Mudawwana – “WebLog” ko “Blog” – (2)

 Idan mai karatu bai mance ba, a makon da ya gabata mun kawo bayanai ne kan Mudawwanar Intanet, wato Web Log, a turance, da tarihinta da kuma yadda ake mallakar mudawwana ga duk mai son yada nasa ra’yin don wasu su karanta a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Na san da dama cikin masu karatu sun fara himma wajen gina nasu mudawwanar, sakamakon sakonnin da nai ta samu ta Imel da wayar salula da kuma bugowa ma da wasu suka yi, don neman Karin bayani.  Haka ake so daman.  Wannan na daga cikin abin da nai ta jaddada mana cikin kasidar Waiwaye Adon Tafiya, wato kwatanta abin da aka koya ko karanta, a aikace.  Da haka harkan ilimi ya ci gaba a duniya gaba daya.  Don haka duk wanda ya fara ginawa, to ya natsu ya karasa.  Wanda bai fara ba, ya fara.  Wanda kuma ya gama ginawa, ya aiko mana da adireshin don mu ziyarce shi, mu ga abin da yake tallata ma duniya a tsarin tunaninsa.  A yau za muci gaba da bayanai kan Mudawwana har wa yau, sai dai za mudan maimaita wasu gabobin bayanan da muka yi, kafin mu zarce, don na fahimci wasu na samun matsala.

397

Matashiya

 Bayan dogon bayani da muka kawo kan ma’ana da tarihi da kuma bunkasar wannan kebantacciyar hanyar sadarwa, mun nuna ma mai karatu yadda zai iya bude nasa shafin cikin sauki, ba tare da mishkila ba.  To amma saboda dabi’ar koyo ta gaji ‘yan kurakurai, wasu basu fahimci tsarin sosai ba.  Da farko dai muka ce akwai gidajen yanan sadarwa masu bayar da daman bude Mudawwana kyauta, kamar su LiveJournal (http://www.livejournal.com), Xanga.com (http://www.xanga.com), NewBlog.com (http://newblog.com), Blog.com (http://blog.com), da Blogger.com (http://www.blogger.com/start) na kamfanin Google kenan.  Kowanne tsarinsa daban. Mun kuma kawo misali ne da Blogger.com, wanda gidan yanan sadarwan Google ce ke dashi.  Muka kuma sanar da mai karatu cewa ba zai iya bude Mudawwana ba sai yana da adireshin Imel, amma in so samu ne ya zama Imel din na Gmail ne.  Idan bashi da Gmail, sai ya je http://mail.google.com.  Da zarar shafin ya budo, sai ya dubi can kasa daga hannun dama, zai ga inda aka rubuta “Sign Up for Gmail”, sai ya matsa, ya bi ka’idojin da ke tafe a fam din, don samun adireshin Imel na Gmail.  Da zarar ka samu, sai ka shigo Zauren Blogger da  ke http://www.blogger.com/start, ka shigar da suna (username) da kalmar iznin shiganka (password), ka matsa “Sign In”.  Za a kai ka shafin da za ka zabi suna da adireshin Mudawwanarka, wanda da shi za a iya shiga don karanta abin da ka zuba a ciki.  Kana gama zaba, sai ka zarce shafin gaba, inda za ka zabi irin kala da kuma tsarin da kake son Mudawwanarka ta kasance da shi.  Akwai ginannun kwarangwal (Templates) wajen goma, sai ka zabi daya daga cikinsu.  Ka gama kenan, sai kawai ka fara zuba bayanai don wasu su karanta.

Amma ka tabbata ka bayar da bayanai kan karan kanka (Biodata), don masu ziyara su san ko waye kai.  Nan gaba za mukawo bayanai kan yadda ake canza ma shafin yanayi gaba daya, zuwa irin tsarin da kake so.  Sai dai hakan na bukatar wasu yan dabaru na gina gidan yanan sadarwa.  A yanzu dai wadannan sune hanyoyin da ake bi wajen bude mudawwana.  Sai ka haddace adireshin Mudawwanarka, kuma ka san cewa duk lokacin da kake son zuba bayanai a ciki, za ka je Zauren Blogger.com ne (http://www.blogger.com/start), ka shigar da suna (username) da kalmar iznin shiganka (password).  Za ka iya shiga ma ta Mudawwanarka;  sai ka dubi can sama daga hannun dama, za ka ga inda aka rubuta “Sign In”, da ka matsa za a kai ka zauren.  Kuma a lura da cewa, adireshin Mudawwana bashi da haruffan “www”, kamar cikakkun gidajen yanan sadarwa.  Ga yanda yake zuwa http://sunan-mudawwanarka.sunan-manhajar-mudawwanar.com.  Mu kaddara ka bude da sunan “tunanin-zuci, a Blogger.com.  Ga yadda adireshin zai kasance: http://tunanin-zuci.blogspot.com.  Da fatan an gamsu.

Matambayi Ba Ya Bata

 Wani abin da masu karatu za su so ji shi ne dukkan Mudawwanan da aka gina su a yanzu (wanda sun zarce Milayan Saba’in da Biyar, kamar yadda muka sanar makon da ya gabata), su na da gidan yanan sadarwan Matambayi Ba Ya Bata (Search Engine Web Site) na musamman da ake neman su ta nan.  Idan ba a manta ba, a baya mun yi ta’arifin Matambayi Ba Ya Bata da cewa “gidan yanan sadarwa ne mai dauke da manhajar neman bayanai, wanda ke yawo rariya-rariya don cafko bayanai daga gidajen yanan sadarwan da ke giza-gizan sadarwa ta duniya, yana zubawa a runbun bayanan gidan yanansa, don amsa tambayoyin masu neman bayanai.”  Wasu daga cikin ire-iren wadannan gidajen yanan sadarwa ba boyayyu bane.  Akwai irin su Google (http://www.google.com), Yahoo (http://www.yahoo.com) da dai sauransu.  Ta la’akari da cewa Mudawwana wani kebantaccen gidan yanan sadarwa ne mai dauke da kebantaccen sakon da ya sha banban da na galibin gidajen yanan sadarwan da ke Intanet, wasu masu kwazo sun yi kokarin kirkiro masa nasa gidan yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata na kashin kansa, don ba masu sha’awan yawo ko bincike a ire-iren wadannan mudawwanai daman yin haka.  A kasidar da ta gabata, mun kawo cewa galibin bayanan da ke cikin Mudawwanan mutane duk ra’ayoyi ne na kashin kai (personal opinions), duk kuwa da cewa galibin gwamnatocin duniya na da Mudawwanai su ma, amma wannan bai banbanta kalan ra’ayin da ke ciki da na talakka iri na.

A takaice dai Mudawwana wata kafa ce da mai ita ke fitar da ra’ayinsa karara don kowa ya karanta, hakan na iya faruwa ba tare da bin ka’idojin ilimi ba wajen muhawara ko tattauna mas’ala.  Don haka masana fasahar Intanet ke shawartan duk mai son jin ra’ayin mutane tsagwaronsa, to ya shiga Mudawwanai, sai ya gaji dasu.  Wannan tasa aka samu gidajen yanan sadarwa na Matambayi Ba Ya Bata da ke taimaka ma mai yawo a giza-gizan sadarwa nemo bayanai ko nau’ukan bayanan da ke Mudawwanai.  Manya daga cikinsu su ne Technorati.com (http://www.technorati.com), da kuma Blogdigger.com (http://www.blogdigger.com).  Idan ka shiga wadannan gidajen, za ka samu gamsassun bayanai kan nau’ukan Mudawwanan da ke Intanet.  Wannan zai taimaka ma masu son budewa, idan sun kasa tsayar da hankalinsu kan abin da za su zuba cikin Mudawwanansu.  Idan suka gabatar da dan gajeren bincike ta amfani da kalmomin da ke da nasaba da abin da suke sos a Blogdigger.com ko kuma Technorati.com, za su samu waraka in Allah Ya yarda.

- Adv -

Ingancin Bayanai

 Kamar yadda bayani ya gabata a sama, Mudawwana wuri ne da ake zuba bayanai na son zuciya da ra’ayi; shin ra’ayin mai kyau ne ko akasinsa.  Abin da zai tabbatar da hakan kuwa shi ne abin da mai ziyara ke son ji.  Domin galibin bayanan da ke cikinsu ba a gina su kan tabbatattun mizanin ilimi ba.  Wannan tasa a farkon al’amari wasu ke ganin cewa idan dalibi ne kai mai neman bayanai na ilimi, to kada ka kuskura ka tattaro  bayanai daga Mudawwanai, sam sam.  To amma a yanzu al’amura sun fara canzawa.  Ana samun kasidu da makaloli masu muhimmanci da amfani da aka rubuta su cikin insafi da bin ka’idojin ilimi wajen tabbatar da hujja.  Misali, idan ka shiga Mudawwanar Farfesa Abdallah Uba Adamu da ke Jami’ar Bayero, Kano (http://arewanci.blogspot.com), za ka samu kasida da ya rubuta, doguwa mai cike da hujjoji kan batun cire rubutun Ajami da aka yi  a kudaden Nijeriya.  Wannan ke nuna cewa a yanzu akan samu bayanai ingantattu masu amfani a Mudawannai, ba kamar da ba.  Abin da mai neman bayanai zai kiyaye kawai shi ne, ka tabbata ka samu cikakken bayanai kan wuraren da marubuci ya ciro bayanai da hujjojinsa (references), ba da ka ya rubuta ba.  Kada kyale-kyale da tsarin Mudawwanansa su razana ka.  Idan ka samu wannan, ba ka bukatan daukan adireshin Mudawwanarsa don ishara.

Fadin Albarkacin Baki da Haddinsa

 Duk da yake Mudawwana wuri ne da mai shi zai zage dantse wajen fadin albarkacin bakinsa, a wasu lokuta hakan na bukatan nazari, musamman ta la’akari da yadda hankalin Gwamnatoci da kungiyoyi ya fara komawa kan su don samun ra’ayoyin masu rubuce-rubuce, musamman ma ‘yan jaridu.  Domin galibin ‘yan jaridu sun fi zagewa su fadi gaskiyar yadda abu yake ko kuma hakikanin ra’ayinsu kan wani al’amari da ya shafi kasarsu ko siyasar duniya, fiye da yadda suke yi a shafukan jaridunsu da ake bugawa kuma ake yadawa a kan titi.  Galibin ‘yan jaridun da ke lura da al’amuran da ke faruwa a kasar Iraki (wanda galibinsu Amurkawa ne ko Turawan Turai), kan mike kafa wajen fadin hakikanin abin da ke faruwa a birnin Bagadaza.  Wannan bai yi ma kasar Amurka dadi, sam! Har wa yau, galibin matasan da ke kasashen Larabawa su ma ta haka su ke baza “hakikanin” abin da ke faruwa a kasashensu (akwai Mudawwanai cikin harshen Larabci a http://www.maktoob.com) .  Wannan tasa hankalin gwamnatoci, musamman a Gabas-ta-Tsakiya, ya koma kan ire-iren wadannan Mudawannai na yan jaridu marasa-boda (Freelance Journalists). Don haka ba abin mamaki bane kaji an kama dan jarida haka kawai, saboda irin ra’ayin da ya zuba a cikin Mudawwanarsa.

Cikin watan Maris hukumar kasar Masar (Egypt) ta cafke wani saurayi da tace ya fadi wasu maganganu da a cewarta cin mutuncin addinin Musulunci ne.  Ba na tunanin an sake shi a yanzu.  Makamancin wannan ya sha faruwa a kasashe da dama.  Wannan ke nuna ma mai karatu cewa yancin fadin albarkacin baki na da iyaka, musamman a kasashen da ke ganin sun ci gaba wajen yanci da ilimi, a farkon al’amari.  Don haka, sai a yi taka-tsantsan da abin da za a zuba cikin Mudawwana, duk da yake mu ba mu fara samun irin wannan karan tsayen ba a kasashenmu.

Kammalawa

 A nan za mu dakata, sai wani mako.  Duk kuma wanda ya bude Mudawwanarsa sai ya aiko mana da adireshin don mu sanar da sauran masu karatu, su leka su ga abin da ya rubuta ko yake tsarawa.  Ni ma na bude nawa Mudawwanar na kashin kai na, za a kuma same ta a http://babansadiq.blogspot.com.  Har wa yau, da zarar na gama rubuta littafin Intanet da nake kai, zan zuba shi dungurun cikin Mudawwana ta musamman da na bude don masu son karantawa su karanta; Babi Babi.  Daga karshe, kada a mance a shigo Mudawwanar Fasahar-Intanet in da za a samu dukkan kasidun da aka buga a wannan shafi.  Mudawwanar na http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Dubun gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan Media Trust masu buga AMINIYA, musamman Hajiya Aishah Umar Yusuf, da kuma Malam Abubakar AbdurRahman.  Sai mun sadu mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
3 Comments
  1. Hamisu says

    Slm

  2. Kamal Ahmad says

    Assalamu Alaikum Baban Sadik ga na wa blog dina ya zanyi na samu free domain,ya kuma zan shiga tsarin google adsense

  3. Kamal Ahmad says

    Salam Baban sadik ga blog dina http://nabeelblogspot.blogspot.com.ng

Leave A Reply

Your email address will not be published.