Gaskiya da Gaskiya (12): Idan Bera da Sata…(2)

Wajibi ne kowane dan Najeriya ya gyara halinsa, wajen kasuwanci ko mu’amalarsa da sauran jama’a, muddin muna son gamawa lafiya.

181

Dabi’armu ce a Najeriya mu ta aibanta shugabanni kan zalunci, da sama-da-fadi, da son kai ko son danginsu ko kabilarsu, da rashin adalci a tsakaninmu talakawansu, da dai sauran matsaloli.  A bangare daya wannan haka yake.

Duk wanda ya san Najeriya ko ba dan Najeriya bane ya san da matsala. Cin hanci da rashawa sun mana katutu ta kowane bangare.  Tsarin shugabanci a jirkice yake saboda son rai.  Wanda talakawa suke so ba shi ake tsayarwa ba, ko bashi mulki.  Idan aka samu mulkin, abin da aka ga dama shi ake aikatawa.  Kudaden da ake rabawa tsakanin hukumar tarayya da sauran jihohi da kananan hukumomi ba wanda ke ganin aiki a kasa, sai ‘yan kadan.  A yau fa an wayi gari a Najeriya; shugaba ko gwamna ko ciyaman na karamar hukuma dake yin aiki tare da sace kudi, shi ne abin yabo yanzu.  Domin galibi sai dai su sace kudaden, ba aiki.  Akwai gwamna na wata jiha a lokacin Obasanjo da aka bashi kaso na musamman da ake baiwa jihohi masu matsalar zaizayar kasa a kudancin Najeriya, labaru sun tabbatar da cewa, bikin tuna ranar haihuwarsa yayi da kudin baki daya. Tirkashi!

Galibin kudaden da ake sacewa duk ta hanyar kwangila ne da alfarmar karya da WASU shugabanni ke yi wa abokansu, ko kansu, ko danginsu, ko karuwansu, ko duk wanda ya samu hanya ta sanadiyyar wadannan.  Makarantu babu mahallin karatu mawadaci.  Tituna sunyi karanci.  Wadanda ake dasu sun lalace, face ‘yan kadan.  Asibitoci babu ingantattun kayayyakin aiki.  ‘Yan kadan da ake dasu, wasu masu uwa a gindin murhu sun kwashe!  Takin zamani sai wane da wane.  Adalci a kotuna kuma wannan sai Allah, wai Dan daudu a kabari!  Wadannan kadan ne cikin kadan na korafe-korafen talakwa kan shugabanni a Najeriya.

- Adv -

To amma, wai su shugabannin namu da muke korafi kansu, daga ina suke?  Aljanu ne su?  Ko allanmisiru ne?  Mutane ne kamarmu, daga cikinmu, ‘yan uwanmu, masu kamanni irin namu,  da suka taso a tsakaninmu.  In kuwa haka ne, meye marabinmu da su?  Jama’a, mu sake nazari!

Watarana, Abdulmalik bn Marwan, daya daga cikin sarakunan musulunci daga cikin kabilar Banu Umayya ya ji jama’a, musamman malamai da wasu cikin manyan gari suna ta korafi kan yadda yake tafiyar da mulkinsa.   Cewa akwai zalunci, akwai sama-da-fadi, akwai kashe-kashe da dai sauransu.  Nan take ya tara su.  Bayan su taru, sai yace musu: “Ina jin duk korafin da kuke yi a kaina ko tsarin mulkina.  Tambayar da zan muku ita ce:  kuna son in zama irin su Abubakar da Umar?”  Nan take kowa yace: “Eh, tabbas muna so.”  Sai yace musu:  “To, ku ma ku zama irin mutanen da suka kasance karkashin su Abubakar da Umar.”

Jama’a, mu hadu a kashi na uku!

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.