Sakonnin Masu Karatu (2017) (26)

Ci gaban sakonnin masu karatu. Da fatan za a rika rubuto adireshi da cikakken suna, bayan tambaya.

71

Assalamu Alaikum. Da fatan kana lafiya, Baban Sadik don Allah ka taimaka min da dabaran yadda zan iya hawa profile dina na N-Power. Kuma sai da waya kirar Android ne kadai ake iya shiga Profile din ko duk Smart Phone mai browser? Ka taimaka min. Nagode. Maman Abdulsamad Gombe

Wa alaikumus salam, barka dai Maman AbdusSamad.  Dangane da yadda ake hawa shafin N-Power, duk wayar da ake iya hawa Intanet da ita ana iya isa ga shafinsu, ba dole sai nau’in Android kadai ba.  Abin da ke da mahimmanci kadai shi ne, ya zama an samu cikakken adireshin shafin da ake son hawa.  Wannan ita ce ka’ida.  Da fatan kin gamsu, kuma Allah ya taimaka, amin.


Assalamu alaikum da fatan Baban Sadik yana lafiya.  Sunana Ismail Salisu, dalibin Computer Science.  Ina aji 3 a jami’ar Umar Musa ‘Yar Adua University dake katsina.  Ina godiya gareka musamman bisa kokarin da kakeyi na ilmantarwa.  Ina da sha’awar fannin Networking da Telecoms (rubuce-rubucenka sun kara zaburar dani da sa mani sha’awa na wannan fage mai fadi), kuma yanzu haka ina fuskantar horaswa na SIWES ko IT.  Shi ne nake neman shawararka: ina ya kamata naje domin samun horaswa na aiki sosai?  Na gode: (salisudauraismail@gmail.com) bissalam

Wa alaikumus salam, Malam Ismail.  Na yi farin cikin jin cewa kana samun gamsuwa cikin abin da kake karantawa a wannan shafi mai albarka a duk jumu’a.  Dangane da batun tsarin horaswa na SIWES ko IT, kawai ka nemi hukumar da ka san suna da amfani da tsare-tsare da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani, don yin wannan aiki a tare da ita.  Wannan shi ne zai taimaka maka wajen ganin yadda ake tafiyar da na’urorin sadarwa na zamani cikin sauki, kuma a aikace.  Amma idan hukuma ko kamfani ko ma’aikatar da kaje ba su da wadannan na’urori (irin su Kwamfuta da sauransu), to, sai dai ka ta zama kawai kuna kallon juna kai da sauran ma’aikatan dake wurin.

In so samu ne, ka samu kamfanin ko hukuma ko ma’aikatar da ke aiwatar da aikin a aikace.  Irin su gidajen talabijin, ko jaridu, ko kafafen yada labarai na rediyo na gwamnati ko masu zaman kansu.  Hakan idan hukumar gwamnati ce, ya zama suna da wadannan kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani.  Samuwan wadannan kayayyaki ne zai taimaka maka wajen ganin aikin a aikace, musamman ma a fagen hada alaka tsakanin kwamfutoci, wato: “Networking.”  Duk kamfani ko hukuma ko ofishin da ke da kwamfutoci da ake aiki dasu, kuma suke hade da juna, to, kana da aikin yi a wurin.

Wanann shi ne dan abin da zan iya baka na shawarwari a halin yanzu.  Ina kuma maka fatan alheri a duk inda za ka samu kanka.  Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Baban Sadik, Allah yasa kana nan lafiya tare da iyalanka amin.  Don Allah Baban Sadik ina son kayi mini bayanin yadda zanyi in bude shafin Twitter a waya ta. Wassalam ka huta lafiya, nine: 08056526803

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Bayani kan yadda ake budewa ko yin rajistan shafin Twitter ba wani abu bane mai tsayi.  Ka garzawa shafin Twitter dake: http://www.twitter.com, sai ka matsa alama mai take: “Sign Up” dake can sama daga kuryar dama.  Kana matsawa za a budo maka shafin dake dauke da fom din da ake son ka cike, kafin a maka rajista.  A yayin da kake cike fom din ne za ka zabi suna (username) da kalmar sirrin (password) da za ka rika amfani dasu wajen hawa shafin a duk sadda ka tashi hawa. 

Bayan haka, idan kana da waya mai dauke da babbar manhajar Android ko Windows Phone ko iOS na kamfanin Apple, kana iya zarcewa cibiyar manhajojin wayar (“Play Store” a Android, ko “Store” a Windows Phone, ko kuma “App Store” a wayar iPhone), don saukar da manhajar Twitter, wadda za ta sawwake maka isa ga shafin a duk sadda ka tashi bukata.

Wannan shi ne takaitaccen bayani kan yadda za ka iya mallakar shafi a manhajar Twitter.  Da fatan ka gamsu, kuma ina maka fatan alheri.  Na gode.


Salam a cikin wata kasidarka da na karanta a baya, na ga ka rubuta cewa duk kwakwalenmu iri daya ne.  Sai dai kuma ni na kasa samun natsuwa da hakan domin kuwa kai da kanka ka san cewa akwai ire-irenku (gifted) akwai kuma ire-irenmu (ordinary).  Bayan haka, don Allah ina so in san tarihi na hakikanin abin da ya faru a yakin duniya na 1 da na 2. Wasu kasashe ne suka fafata kuma mene ne sila?  Afuwan na manta. Sunana: Junaidu Sokoto: 09035907765

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Junaidu.  Dangane da bayanin da nayi cewa duk kwakwalenmu iri daya ne, ina kokarin tabbatar da cewa babu wani bambanci tsakanin kwakwalwarmu da na turawa da suke ta kirkirar abubuwa masu ban sha’awa da ban mamaki a fagen sadarwa.  Ma’ana, wani abu ne da Allah ya baiwa kowane jinsin dan Adam, ba wai turawa kadai aka kebe da wannan baiwa ba.  Idan muka dage, tare da samun yanayi irin wadanda suka samu kansu a ciki, da tsari irin wanda kasashensu suke ciki, muna iya kera abin da yafi wannan ma.  Wadannan su ne bambance-bambancen dake tsakaninmu dasu.  Don haka mu daina ganin cewa mu ba kowa bane, turawa ne kadai masu hazaka ko kokari. 

Wani abin sha’awa ma shi ne, galibin kamfanonin waya na duniya suna da ma’aikata bakaken fata musamman ‘yan Najeriya da sauran kasashen Afirka.  Kuma da yawa cikin abubuwan da muke gani a wayoyin salularmu, kusan su suke kirkirarsu.  Wannan ke nuna ashe dama ce kawai bamu samu ba.

A daya bangaren kuma, bayani kan Yakin Duniya na daya da na biyu (First and Second World War), ba ya cikin maudu’in wannan shafi nawa, kuma a gaskiya ba ni da wani girkakken masaniya a kai.  Wanann shafi, kamar yadda ka fi kowa sani, ya mayar da hankalinsa ne ga bincike kan Kimiyya da Kere-kere. 

A karshe, ina fata ba za ka yi hakurin rashin samun amsar tambayarka kan wannan maudu’i.  Allah sa mu dace, ya kuma kara mana ilimi da fahimta, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.