Waiwaye Adon Tafiya (9): Bitan Darussan Baya (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 14 ga watan Janairu, 2022.

263

Bayan Shekaru Hudu

Ga al’ada, bayan tsawon lokaci da muka dauka muna kwararo darussa a wannan shafi mai albarka, mukan yi zama na musamman a karshen shekara ko farkon sabuwar shekara, don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe kan kira “Adon tafiya.”  Haka abin yake tun faro wannan shafi mai albarka a shekarar 2006.  Zama na karshe da muka yi shi ne wanda ya gudana a shekarar 2017, bayan na kaddamar da “Taskar Baban Sadik” (https://babansadik.com), wanda shafi ne dake dauke da dukkan makalolin da masu karatu ke karantawa a wanann shafi a duk ranar Jumma’ar kowane mako.  A halin yanzu, bayan shekaru 15 da fara rubutu a wannan shafi na jaridar AMINIYA mai albarka, mun gabatar da makaloli guda 680.  A halin yanzu za mu yi bitar makalolin da muka amfana dasu ne tsakanin shekarar 2018 zuwa karshen shekarar 2021.  Wannan shi ne bita na 9!

Sakonnin Masu Karatu

Kamar yadda aka saba, masu karatu kan rubuto sakonnin tambaya ko neman makalolin da suka gabata, ko neman karin bayani, ko sharhi kan abin da suka karanta, ko kuma, a wasu lokuta, su min gyara kan kura-kuran da na tafka a daya daga cikin abin da na gabatar na rubutu.  A marhalar da ta gabata masu karatu sun aiko sakonni da dama.  Na kuma buga sakonnin masu karatu, dauke da sharhin amsoshin tambayoyinsu, a tsawon makonni 70, cikin shekarun 4 da suka gabata.  Wadannan sakonni kan kara min kwarin gwiwa, da karuwar ilmi da fahimta, da kuma wayewa, kan mu’amala da jama’a, da kuma koyon sababbin hanyoyin karantarwa.

Shahararrun Makaloli

- Adv -

Kamar yadda na ambata a sama, ya zuwa wannan mako na rubuta makololi guda 670 a wannan shafi mai albarka.  Wadannan makaloli sun karade fannoni daban-daban tsakanin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani da kuma zamantakewa.  Ga bayani kan shahararru daga cikinsu nan, kamar yadda muka saba.

Bayan gama bita na 8, makalar da ta biyo baya wacce ta shahara sosai kuma tayi tsayi, ita ce wacce na gabatar kan yadda ake satar zati a kafafen sada zumunta.  Takenta shi ne: “Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani”.  Jerin makaloli ne daga kashi na daya zuwa kashi na goma shabiyu (1 – 12).  Bayani ne kan yadda ake satar shafukan mutane a kafafen sada zumunta, da yadda ake satar bayanan banki na jama’a, da yin amfani dasu wajen satar kudade ko dukiyarsu, ko kuma aikata ta’addanci don batar da sawu.   Wadanda basu samu daman karanta wannan jerin makaloli ba, suna iya ziyartar Taskar Baban Sadik.  Ga adireshin dake dauke da bayanin: https://babansadik.com/satar-zati-a-kafafen-sadarwa-na-zamani-1/, ko kuma shafin AMINIYA dake: https://aminiya.dailytrust.com.  A karshen kashi na daya, za a ga ci gaban sauran makalolin.

Daga nan muka gabatar da Makala mai taken: “Tsarin Fasahar Faifan DVD”. Wannan ci gaba ne daga jerin makalolin da a baya (cikin shekarar 2010) muka faro, mai take: “Tsarin Ma’adanar Bayanai.”  Makalar Faifan DVD ta kunshi jerin makaloli 4 ne.  Bayan nan kuma sai muka bibiyi bayanta da Makala mai take: “Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam.”  Wannan, ta wata fuskar, ci gaba ne na makalar da muka fara a baya kan Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta, wato: “Genetics”.  Mun gabatar da jerin makaloli guda 6 a wannan karon, wadanda suka shafi bayani kan sabuwar hanyar yin kwaskwariman dabi’un halittar dan adam a zamanin yau, ta amfani da kwarewa a wannan fanni.  Ana iya karanta wadannan makaloli a bangaren “Dabi’u da Halayya” dake Taskar Baban Sadik.  Ga adireshin nan: https://babansadik.com/category/dabiu-da-halayya/.

Gama wannan silsila ke da wuya sai muka yi sharhin littafin babban malamina, Malam Salisu Webmaster dake Kaduna, mai take: “Kwamfuta”.  Mun yi wannan sharhi ne cikin makommi uku.  Kuma taken makalar shi ne: “Sharhin Littafin Kwamfuta”.  Ana iya karanta wannan sharhi a bangaren fasahar Kwamfuta dake Taskarmu, ta wannan adireshi: https://babansadik.com/category/kwamfuta.  Daga nan kuma na dano mana hira da sashen Hausa na BBC suka yi dani kan bikin ranar tsaftace fasahar Intanet ta Duniya na shekarar 2020.  Wannan hira mai tsayi ce, duk da ba cancan ba.  Mun gabatar da makaloli guda 4 kan haka.  Wato tsawon wata guda kenan.  Hakan yazo daidai da sadda aka cutar korona ta hana kowa sakat.  Nan take muka dubi tasirin hakan ga kamfanonin sadarwa na duniya.  Na yi hakan ne cikin makaloli guda 3, masu take: “Tasirin Killace Jama’a ga Kamfanonin Sadarwa Sanadiyyar Cutar COVID-19.”

Daga cikin manyan kalubale da yaduwar wannan cuta ta COVID-19 ta haddasa akwai yaduwar jita-jita masu dauke da karerayi.  Shahararriya daga cikinsu ita ce jita-jitar dake alakanta cutar korona da Fasahar sadarwa ta 5G.  A kan haka ne muka yi nazari mai zurfi, inda a karshe na kawo makaloli masu dauke da bayani kan ma’ana, da tarihi, da nau’uka, da amfani, da kuma illolin da ake hasashen wannan sabuwar fasaha na dauke dasu, sannan a karshe, muka yi nazari kan ko wannan fasaha tana da wata alaka da yaduwar cutar korona.  Wannan maudu’i ya dauke mu tsawon lokaci.  Domin sai da muka yi makonni 17 muka Magana kan wannan al’amari; watanni 4 da rabi kenan.  Ana iya riskar wadannan jerin makaloli a bangaren Fasahar 5G dake taskarmu, ta wannan adireshi:  https://babansadik.com/category/fasahar-5g/.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.