Manyan Fasahohi 5 Masu Tasiri a Duniya Waɗanda Har Yanzu Galibin Mutane Basu Fahimci Haƙiƙaninsu Ba a Aikace (1)

Manufar samar da fasahar AI shi ne, maimakon aikin da kake yi akan kwamfuta, ta hanyar ba ta umarni kai tsaye, ɗaya-bayan-ɗaya, don ta aiwatar maka da abinda kake so.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 20 ga watan Janairu, 2023.

105

Mabuɗin Kunnuwa

Shekaru 10 da suka gaba (daga shekara ta 2012 zuwa shekarar 2022), an ƙirƙiri wasu nau’ukan fasahohin sadarwa na zamani, waɗanda suke kan game rayuwa ta kowane ɓangare – fannin Likitanci, Ƙere-ƙere, Sadarwa, Tsarin karantarwa, Sararin Samaniya da sauransu.  Duk da shahararsu a bakunan mutane, da shafukan jaridu, da kafafen sadarwa na zamani, fahimtar haƙiƙanin waɗannan fasahohi da yadda suke aiki a aikace, ya zama abu mai wahala ga mutane.

Duk da cewa a asali ma dai, duk wata fasaha ta zamani, galibi idan ba ahalinta ba, ba kowa ke sanin yadda take aiki ba, a aikace.  To amma ta la’akari da yadda kafafen sadarwa na zamani suke kururuta ilmummukan zamani a yau, yasa kowa ke ganin ya san yadda waɗannan fasahohi ke aiki.  Sai dai, galibin fahimtar, kuskurarriyar fahimta ce.  A yau in Allah Yaso za mu yi nazari kan waɗannan fasahohi da irin abin da mutane suka fahimta kansu, da kuma asalin yadda suke, a aikace ko a nazarce.

Fasahar “Artificial Intelligence” (AI)

- Adv -

Wannan fasaha, duk da cewa sabuwar fasaha ce a yau, sai dai an jima ana haɓaka ta, musamman cikin shekaru 10 da suka gabata. Dukkan na’urar mutum-mutum, wato: “Robot” da ake amfani dasu a ma’aikatu da masana’antar ƙere-ƙere a ƙasashen da suka ci gaba, suna amfani da wannan fasaha ta AI.  Abin da fasahar ta ƙunsa shi ne, koya wa kwamfuta ko na’urar sadarwa – wayar salula da sauransu – hanyoyin koyo da aiwatar da wani aiki na musamman, ta hanyar bayyana mata matakan gudanar da aiki, da hanyoyin aiwatar da aikin, ta amfani da bayanan dake da alaƙa da aikin gaba ɗaya.  A hankali, da zarar ta daɗe tana yi, sai ta ƙware, ta ma fi ɗan iyawa.

Manufar samar da fasahar AI shi ne, maimakon aikin da kake yi akan kwamfuta, ta hanyar ba ta umarni kai tsaye, ɗaya-bayan-ɗaya, don ta aiwatar maka da abinda kake so.  A yanzu sai aka samar da fasaha ta musamman da za ka ba ta umarni ta aiwatar maka da waɗannan ayyuka cikin sauƙi.  Akwai wannan sabuwar fasaha a kusan dukkan manhajojin sadarwa na kwamfuta da wayar salula masu amfani da siginar Intanet, ko na’urorin sadarwa sababbi, irin su wayar salula da kwamfutoci na gama-gari da kwamfutoci na musamman (Special purpose computers).  A taƙaice dai, dukkan kafafen sada zumunta na zamani (Social Media Platforms) suna aiki ne da manhajojin da aka gina su da wannan sabuwar fasaha ta AI.  Shi yasa a kafar Facebook za ka ga ana bijiro maka da sunayen mutanen da ka sani a zahirin rayuwa, da waɗanda kayi makaranta ɗaya dasu, da waɗanda kake zama anguwa ɗaya dasu, da kuma waɗanda ke da ɗanɗanon tunani irin naka.  Haka a wurare irin su Instagram; za ka ga hotuna masu alaƙa da manufofin da ka zayyana a shafinka lokacin rajista, da mutanen da ke da alaƙa da irin bayanan da ka rubuta.  Kai, hatta a kotunan wasu ƙasashe ma, alƙalai na amfani da manhajoji masu ɗauke da fasahar AI wajen nazarin shari’o’i da kuma yanke hukunci.

A ɗaya ɓangaren kuma, an ƙirƙiri na’urorin sadarwa na zama da ake amfani dasu wajen gudanar da bincike kan cututtuka, da illolin jiki, da mahalli, da tsarin karantarwa, duk ta amfani da wannan sabuwar fasaha ta AI.  Ta ɓangaren wayoyin salula misali, akwai ƙananan manhajoji masu yawa da take amfani dasu masu ɗauke da wannan fasaha ta AI.  Shi yasa ake cewa, bayan Allah mahaliccinka, babu wanda ya sanka sosai irin wayarka ta salula, mai ɗauke da siginar Intanet, wacce kake amfani da ita wajen gudanar da rayuwarka ta yau da kullum.

Ta san wa kake kira a kullum, kuma su wa ke kiranka kullum;  ta san waye ba ka kiransu, kuma wace lambar waya ce baƙuwa cikin lambobin wayar dake kan wayarka; ta san manhajojin da kake amfani dasu – me kake yi dasu?  Su wa kake ta’ammali dasu a kan manhajar? Wasu manhajoji ne ba ka ma amfani dasu? – ta san ina kake zuwa a kullum?  Su wa kake zuwa wajensu (ta hanyar lambobin da kake kira kafin ka tafi, da amfani da manhajar taswira da kake yi wajen zuwa wajen); ta san sa’o’i ko adadin lokaci da kake kashewa a kan kowane ɓangare na wayar; ta san hotuna nawa ka ɗauka, a ina ka ɗauke su? Da wani lokaci ka ɗauke su?  Su wa da wa ka aika ma wa? Ta amfani da wace manhaja ka aika musu?; ta san sau nawa kake kashe ta kuma sau nawa ka kunna ta; ta san awanni nawa kake bacci, kuma meye abin da ka saba yi da ita kafin kayi bacci; ta san me ka rubuta, da wace manhaja ka rubuta, meye adadin abin da ka rubuta, wace rana ka rubuta, wa ka aika ma wa, kuma nawa aka caje ka (idan saƙon tes ne), ko kuɗin data nawa aka cajeka wajen aika saƙon; ta san wasu shafuka ka shiga a Intanet, da adireshinsu, da iya wuraren da ka ziyarta a cikinsu, da lokacin da ka ɗauka akan kowane shafi, da adadin bayanan da kayi ta’ammali dasu a shafin, da manhajar lilo (Browser) da kayi amfani ita wajen hawa shafin, da ranar, da watan, da wuraren da kake sadda ka hau shafin; ta san saƙonnin Imel nawa ka rubuta, wa ka rubuta ma wa, yaushe ka aika, an aiko maka jawabi ko a a, duk ta sani.  Bayan wannan, tana iya baka shawara kan me za ka yi, ta la’akari da abubuwan da kayi a baya, ko ta umarceka ma, idan kaƙi, nan gaba za ka ga sakamako.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.