Shafinku Ya Cika Shekara 10

Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.”  A yanzu shekarun wannan shafi namu goma kenan da watanni shida cif-cif.  Kuma wannan shi ne zama na takwas da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya.  Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Nuwamba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha.  Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku da na hudu da na biyar da na shida da na bakwai ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2016.  Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na bakwai, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2016.

668

Tuna Baya…

Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na takwas.  A yau ma za mu yi nazari ne kan darussan da muka koya a wannan zango, duk da cewa ba su da yawa.  Bayan haka, za mu ga yawan kasidun da muka kawo a zangon, da abin da suke karantarwa, da irin usulubin da muke bi wajen tafiyar da shafin, da tsarin mu’amala da masu karatu, da kasidun da ba a gama su ba, sannan mu ji inda za mu dosa a zangon da ke tafe.  Har wa yau, muna dauke da babbar albishir, wanda ya kunshi cika alkawarin da na dauka cikin watan Satumbar bara.

Me Muka Koya Daga Darussan Baya?

A wannan Zango bamu dai bamu gabatar da kasidu masu yawa ba, sabanin sauran marhaloli da suka gabata.  Abin da yafi komai yawa a wannan marhala dai shi ne amsoshin sakonnin masu karatu.  Da  farko dai munyi bayani kan kimiyyar lantarki, cikin kasida mai take: Kimiyyar Lantarki a Sawwake.  Mun samu kashi na daya zuwa na biyar.   Ba wani nisa muka yi ba sosai, saboda muna hada kasidar ne da kasidar koyon “Programming.”  Don haka mun dakata a kashi na biyar ne.  manufarmu ita ce mu zurfafa bincike cikin wannan fanni don ilmantar da masu karatu kan abin da ya shafi makamashin lantarki da tasirinsa ga rayuwar al’umma.

A daya bangaren kuma, mun fara silsila cikin fannin gina manhajar kwamfuta.  Hakan ya zo ne sanadiyyar yawan tambayoyi da neman karin bayani daga masu karatu kan yadda ake gudanar da wannan sana’a mai matukar tasiri a duniyar sadarwa.  Taken kasidun shi ne: Mu Koyi “Programming” a Sawwake, a Hausance.   Da yawa cikin karatu sun yaba wannan kasida matuka.  Tana cikin kasidun da suka shahara sosai, duk da karancin lokacin da aka fara sako ta.  A halin yanzu mun dakata a kashi na tara ne, in ban mance ba. 

A bangaren karshe sai tambayoyi da sakonnin masu, wadanda suka taru tun cikin marhala ta bakwai.    A cikin wannan marhala da muke wa bankwana, mun kwashi makonni sama da ashirin muna amsa tambayoyin masu karatu zalla.  Galibin tambayoyin sun fi ba da karfi wajen fannin kimiyya da fasahar sadarwa.  A halin yanzu akwai tarin sakonni har wa yau dake jiran amsa.  Mun dan dakata ne don kada mu kwashe lokacin filin wajen amsa tambayoyi zalla, duk da cewa shi ma hakan na da nashi fa’idar.

Alkawari Kaya…  –  TASKAR BABAN SADIK (https://babansadik.com)

A cikin watan Satumbar bara na yi wa masu karatu alakwarin cewa zan gina gidan yanar sadarwa na musamman, ba “Blog” ba, don zuba dukkan kasidun da na taba rubutawa a wannan shafi mai albarka, tare da sauran makalolin da na gabatar a wurare daban-daban da aka gayyace ni don wannan munasaba.  Kari a kan haka, na tabbatar da cewa  wannan shafi gidan yanar sadarwa ne na kashin kaina da zan gina da hannuna, ta amfani da dabarun gina gidan yanar sadarwa na zamani.

A halin yanzu na gama gina wannan gidan yanar sadarwa, kuma na sa masa take: “TASKAR BABAN SADIK.”  Za a iya samunsa a adireshin dake sama, wato: https://babansadik.com, ko www.babansadik.com, ko kuma https://babansadik.com.  Duk wanda aka shigar a manhajar lilo (Browser) zai kai mai ziyara zuwa shafin kai tsaye.   Idan an mance adireshin ma, a shiga Google dake kwamfuta ko wayar salula, a rubuta: “Taskar Baban Sadik,” cikin yardar Allah za a ga shafin a sama.  Wannan kenan.

- Adv -

Me Taskar Ta Kunsa?

Wannan taska dai ta kunshi dukkan kasidun da na taba gabatarwa ne a wannan shafi mai albarka.  A halin yanzu taskar na dauke da kasidu 339, da kuma amsoshin tambayoyi da suka kai kasidu guda 119.  Idan ka hada gaba daya zaka samu kasidu guda 458 kenan.  A yayin da mai karatu ke karanta wannan shafi, tuni kasidun sun karu, domin har da wannan bita da muke yi zai hau kai nan take.  Na karkasa wadannan kasidu ne zuwa fannonin ilimi sama da 20, don bai wa mai karatu daman zaban abin da ya dace da dandanonsa.

Manyan bangarorin dake shafin su ne bangaren Kimiyya da kuma Fasaha.  A karkashin Kimiyya akwai: Lantarki, da Dabi’u da Halayya, da Kur’ani da Zamani, da Kere-kere, da Mahalli da Sinadarai, da Teku, da Sararin Samaniya da kuma Kwakwalwa da Zuciya.  A bangaren Fasaha kuma akwai: Intanet, da Imel, da Kwamfuta, da Kariyar Bayanai, da Dandalin Abota, da Sadarwa, da Rediyo, da Gina Manhaja, da kuma Wayar Salula.  Bayan wadannan manyan bangarori biyu, akwai shafi na musamman kan kasidun da suka shafi al’ummar Hausawa da harkar sadarwa.  Sannan akwai shafi mai take: “Hira da Masana,” wanda ya kunshi nau’ukan hirarrakin da aka yi dani ko wani masani kan harkar sadarwa da kimiyyar sararin samaniya.

Bayan haka, akwai shafi na musamman mai dauke da amsoshin tambayoyin masu karatu guda 119 da nayi bayani a sama.  Sai shafi mai suna: “Waiwaye,” wanda ke dauke da dukkan kasidun da na gabatar don yin bita.  Shi kanshi wannan bita da mai karatu ke karantawa yanzu, can zan je.  Akwai kuma bangare ko shafi mai suna: “Rayuwata.”  A wannan bangare akwai shafuka dake bayani kan rayuwata, da sakonnin bidiyo, da na sauti, da kuma laccocin da na taba gabatarwa a wasu wurare da aka gayyace ni, sai kuma shafi na musamman don saukar da dunkulallun kasidu, wadanda shafukansu suka zarce shafi 10.  Kasida mafi tsayi da muka taba gabatar ita ce wacce muka zurfafa bayani kan dukkan bangarorin wayar salula, mai take: “Tsarin Mu’amala da Wayar Salula.”  Tana dauke da shafuka 84 ne.

Abu na karshe shi ne, akwai wurare ko hanyoyin mu’amala da ni a wannan shafi.  Akwai inda za ka iya aikawa da sakonni gare ni kai tsaye, da inda za ka iya ba da adireshin Imel don a rika tuntubarka da zarar an loda sababbin kasidu a shafi.  Sannan a karshe shafin kowace kasida akwai karamar akwati mai dauke da hotona da takaitaccen bayani kaina.  A kasansa kuma akwai kasidu masu alaka da kasidar da aka karanta a shafin, guda uku.  Sai kuma fam da aka tanada don mai karatu ya ba da ra’ayinsa ko karin bayani kan abin da ya karanta.  Na yi iya kokarin ganin na “Hausantar” da shafin gaba daya, don bai wa masu karatu saukin mu’amala a taskar.  Zan kuma bude shafi mai take: “Makaranta” don koyar da ilimin sadarwa da kwamfuta a aikace, ga masu karatu.

Kammalawa – Godiya da Yabo

A karshe dai, ina mika godiyata ga dukkan masu karatu; tsakanin masu bugo waya, da masu rubuto tes, da wadanda ma ba a jin duriyarsu, wanda su ne suka fi yawa.  Allah saka wa kowa da alheri.  Ina mika godiyata ga Editan Aminiya Malam Balarabe, da irin gudunmawar da yake bani, tare da hakuri da ni sanadiyyar halin da na samu kaina na yawan aikace-aikace.  Sai godiya ga Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo), da Malam Ahmad Garba, masu lura da wannan shafi nawa. Ina godiya gare su matuka, musaman wajen shawarwari da suke bani kan yadda zan inganta  shafin baki daya.  Godiya ta musamman har wa yau ga Malam Salihu Makera, wanda babban Yaya yake gare ni, don abokin Yayana ne, tun ina Sakandare.  Sai Malam Bashir Yahuza Malumfashi.  Sannan ina godiya ga kamfanin Media Trust da hukumar gudanarwarsa baki daya.

A karshe, bazan mance da ma’aikatan Sashen Hausa na BBC da irin sanayyar da suke baiwa shafin wajen gayyata na ofishinsu, da yin hira da ni kan al’amuran da ke faruwa a fannonin kimiyyar sadarwa musamman ba, da kuma amsa tambayoyin masu sauraronsu.  Su ma a wannan zango sun gayyace ni bila-adadin zuwa ofishinsu da ke nan Abuja. Ina godiya matuka, musamman ga Babban Edita da sauran ma’aikatansu irinsu: Malam Muhammad An-Noor, da Malam Ibrahim Mijinyawa, da Malama Raliya Zubairu, da Malam Naziru Minka’ilu, da Malam Nasidi Yahaya, da kuma babban Kochinmu, Malam Mammam Skipper, da dai sauransu.

Jama’a, zan dakata a nan, sai Allah ya hada mu a mako mai zuwa.


An buga wannan kasida a jaridar Aminiya na ranar 19 ga watan Mayu, 2017.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.