Sakonnin Masu Karatu (2009) (13)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

75

Baban Sadik, tambaya ta ita ce: shin yaya zan yi in aika da sakon Imel ga mutane da yawa a lokaci guda?  –  Bashir, Minna, Naija: bashir.kasim@yahoo.com

Malam Bashir, aikawa da sakon Imel ga mutane masu yawa babu wahala.  Idan ka budo allon rubutu, wato “Compose”, sai ka shigar da adireshin wadanda kake son aika musu a filin da aka rubuta “To”.  Idan ka rubuta adireshin farko, sai ka sanya alamar wakafi (wato “comma” – , -), sannan ka sanya na biyu, ka sa wakafi, ka sanya na uku, ka sa wakafi…har sai ka sanya dukkan adireshin wadanda kake son aika musu.  Wannan haka tsarin yake: a kwamfuta kake, ko a wayar salula.  Da fatar ka gamsu.   


Salam Malam, sai naga layin MTN a wayar salula mai Katin SIM guda biyu, yana komawa “MNT”.  A wata wayar kuma, layukan suna komawa lambobi maimakon sunan kamfanin wayar.  –  Khalil Nasir Kuriwa, Kiru, Kano: 07027275459

Malam Khalil, ta yiwu akwai matsala tare da wayar.  Don kusan dukkan wayoyin salula na zamani suna da manhajar da ke iya nuna sunan kamfanin wayar da aka sanyan musu katin SIM dinsa.  Idan kaga wayar na nuna maka “MNT”, maimakon “MTN”, a iya cewa matsalar daga wayar ce, ba daga kamfanin wayan ba.  In kuwa daga kamfani wayan ne, to bai kamata ya zama a wayarka ce kadai matsalar ba, musamman a bangaren da kake.  Kamata yayi a ce dukkan masu amfani da katin MTN su ma nasu ta rika nuna “MNT”. 

- Adv -

A daya bangaren kuma, rashin nuna sunan kamfanin waya a fuskar waya kuma, ya danganci kirar wayar. In har wayar ‘yar asali ce (irin nau’in “Samsung” mai katin SIM guda biyu, ‘yar asali), ba irin kirar Sin ba, ya kamata ta nuna. Amma idan kirar Sin ce, ba matsala idan bata nunawa.  Hakan na iya zama nakasa ce daga kamfanin da ya kera wayar; ma’ana bai tarbiyyantar da ita yin hakan ba. Da fatan ka gamsu.


Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta dangane da wayar salula ce: shin da kira, da amsa kira, wanne ne yafi cin batirin waya ne?  –  Aliyu Muktar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

Ya danganci tsarin mu’amala da wayar.  Idan wayar salula tana ajiye a kunne, ba a amfani da ita, bata cin batir sosai. Kamar mota ce ka tayar da ita, ka barta tana diri (slow).  Idan kana shiga wurare don shigar da lamba ko gogewa ko wani abu daban, cin batirinta yafi na lokacin da  take ajiye babu komai.  Idan kuma kana sauraron wakoki, ko kallon talabijin, ko sauraron rediyo, ko yin wasa (da “games”) da sauran makamantansu, cin batirinsa yafi na yanayin baya. 

A karshe, idan wayar tana mu’amala da wata wayar, ta hanyar aika sako ta Bluetooth ko Infra-red ko Kwamfuta, ko kuma tana halin kara sanadiyyar kira (ringing), ko yanayin amsa kira ko yin kira da Magana da abokin kira, ko neman balas, ko neman yanayin sadarwa (Network Search), wayar tafi cin batir sosai. A takaice dai, idan waya tana mu’amala da wata wayar (ta hanyar kira ko amsa kira ko karba ko aika bayanai), ko kuma tashar sadarwar kamfanin waya (Telecom Base Station), tafi cin batir sosai.  Illa dai yanayin cin ya danganci tsawon lokacin da aka dauka ne ana kira ko amsa kiran, ko aikawa da sakonnin ko karbansu.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.