Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (9)

Kashi na 9 cikin jerin kasidun da muke kwararowa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. A sha karatu lafiya.

146

Alamomin Dake Nuna an Sace Zatinka (2)

Samun Kiran Tantancewa Kafin Biyan Kudi

A tsarin aikin banki, akwai iya adadin kudin da mai taska zai iya kayyadewa cewa idan ya bukaci a biya wani kudin da adadinsa ya wuce hakan, to, sai an nemi tabbaci daga gare shi kafin a biya.  Wannan tsari shi ake kira: “Cheque Confirmation.”  Wannan ga masu taskar dake mu’amala da takardar cak ne, wato: “Current Account.”  To duk sadda kaji an kira ka daga banki cewa: “Ana neman izninka ne kan takardar cak da ka ba wane na dubu kaza ko miliyan kaza, shin, da masaniyarka?”, alhali baka ba kowa takardar cak ya karbi wani adadi na kudi ba, alamar an sace maka zatinka kenan, musamman ta hanyar sace maka takardar cak. Ko dai gaba dayansa ko wani bangare nashi.

A nan ya zama wajibi ka sanar dasu cewa ba da yawunka bane, kuma nan take ka binciki inda ka ajiye takardan cak dinka.  Ka kuma tabbatar cifcif suke, babu daya da yayi ciwon kai.  Idan akwai shafukan da aka yage, to, matsalar daga gareka ta samo asali.  Idan kuma babu, komai daidai yake, dole ne ka zarce bankin kai tsaye, ka nuna musu.  Wannan zai basu damar aiwatar da bincike don tantance abin da ya faru.  Wannan ita ce alama ta hudu.

Sakon Sanarwar Karancin Kudi a Taskarka

- Adv -

Wannan ita ce alama ta biyar.  A duk sadda ka ga sako daga banki cewa: “Saboda karancin kudin dake taskarka, ba za ka iya cire dubu kaza ko miliyan kaza ba”, kuma kai baka ma je banki ko ATM ba, baka kuma aiki wani ya ciro maka kudi a ATM ba, to, alamar wani ya sace zatinka kenan.   Ko dai an sace maka katin ATM dinka ne kai tsaye, ko kuma an samu bayanan katin naka, aka yi amfani dasu wajen kera wani kati don ciran kudi daga taskarka.  Nan take sai ka garzaya bankinka don sanar dasu halin da ake ciki.  Idan har katinka na ATM na tare dakai, to, watakila bayananka aka samu ta wata hanya da bayanai suka gabata a kai.  In kuma ka duba baka ga katin ba, sama ko kasa ka rasa, to, watakila an sace katin ne kai tsaye.

Ziyarar Jami’an Tsaro a Gida ko Wajen Aikinka

Alama ta shida ita ce, haka kawai kana zaune a gida ko wajen aikinka, sai kaga jami’an tsaro sun zo da sammaci kan cewa ka aikata laifi a wuri kaza rana kaza ga wane ko wance; abin da ko kadan ba ka da masaniya a kai.  Wannan ya fi shahara a kasashen da suka ci gaba.  Inda za a sace katin shedar zama dan kasan mutum (National ID Card) ko katin tallafi na kasa (Social Security Card), ko kuma ayi jabunsa ta daya daga cikin dabarun da bayanansu suka gabata a baya, aje a aikata ta’addaci sannan a jefar da katin a wurin, ko kuma a kama mai laifi da wannan kati, amma ya gudu daga hannun jami’an tsaro.  Da zarar an zo nemansa, kai tsaye adireshin dake kan katin za a je.  Idan aka yi rashin sa’a ya fado kan mutum, haka kawai yana zaune a gida sai yaga jami’an tsaro sun zo don tafiya dashi.  Wannan na daga cikin mafi munin wannan ta’ada ta satar zati.  Domin idan mutum ya samu kansa a yanayi irin wannan, to, wanke kanshi kan zama da wahala sosai.  Bayanai kan haka na tafe, a bangaren “Munanan Tasirin Satar Zati.”

Sakonnin Sauya Tsarin Kati

Alama ta bakwai kan samu ne ta hanyar samun sakonnin dake nuna cewa bayanan da suka shafeka a taskar hukuma ta kasa, ko ma’aikatarku, ko kuma bankin da kake ajiya dasu, sun sauya sanadiyyar bukatar da ka nema.  Wannan ya fi faruwa ne a kasashen da suka ci gaba a fannin tattalin arziki.  Inda za ka iya zuwa hukumar dake lura da bayanan jama’a ko ka hau shafin hukumar ka duba bayanan da suka shafeka, a wasu lokuta ma ka bukaci sabunta bayanan, sanadiyyar ci gaba da ka samu a rayuwarka ko canjin adireshin gida ko wani abu makamancin wannan.  Da zarar ka aika da Karin bayanan, hukumar za ta duba bukatarka, sannan ta sabunta bayanan idan ta gamsu da tsarin da ka bi.  Idan ta sabunta, za ka samu sako ta waya ko na Imel dake sanar dakai wannan ci gaba.  To a wasu lokuta idan aka sace wa mutum bayanansa, ‘yan ta’adda na iya aiwatar da wannan sauyi ba tare da saninka ba.  Idan aka yi rashin sa’a basu sauya lambar wayarka dake kan shafinka a hukumar ba, kana iya samun sakon sanarwa da zarar an sabunta bayanan.  Wannan zai tabbatar maka cewa lallai akwai matsala.  Tunda ba kai bane ka bukaci wadannan sauye-sauye.  In kuwa haka ne, to kenan akwai wadanda ke kokarin sace maka zati da karfin tsiya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.