baya, don kamala fa’idar dake cikinsu.

A karshe, muna godiya ga Allah madaukakin sarki da ya hore mana lokaci da juriya don gudanar da wannan aiki.  Sai kuma kamfanin Media Trust, mai buga jaridar AMINIYA da sauran yayyinta, don baiwa jama’a damar karuwa da wayewa a fannonin rayuwa da addini.  Ina godiya har wa yau ga Editan AMINIYA, da mataimakansa, musamman mai lura da wannan shafi naku mai albarka, wajen tsara shafin.  Allah saka musu da alheri.  Sannan ina mika godiya ga masu karatu, musamman masu aiko shawarwari da gyara, har da masu korafi ma. Duk da bazarku nake rawa.  Allah saka wa kowa da alheri.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.