Facebook Gidan Rudu: Kowa “Admin” Ne

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

214

Kowa “Admin” Ne

Idan aka ce “Admin,” ana nufin jagora ko madugun wani zaure a shafin Intanet, a wannan ta’arifin kenan.  Ma’ana wanda ya bude wani zaure don tara jama’a da tattaunawa kan al’amuran rayuwa da hanyoyin ci gaba. Wannan matsayi ne mai girman gaske a fannin Intanet da hanyar sadarwar zamani.  Duk wanda zai zama “Admin” to, dole ya zama kwararre ne, masani kan maudu’i, kuma mai iya warware matsaloli da sabanin dake shiga tsakanin mutanen da ya tara a zaurensa, ko ince: Group, idan Facebook ne.

Daga cikin rudu dake cikin Facebook shi ne, kowa ya zama Admin yanzu.  Da zarar mutum ya bude shafi a facebook, ya ga yana da abokai da yawa, sai kawai ya bude Group, yasa masa suna mai ban sha’awa.  Yayi ta jajibo mutane yana shigar dasu karfi da yaji; ba tare da neman izininsu ba.  Kashi 70 cikin 100 na Groups dake Facebook na mutanenmu (Hausawa), duk an shigar ko ana shigar da mambobin ne ba tare da neman izininsu ba.  Wannan ke sa a shigar da mutane, musamman mata, cikin zaurukan batsa ba da saninsu ba.  Sau tari idan na duba Profile di na, sai in ganni a cikin zaurukan da ban taba sanin sadda na shige su ba (kuma ba ni na shiga ba), marasa ma’ana, wadanda basu dace da dandanona na karatu ko mahangar rayuwa ba.  Galibin mata dake Facebook ana shigar dasu Groups ne ba tare da saninsu ba.  Wannan kuskure ne mai girman gaske.

Maudu’in da ake baiwa Group din a karshe yakan zama suna ne kawai, don jawo hankalin masu shiga.  Amma hakikanin abin da ake yi a Group din na shirme da shashanci da rashin alkibla shi yafi yawa.  Za ka ga Group da suna: ZAUREN GYARAN WAYOYIN SALULA misali, amma da zarar ka shiga sai ka ga in ban da shirme da bayanin yadda ake satar “Data” daga kamfanonin waya ba abin da ake yi a ciki.  Ko kaga Group da sunan wani malami na addini, amma in ban da zantukan siyasa ba abin da ake yi a ciki. Ko ka ga Group da kyakkyawan suna, amma in ban da hira mara alkibla ko na siyasa ko kungiyancin addini dake raba kan mutane ba, ba abin da ake yi a ciki.

- Adv -

Zaurukan da suka fi kowanne nishadi su ne na iyayenmu mata.  Kasancewar mata sun fi mu zumunci, za ka ga zaurukansu a cike, ana ta hira abin ban sha’awa. Sai dai babbar matsalar zaurukan mata kuma shi ne yawan gulmace-gulmace (a min gafara iyayena mata), da soki burutsu.  A wasu lokuta kuma sai a wuce gona da iri, ko dai ayi ta tallace-tallace a cikinsu ko zantukan batsa, ko duk biyun – kamar yadda wannan dabi’ar dan adam ce.   Galibin Groups na mazaje kuma za ka samu mahada ce kawai. Inda ake kawalanci, da hada mai nema da wadda ake nema, da sauran bukatun shashanci.  A takaice dai, kamar office ne na neman mata da mata ko maza da maza ko mata da maza.  Kun dai fahimci zancen.

Mafi girman rudu shi ne har yanzu ana ta bude Group kan abubuwa da dama, alhalin akwai da yawa da aka bude su wadanda ba a komai a ciki.  Ko dai saboda Admin din ya gaza don rashin hikima da ilimin tafiyar da zauren, ko don rashin wadanda za su agaza masa, ko don daman ya bude ne don yayi.  Da zarar zamani ya wuce shikenan.

Darasi:

  1. Kada ka bude Group idan ka san ba za ka iya tafiyar dashi ba sanadiyyar karancin ilimi ko kwarewa wajen iya mu’amala da jama’a;
  2. Kada ka bude Group don yayi; don kawai ana harkar zabe ko siyasa (kuma kai ba dan siyasa bane);
  3. Kada ka shigar da mutane kai tsaye ko da abokananka ne, cikin Group ba tare da neman izininsu ba. Akwai hanyar shigar da mutane Group guda biyu; ko dai ka gayyaci mutum (Invite) ko ka shigar dashi kai tsaye (Add).  Dole sai da izini ake shigar da mutum Group;
  4. Yana da kyau a duk mako ko yini ka rika duba profile dinka, bangaren Group. A nan ne za ka rika ganin nau’ukan zaurukan da kake ciki. Duk sadda na ga an shigar dani Group ba tare da izinina ba, kuma ba abu bane da nake da dandano a cikinsa na ilimi, nan take nake ficewa kuma in kulle hanyar sake shigar dani;
  5. Ka sani, nau’ukan Group da kake ciki ne ke bayyana hakikaninka. Idan Groups ne na kirki a dauke ka mutumin kirki, idan na banza ne ma haka za a dauke ka.  Ba ruwan mutane da cewa an shigar da kai ne ba tare da izini ba.  Me ya hana ka ficewa daga ciki, ko bincike don kokarin ficewa daga ciki?

Jama’a, mu fadaka!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.