Fasahar 5G: Siffofin Fasahar 5G

An buga wannan makala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 26 ga watan Yuni, 2020.

122

Siffofin Fasahar “5G”

Bayan bayani kan dalilin samar da marhalar sadarwa ta biyar da a yanzu ake kan gabatar da ita don dabbaka ka’idojin a na’urori da hanyoyin sadarwa na zamani a kasashen duniya daban-daban, wanda ya gabata a makon jiya, a yau cikin dacewar Allah za mu dubi siffofin da wannan marhala ta biyar mai suna “5G”, da hanyoyin da suka banbanta ta da sauran marhaloli ko zamunnan sadarwa da suka gabata a shekaru da zamunnan baya. Hakan na cikin dalilan da zasu sa mai karatu ya kara fahimtar dalilan da suka sa aka yi wannan yunkuri don nemo wani sabon tsari.

Babbar siffa ta farko ita ce, fasahar “5G” na dauke ne da tsarin sadarwa mai karfin gaske, wajen daukan adadi mai yawa na na’urorin sadarwa a lokaci guda, a wuri guda, kuma ta hanya daya. Misali, idan mutane sama da dari suka taru a wani dakin taro ko gidan kallo, ko masallaci, ko wata kasuwa mai girma ko filin wasanni, fasahar “5G” na iya baiwa dukkansu damar mu’amala da fasahar Intanet, wajen aikawa da sakonni ko karbarsu, ko mu’amala da bidiyo ko sauti daga wasu gidajen yanar sadarwa, ko kallon shirye-shiryen gidajen talabijin kai tsaye, ba tare da wani tsaiko ba. Idan a misali fasahar “4G” na baiwa mutum hamsin ne irin wannan dama, to, fasahar “5G” na iya ninka wannan adadi sau dari, akan adadin da tsarin “4G” ke iyawa, cikin yanayi da karfin sadarwar da suka shallake tsarin “4G”. Domin a tsarin fasahar “5G”, adadin na’urorin sadarwa na iya karba ko aika sako a lokaci guda ba tare da samun takaituwan adadin bayanan da kowannensu ke karba ko aikawa ba.

Amma a tsarin “4G”, wanda muke masa bankwana a halin yanzu, idan mutum 2 suka hau wani shafin sadarwa don saukar da sakon bidiyo misali, idan kowannensu na karbar bayani megabyte 2 a duk dakika, da zarar mutane 2 sun hau wannan shafi su ma don karban wasu bayanai, nan take adadin bayanan da biyun farko ke karba zai ragu. Ma’ana, iya karancin masu saukar da bayanai, iya yawan bayanan da kowannensu zai iya karba a lokaci guda. Iya yawansu kuma, iya karancin bayanin da kowanensu zai karba, tunda adadinsu ya karu. Amma a tsarin fasahar “5G” ba haka abin yake ba. Yawan masu saukar da bayani ko aiwatar da sadarwa a lokaci guda, ba ya tasiri wajen adadin sakonni ko bayanan da kowanensu ke saukarwa a lokaci.

Siffa ta biyu ita ce, tsarin fasahar “5G” ba shi da saibi wajen aiwatar da sadarwa. Abin da wannan ke nufi shi ne, a tsarin sadarwa, idan kana sauraron shirin gidan rediyo, ko kallon shirin talabijin, ko sauraren wasu bayanai na sauti kai tsaye daga wani gidan yanar sadarwa ta Intanet, akwai ‘yar tazarar lokaci tsakanin sadda wayarka ko kwamfutarka ta karbo sakon, daga kwamfutar dake dauke da bayanan ko inda ake shirya shirin, zuwa lokacin da wayarka ko kwamfutarka za a jiyar da kai ko nuna maka sakon da ta dauko. Haka ma a tsarin wayar salula akwai wannan yanayi.

- Adv -

Idan ka kira mutumin dake kasar Saudiyya ta wayar salula, akwai ‘yar rata dake samuwa tsakanin sadda yayi magana da lokacin da kaji maganarsa. Kana iya gane hakan ne ta hanyar jin yayi shiru, bayan ka gama naka zancen, a lokacin sakon muryarka bata kai gare shi ba. Sai sakon ya isa gare shi, sai kaji ya fara baka amsa. Masu sauraron hirar da gidajen rediyon BBC ko VOA ko DW Hausa misali, sun saba jin wannan idan ana hira da wani dake wata kasa da akwai tazara tsakaninsu. Wannan ‘yar tazara ko saibin jin magana ko karban sako tsakanin kayayyakin sadarwa na samuwa ne sanadiyyar jinkirin da na’urar sadarwar ke yi yayin dauko sakon da isar dashi inda aka aiko shi. A fasahar sadarwa ta zamani, wannan jinkiri shi ake kira: “Communication Lag”, ko kuma “Lag” a gajarce.

A tsarin sadarwa na fasahar “5G”, babu wannan jinkiri ko saibin da ake samu tsakanin karba da isar da sako tsakanin na’urori da hanyoyin sadarwa. Da zarar ka bukata, nan take za ka samu. Haka da zarar wayarka ta aiwatar da sadarwa da wata kwamfuta don karbar sako, ana bata, nan take za ka same shi. Idan sauti ne, sadda kwamfutarka ke karba sannan kake jinsa. Idan bidiyo ne, sadda abin ke faruwa sannan kake ganinsa. Duk nisan dake tsakanin na’rorin kuwa.

Siffa ta uku daga cikin siffofin tsarin fasahar “5G” ita ce, isar da sakon bayanai masu dimbin yawa cikin dakika guda. A gwajin fasahar “5G” da kamfanin wayar salula ta MTN dake Najeriya yayi a shekarar 2019 a Abuja, an saukar da bidiyo mai nauyin gigabyte 2.3 cikin dakiku (seconds) 15.78. Da aka saukar da bidiyon a tsarin “4G” kuma, sai da ya dauki tsawon minti 5.3. Wannan a gwaji kenan, kuma a kadadar sadarwa ta kasa, mafi karancin kuzari. Amma idan aka gama tsara komai, ta amfani da waya mai dauke da tsarin fasahar “5G”, wayarka ko kwamfutarka na iya saukar da bayanin da mizaninsa ya kai gigabyte 1 cikin dakika guda. Idan aka yi amfani da kadadar sadarwa na kololuwa kuwa, wanda bayaninsa zai zo nan da makonni biyu, kana iya saukar da bayanin da mizaninsa ya kai gigabyte 10 a dakika guda! Tirkashi! A mafi ingancin kuzari, tsarin “4G” na iya saukar maka da mizanin bayanai iya megabyte 250 ne a dakika guda. Wannan daya cikin kashi 4 na abin da mafi karancin kuzarin tsarin fasahar “5G” zai saukar maka kenan a dakika guda. Don haka, ko kadan babu hadi a tsakaninsu.

Siffa ta gaba ita ce, fasahar “5G” na dauke ne da hanyoyi da tsarin sadarwa tsakanin kayayyaki da na’urorin sadarwa daban-daban, wadanda a al’adance ba a sansu da wani tsari na aiwatar da sadarwa ba. Misali, karkashin tsarin fasahar “5G”, motocin lantarki marasa direba (Driverless Cars) suna iya musayar bayanai tsakaninsu a ko ina suke, don gano bigire da tazarar ‘yar uwarta. Na’urori a asibitoci da manya da kananan makarantu na iya aiwatar da sadarwa tsakaninsu. Haka kananan na’urori da ake kira: “Internet of Things” ko “IoT” a gajarce, duk suna iya amfani da fasahar Intanet don aiwatar da dasarwa. A kasashen da suka ci gaba, kana iya samun gida mai dauke da hanyoyi da kayayyakin sarrafa gida masu amfani da tsarin Intanet. Misali, na’urar sarrafa talabijin a ko ina kake, ko sarrafa wutar lantarkin dake gidaje, daga wani wuri. Sai kaga mutum na zaune a ofishinsa, amma ya kunna wutar lantarkin dake dakinsa a gidansa. Ko ya kunna talabijin din gidansa ko kuma ya kasha, idan ya mance ya barshi a kunne, duk daga ofishinsa. To, a karkashin tsarin fasahar “5G”, wannan tsari na sadarwa zai yadu sosai, ya kuma yawaita, tare da saukaka hanyoyin mallakar na’urorin.

Wadannan su ne manya cikin siffofin tsarin fasahar “5G” da ake kan kadamarwa a duniya baki daya. Siffofi ne da suka sha gaban sauran marhalolin da aka wuce a baya. Dangane da tambayar ko nan gaba za a iya samun wani tsarin kuma da ya wuce tsarin fasahar “5G”? Amsar ita ce, eh ana iya samu, ko da kuwa yunkuri ne na inganta tsarin. Domin babu wani abin da yake dindindin a wannan duniya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.