Kowa Ya Debo Da Zafi: Labarin Pablo Escobar (4)

Na rubuta wannan labari ne a shafina na Facebook, a shekarar 2016.

366
  1. Nan take Pablo ya sayi wani katafaren fili a saman tsaunin dake kallon birnin Medellin, yasa aka gina gari guda, bazan ce gida ba. Ga wasu daga cikin hotunan ginin nan da harabarsa daga hoto na 1 zuwa na 4, wanda suna cikin jerin hotunan da shahararren Dan Jarida Tom Griggs ya dauko, bayan faruwan lamarin gaba daya.  A cikin wannan gida akwai filin wasannin motsa-jiki, da gidan rawa, da mashaya, da gidan tambola (casino), da coci, da kuma ofishinsa, don ci gaba da gudanar da kasuwancinsa.  A bangaren sadarwa kuma akwai wayoyin salula, da cibiyar na’urar sadarwa, da na’urar aika sakonni mai suna Fax, da sauran kayan alatu na jin dadi.  Ana kiran wannan kurkukun da suna: “La Cathedaral.”  Wasu kuma kan kira wurin da suna “Hotel Escobar”, duk dai abu daya ne.  Bayan an gama gina wannan wuri da kayatar dashi, sai Pablo ya tare a ciki a ranar 19 ga watan Yuni, inda ya diro gidan daga jirginsa mai Saukar Ungulu (Helicopter).  A wannan rana ce ya fara zaman kaso, kamar yadda aka tsara.

 

  1. A yayin zamansa a wannan wuri, duk wanda yake son gani, zai iya gani. Akwai na’urar hangen nesa mai suna “Telescope” ya girke.  A duk sadda yake son yin waya da ‘yarsa, bayan ya kira ta dauka, yana ganinta kai tsaye daga wannan na’ura ta hangen nesa.  Hoto na 5 na dauke ne da iyalansa, na 6 kuma babban dansa ne, wanda ya girma yanzu, haka ma na 7, na yarsa ce mai suna: Manuela.  Bayan haka, abokan kasuwancinsa na iya ziyartarsa. Haka ma karuwansa, da shahararrun ‘yan kwallo, da duk wani mutum na musamman da ya amince ya shigo, ana iya barinsa ya shigo.  A haka yaci gaba da holewarsa, abin sai wanda ya gani.  Kusan kullum biki ake a wurin.  Ana cikin haka watarana sai rikici ya barke tsakanin wasu yaransa kan batun kudi, nan take yasa aka harbe hudu daga cikinsu har lahira.  Babbar magana!  Wannan ya ta da hankalin hukuma, har ta yanke shawarar dauke shi daga wurin gaba daya zuwa kurkukun sojoji a bariki (Military Prison).  Aka aiko shugaban hukumar fursunar kasar, da karamin ministan shari’a da wasu jami’an gwamnati, da sojoji matsara da suka rako su.  Amma su a waje suka tsaya.  Shigowarsu ke da wuya aka sanar dashi cewa hukuma ta canza shawara, ana son a canza masa mahalli saboda tsaron lafiyarsa.  A nan fa yace bai san zancen ba.  Mai gadinsa, wanda aka fi sani da: Popeye, ya fara zungurar karamin minista da gindin bindiga.  Sai aka ji karar fashewar wani abu kamar bam daga waje, habawa!  Kafa me naci ban baki ba, sai Pablo ya arce ta kofar baya shi da wasu yaransa.  Zamansa wurin gaba daya bai wuce shekara guda da watanni ba. Wasu ma suka ce bai wuce watanni 9 ba.  Labari ya koma sabo.  Pablo ya gudu daga gidan kaso.

 

  1. Da hukumar kasar ta ga abin ya zama gero ba dawa ba, sai ta nemi agajin gwamnatin Amurka, aka hada tawaga ta jami’an tsaro don nemo Pablo ruwa a jallo, a raye ko a mace, don kowa ma ya huta. Nan aka nada jami’an tsaro 600 ‘yan asalin kasar Kolombiya, suka hadu da tawagar hukumar tsaro na musamman na kasar Amurka mai suna “Delta Force”.  An sa wa wannan tawaga suna: “Search Bloc.”  Nan take su ma yan bangaren Los Pepes suka ce da mu za ayi.  Aka dunguma, duk a kan Pablo Escobar.  Hukuma tace duk wanda ya kamo shi za a bashi Dala Miliyan Shida ($6,000,000.00).  Watanni 17 da kaddamar da wannan zuga ta manema, sai aka gano shi a wani karamin Otal dake birnin Medellin.  Me ya faru?  Wannan zuga ta manema ta yi amfani ne da wata fasahar sadarwa mai suna: “Radio Triangulation,” wanda tsari ne dake iya killace murya/sauti, ko wani abin da ake nema, cikin kusurwa uku, ta yadda hakan zai ba da damar dirkake shi.  Sadda Pablo ke boye, babban yayansa Robert, ya samu labarin cewa za ai amfani da wannan fasaha don gano inda Pablo yake, nan take, kamar yadda ya fada cikin littafinsa mai suna: “The Accountant Story,” ya rubuta wa Pablo wasika cewa, idan an kira shi ta waya, kada ya sanya wayar a tsarin “Speakerphone,” don za a kashe shi.  Amma ina, Pablo bai ga wasikar bane, ko dai kaddara ce, wallaahu a’alam.  Ya kira dansa suna hira, sai aka gano muryar, da bigiren da muryar take.  Nan take aka killace unguwar, har aka zo kan Otal din, aka haura; ana bi daki-daki.  Da matsaransa suka fahimci an gano su, suka bude wuta, aka mai do musu.  Pablo ya arce ta saman rufin ginin, amma ina, kafin yayi nisa aka harbe shi, ya fadi kasa.  An kashe Pablo ne a ranar 2 ga watan Disamba, shekarar 1993.  Shekarunsa 46.  Ga hotonsa nan a hoto na 8.

 

- Adv -

  1. An samu Pablo da raunukan harbi daga kafansa har zuwa kunnensa. Duk ana ganin harbin jami’an tsaro ne da suka masa.  Amma babban yayansa Robert yace, shi dai yana ganin Pablo ne ya kashe kansa.  Domin ya taba jinsa yana gaya wa wasu abokansa, cewa, a duk sadda aka darkake shi a wurin da ba zai iya tsira ba, zai harbi kansa da bindiga a kunne.  Wannan shi ne karshen Pablo Escobar, wanda har zuwa yau, kasar Kolombiya, da ma duniya baki daya, ba a samu dan ta’adda irinsa ba.  To, kamar yadda kowa ya sani ne, duk wani abu dake duniyar nan yana da farko kuma yana karshe.  Duk da tsawon lokacin da yayi yana ta’adi, a karshe dai ajali ya zo.  Sai dai ta mummunar hanya, da mummunar sakamako.  A yayin da babban Malami Abu Zakariyya, Yahya bin Sharaf, An-nawawi ya kashe shekaru 46 yana rubutu daa karantar da ilimin addini, wanda har yanzu ana amfana, a nasa bangaren, Pablo Escobar ya kashe shekaru 46 ne yana ta’adi, irin ta’adin da ya bar baya da kura a duniyar yau, musamman a kasar Amurka.  A yayin da An-Nawawi ya zama sanadin wasu su zama manyan malamai sanadiyyar rubuce-rubucensa, Pablo Escobar ya zama sanadin haukar da yawa cikin Amurkawa ne, da ‘yan kasar Kanada, da Spain, da Kolombiya, kar har da wasu dake uwa Najeriya.  A karshe dai PABLO YA DEBO DA ZAFI, amma tafasasshiyar ruwan dalmar da ya debo bata tsaya a bakinsa kadai ba.

Ya Allah kai mana kariya daga fadawa halaka, amin.

 

BABAN SADIK

05.02.2016 – 08:21pm

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.