Waiwaye Kan Darussan Baya (1)

Masu karatu ku gafarce ni wannan mako.  Ba mancewa nayi kan alkawarin da nayi ba, cewa zan kawo bayanai kan ”Yadda Ake Neman Bayanai a Yanar Gizo.”  Ina sane.  Babban abin da yasa na taka mana burki shi ne don muyi waiwaye, abin da Malam Bahaushe ya kira “adon tafiya.”  Kada gabanku ya fadi, ku dauka ko karshen wannan shafi kenan.  A a, zamu ci gaba da kwararo bayanai insha’Allah, sai inda karfi ko iliminmu ya ƙare.

185

Da farko dai ina so in mika godiyata ga masu rubuto saƙonni ko bugo waya, ko aiko da gajeren saƙo ta wayar salula, watau text message.  Haƙiƙa na kan ji dadi kuma kamar yadda a kullum nake cewa shi ne; babu waɗanda suka cancanci wannan yabo irin Hukumar Media Trust, masu buga wannan jarida mai alabarka ta AMINIYA, musamman ma Edita, Hajiya Aishah, da kuma Malam Abubakar AbdurRahmaan, wanda aikinsa ne karbowa da kuma shirya wannan shafi da nake gabatarwa a duk  mako.   Haƙiƙa ta waɗannan saƙonni na fahimci abubuwa da dama.  Wannan yasa na yanke shawaran kawo waɗannan gajerun shawarwari, waɗanda na tabbata zasu taimaka ma mai karatu a hanyarsa ta mu’amala da wannan bakuwar hanyar sadarwa.  Da haka nima na fara, kuma duk da yake ba wani cikakkiyar kwarewa nake da ita ba kan wannan fasaha, a kalla zan iya bayar da shawarwari iya gwargwadon fahimta da sani na.

Ƙasidun da Suka Gabata

Idan mai karatu bai mance ba, wannan shi ne mako na bakwai da muka fara aiko da waɗannan maƙaloli.  A ƙasidar farko mun yi gabatarwa kan ma’ana da tarihin Intanet, da nau’ukan Intanet.  A makon da ke biye da shi kuma muka kwararo bayanai kan amfanin Intanet, da kebantattun siffofin wannan fasaha mai ban al’ajabi.  A mako na uku mai karatu ya karanta bayanai kan yadda ake gina gidan yanan sadarwa, watau Web Designing.  Daga nan muka turo bayani kan yadda ake lilo da tsallake-tsallake a waɗannan shafuka ko gidajen yanan sadarwa.  A mako na biyar mai karatu ya karanta yadda ake budewa da kuma mu’amala da akwatin wasikar hanyar sadarwa, watau Imel.  A mako na shida kuma sai ƙasidar Hira da Tattaunawa ta biyo baya.

Ina da yakinin cewa masu karatu sun karu da wani abu, duk kankantansa.  Domin a tabbace yake cewa mafi yawancin waɗanda suka yi ta aiko da saƙonni basu jima da fara amfani da wannan fasaha ba; wasu kuma ma sai ta waɗannan ƙasidu suka san yadda ake mu’amala da ita.  Tabbas akwai da dama da suka jima suna ta’ammali da fasahar Intanet, amma duk da haka, samun bayanai cikin harshen Hausa kan yadda ake sarrafa wannan fasaha shi kanshi wani ci gaba ne, ko da mutum ya jima yana lilo a giza-gizan sadarwa.  A gaba zamu ci gaba da aiko ƙasidu, kuma zan yi iya ƙoƙari na wajen ganin na daɗa sauƙaƙa bayani cikin ƙasidun, don mai karatu ya samu fa’ida mai yawa, insha’Allah.  Kafin nan, zan so mai karatu ya lura da wasu abubuwa masu mihimmanci dangane da mu’amala da Kwamfuta da kuma Fasahar Intanet, kamar haka:

Sha’awa

Wannan shi ne babban garkuwa da mai karatu yake buƙata.  Sha’awar da nake nufi a nan ita ce abin da ake kira “Interest”, a turance.  Ya zama kana son yin abin, kuma kana kulawa da irin ci gaban da kake samu lokaci lokaci.  Domin idan baka da sha’awa, to babu yadda za a yi ka riƙa kulawa da shiga Yanar Gizon, balle har ka samu fa’idojin da ke tattare da wannan fasaha.  Kada ka damu cewa “ai ban taba mu’amala da kwamfuta ba”, duk wannan ba hujja bane.  Idan kana da cikakkiyar sha’awa, nan da nan za ka koya.  Shekaru shida da suka gabata, ko kusa da kwamfuta bana yi, saboda tsaban tsoro.  Domin a kullum gani nake kamar idan na taba jikin kwamfutar, lalatata zan yi.

Amma na fara gina sha’awa na ne lokacin da nake ta mu’amala da gidajen rediyon BBC da Deuschewelle dake Jamus, da irin su Voice of America.  Nakan ji suna ambaton adireshin Imel dinsu, ni kuma ba a abin da na fi buƙata a rayuwa illa in aika da saƙo, ya isa cikin gaggawa.  Don haka wata rana sai na rubuta saƙo zuwa ga BBC Sashen Turanci (The Learning Zone), na samu wata baiwar Allah da ke sashin kwamfuta a ofishinmu ta aika musu.  Sai ta dinga min yanga.  Har sai da na harzuƙa.  Daga lokacin na yanke shawaran koyan kwamfuta da shiga Intanet.  Ba a dauki lokaci mai tsawo ba Allah Yai mani muwafaka.  A yanzu bana iya kwana ba tare da nayi shaukin taba kwamfuta ko shiga Intanet ba.  Ya zama kamar jinin jikina.

duk wannan ba komai ya kawo haka ba, sai tsaban sha’awa da nake dashi kan hakan.  Ban taba zuwa makaranta don koyon ilimi da aiki da kwamfuta ba, balle yadda ake mu’amala da Intanet.  Don haka, idan mai karatu ya gina sha’awarsa kan wannan fasaha, ina tabbatar masa cewa nan ba da jimawa ba zai samu bakin zaren.

Karatu da Aiki Da Shi

Abin da ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet ke buƙata bayan sha’awa, shi ne aiki da abin da ka karanta.  Domin idan baka aikata abubuwan da kake karantawa, to zai yi wahala ka iya komai a harkan.  Domin shi wani fanni ne wanda karantunsa ke rataye da aiki.  A wasu lokuta ma za ka samu aikin ya fi karatun yawa.  Duk lokacin da ka karanta yadda ake mu’amala da gidan yanan sadarwa, dole ne ka samu Intanet, ka aikata wannan ilimi a aikace.  Babu abin da za ka koya a harkan Kwamfuta da Intanet ba tare da kayi karatu ba; kuma baka iya komai, idan baka kwatanta abin da ka karanta ba.  Don dole ne mai karatu ya riƙa kwatanta ilmummukan da yake dauka cikin ƙasidun da muke aikawa mako-mako.  Wannan ne zai bashi daman auna ilminsa kan abin da yake karantawa.  Duk inda ya cije, sai yayi tambaya.  Wannan tasa nake zaburar damu kan abin da ya shafi neman bayani cikin dukkan abin da mai karatu ya karanta amma bai fahimta ba.  Ko ya koya, amma da yaje aikawa sai ya gab a haka abin yake ba.   Yin tambaya ne kaɗai zai wayar maka da kai cikin abin da kake nema.

- Adv -

Galibin abubuwan da na tara na ilimi da aiki kan wannan fasaha, ya ta’allaƙa da tambayoyin da nake kusan a kullum.  Idan abubuwa suka cakude mani, na kan rubuta ma Farfesa Abdallah Uba Adamu dake Jami’ar Bayero saƙon Imel, don neman ƙarin bayani.  Wasu lokuta kuma sai in nemi bayani (Search) ta hanyar matambayi ba ta ɓata, watau Search Engine, wanda zamu kawo bayaninsa mako mai zuwa, in Allah Ya yarda.  Don haka, mai karatu ya sa a cikin zuciyarsa cewa dole ne ya aikata abin da ya koya, kuma duk inda ya samu matsala, to yayi tambaya.  Domin matambayi, inji Hausawa, baya bata – sai dai in bai yi tambayar daidai ba, ko kuma yadda ta dace.

Manufa

Wannan ya kawo mu kan mataki na gaba, watau manufa.  Kafin nan, yana da kyau mai karatu ya san cewa “kamar yadda ya san cewa zuwansa duniya na da manufa mai karfi,”  to dole ne ya san cewa a duniyar gizo ma sai ya riki manufa kwakkwara, idan kuwa ba haka ba, sai ya bace.  Wannan ya faru ne saboda duniyar Intanet wata irin duniya ce mara badala; babu kyaure, muddin a ciki kake.  Kuma yadda kasashen duniya suka kasu kashi-kashi, to haka manufofi da ra’ayoyin mutane suke birjik.  A duniya irin wannan, idan baka da manufa, sai ka narke cikin rubibi.  Samun manufa ya kasu kashi-kashi;  manufa wajen lilo da tsallake-tsallake.  Wani irin gidan yanan sadarwa za ka ziyarta?  Me kake buƙata a ciki?  Dole ne ka samu manufa a nan, idan ba haka ba, sai ka ci ƙaro da miyagu.  Manufa wajen hira da tattaunawa; su waye abokan huldanka a Intanet?  Wani irin mu’amala kake dasu?  Duk sai ka tantance.  Har wa yau, yana da kyau ka san irin majalisar da za ka riƙa shiga.  Wannan na rataye ne da irin manufarka da kuma abokan da ka shaƙu dasu.

Domin a duniyar Intanet, akwai  wuraren da za ka iya ziyarta gaba gadi.  Akwai waɗanda za ka iya shiga da kyar.  Akwai kuma waɗanda duk tsiyarka baza ka iya shiga ba said a izni.  Ya dai danganta da irin abin da ya kaika wajen.  Kafin in karƙare wannan ɓangare, yana da kyau mai karatu ya san cewa yadda dabi’un mutane suka karkasu a rayuwar yau da kullum, to haka ire-iren waɗannan ɗabi’u suke a duniyar Intanet.  Idan addini kake so akwai.  Idan holewa kake so, akwai mazauninta.  Idan neman kudi kake son yi, ta hanyar da ta dace da wacce bata dace ba, duk akwai su.  Duk irin abin da kake buƙata na ɗabi’u, baza ka rasa mazauni ba.   Don haka nake karfafa Magana kan manufa.  Me kaje yi?

Haƙuri da Juriya

Komai dan haƙuri ne, musamman idan aka ce ya shafi neman ilmi da aiki da shi.  Mu kwatanta rayuwarmu na addini mu gani mana; sau nawa muka ji wa’azi kan hani daga aikata zunubi, kuma sai nawa muka yi amfani da wannan hani?  To balle Intanet, wacce a ciki babu wanda zai kwaɓe ka kan irin Gidan Yanan da za ka shiga, sai tsaban tarbiyyan da kake da ita.  Haƙuri ya kasu kashi biyu a Intnet; juriya wajen kamewa daga aikata alfasha.  Da kuma juriya wajen dagewa da ganin ka koyi abin da zai amfaneka.  Ba za ka san ɗimbin ilimin da ke maƙare a giza-gizan sadarwa ta Intanet ba sai ka fara mu’amala da ita.

Kowane irin ilimi kake son koyo, za ka iya samunsa in Allah Ya yarda.  Abin da kake buƙata kawai shi ne sanin abin da kake nema, da kuma inda za ka je ka sameshi.  Haƙurin da ya fi kowanne shi ne wanda za ka yi wajen koyon ilimi; ilimin kwamfuta da Fasahar Intanet nake nufi.  Domin wani fanni ne dake tsarinsa ke sauyawa kusan a dukkan dakika ko bugun agogo.  Yana buƙatar a kullum ka riƙa mu’amala da shi don sanin irin sauye-sauyen da ke samuwa a kullu. Idan ba haka ba sai ka zama bakauye cikin kankanin lokaci.  Domin ana ƙirƙiro sabbin hanyoyin mu’amala da Intanet kusan a kullum.  Wannan tasa dole mai karatu ya zama mai juriya da haƙuri wajen lazimta da mu’amala da kowane irin ɓangare ne na wannan fasaha.  Idan hakan ya zama maka jiki, ba zai riƙa damunka ba, in Allah Ya yarda.

Kammalawa

Dangane da bayanan da suka gabata, na tabbata mai karatu ya dauki mataki kan tsarin da zai bi wajen mu’amala da wannan fasaha.  Kuma kamar yadda masu karatu suke yawaita bayar da shawara cewa mai zai hana in mayar da waɗannan ƙasidu zuwa littafi mai zaman kansa.  To ina son sanar dasu cewa a halin yanzu  akwai wanann littafi a rubuce, amma saboda ayyuka da suka addabe ni a ofis, ban riga na ɗabba’a shi ko ba.  Amma nan da wasu watanni masu zuwa insha’Allah zan sanar da ku halin da ake ciki.  Akwai gyare-gyare da kuma ƙare-ƙare da zan yi saboda tsawon lokacin da na ɗauka ban buga ba.  Domin kusan dukkan ƙasidun da nake aikowa, da ka nake hararo su, ba da littafin nake amfani ba gaba ɗaya yanzu.  Daga ƙarshe, ina kara sanar da masu karatu cewa samun lokaci, haƙuri da juriya, manufa da kuma amfani da ilimi, sune manyan dirkokin da ake buƙata wajen ci gaba da hulda da wannan fasaha.  Duk abin da mai karatu bai gane ba, sai ya rubuto.  Insha’Allah zan yi iya ƙoƙari na wajen ganin na taimaka.

Sai mun sadu mako mai zuwa!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.