Matsaloli da Hanyoyin Inganta Tsarin “Cashless” A Najeriya (2)

Dole ne bankunan kasuwanci su ƙara inganta tsarin sadarwa wajen aikawa da karɓan kuɗaɗe, tare da inganta manhajoji da tsare-tsaren da suke amfani dasu wajen bai wa mutane damar aikawa da karɓan kuɗaɗe cikin sauƙi.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 12 ga watan Mayu, 2023.

295

Tarnaƙi Daga Bankuna Da Masu POS

Mafi girma da munin matsaloli ko cikas da tsarin “Cashless” ke fuskanta yanzu, sanadiyyar canjin fasalin takardun kuɗi da bankin CBN yayi, shi ne samun tarnaƙi daga bankunan kasuwanci da kuma dillalansu masu na’urar POS, wato “Super Agents”, kamar yadda bayani ya gabata a baya.

A yayin da ya kamata ace sauyin takardun kuɗi ya zo ne a tsarin zango zango, a hankali a ɗauke kuɗaɗen da aka canja tare da maye gurbinsu da sababbi, sai ya zama gaggawan da bankin CBN yayi ya haddasa wata matsala kuma; ita ce ƙarancin takardun kudi, wanda duk da cewa babu yalwan sababbin takardun kuɗi kamar yadda bankin CBN ya sanar, sai dai kuma bayanai sun nuna cewa jami’an bankunan kasuwanci sun ci karensu ba babbaka wajen ɓoye ɗan kaɗan ɗin ma da aka aiko musu, tare da sayar dasu ta bayan fage ga wasu tsirarun ‘yan Najeriya masu zuwa su sayar don cin ƙazamin riba.  Haka masu na’urar POS su ma sunyi amfani da wannan gajeren lokaci na ƙarancin takardun kuɗi don azurta kansu ta hanyar ƙuntata wa mutane.  A tare da cewa wannan matsala ta fara raguwa a manyan birane, sai dai a wasu ƙauyuka har yanzu ana fama da ƙarancin takardun kuɗi, kuma babu masu samun sauƙi sai waɗanda suke da wadatar saya a farashin da ake sayarwa a kasuwar bayan fage, maimakon canzawa.

Waɗannan, a takaice, su ne manyan tarnaƙi da wannan tsari na
“Cashless” ke fuskanta a halin yanzu.  To, mece ce mafita?  Bayanin hakan na cikin sashen dake tafe.

Hanyoyin Inganta Tsarin “Cashless”

Daga yadda aka ɗauko wannan tsari, ga dukkan alamu akwai fa’idoji da yawa da suka fara game tsarin tattalin arziƙi, kamar yadda masana suka tabbatar.  Sai dai samun ingantaccen tsari zai samu ne idan bankin CBN, da Gwamnatin Tarayya da na Jihohi da kuma sauran masu ruwa da tsaki cikin tsarin hada-hadar kuɗaɗe suka kawo ƙarshen matsalolin da muka zayyana a makon jiya zuwa yau.  Hanyoyin da za a bi kuwa sun haɗa da:

Inganta Yanayin Sadarwar Bankuna:  Dole ne bankunan kasuwanci su ƙara inganta tsarin sadarwa wajen aikawa da karɓan kuɗaɗe, tare da inganta manhajoji da tsare-tsaren da suke amfani dasu wajen bai wa mutane damar aikawa da karɓan kuɗaɗe cikin sauƙi.  Sannan su ƙara taƙaita tsawon lokacin da suke ɗaukawa wajen warware matsalolin dake fuskantar mutane musamman idan ya shafi maƙalewar kuɗaɗe wajen aikasu.  Su sani fa, tsarin banki yana ta’allaƙa ne da aminci da amintuwa.  Idan mutane suka daina amintuwa da yadda bankuna ke tafiyar da ayyukansu, da yawa cikinsu ba za su ci gaba da ma’amala dasu ba.  Za a koma ‘yar gidan jiya.

- Adv -

Wayar Da Kan Jama’a:  iya gwargwadon yadda jama’a suka fahimci wannan tsari na “Cashless”, iya gwargwadon yadda za su aminta dashi.  Don haka, wajibi ne hukumomi da kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe su ƙara himmatuwa wajen wayar da kan jama’a kan haka, musamman ta kafafen sadarwa na zamani da na rediyo da talabijin, cikin harsunansu da salon da za su iya fahimta cikin sauƙi.

Tabbas bankin CBN yana ƙoƙari wajen samar da dokokin da suka taimaka wajen sawwaƙe hanyoyin ta’ammali da tsarin banki da hada-hadar kuɗi da dama.  Sai dai da yawa cikin mutane basu san waɗannan hanyoyi ba.  A galibin ƙauyuka wasu basu san ma ko ta hanyar wayar salula za ka iya buɗe taskar ajiyar banki ba. A tare da cewa, ƙarƙashin waɗannan tsare-tsare da bankin CBN ya samar, an samu yaɗuwar bankunan Intanet da yawa da za ka iya buɗe taskar ajiya dasu ba tare da ka je ofishinsu ba, don haka tsarinsu yake.  Shahararru cikinsu sun haɗa da OPay, da Kuda Bank, da Palmpay da dai sauransu.

Inganta Wutar Lantarki:  inganta wutar lantarki zai taimaka matuƙa wajen rage cajin da bankuna ke yi don aikawa ko karɓan kuɗaɗe ta hanyar tsare-tsarensu.  Haka ma masu na’urar POS.  Sannan zai taimaka wajen ingantuwan yanayin sadarwar bankuna tare da rage kuɗaɗen da suke kashewa wajen tafiyar da dukkan wani tsari dake da alaƙa da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani.

Yawaita Bankuna da Na’urar ATMs a Ƙauyuka:  duk da cewa a galibin ƙasashen da suka ci gaba bankuna na rage yawan rassansu ne don ƙara inganta tsarin hada-hadar kuɗaɗe ta amfani da hanyoyi da na’urorin sadarwa na zamani, irin su Intanet, da Manhajar wayar salula da na’urar ATMs da kuma na’urar POS, iya gwargwadon yadda doka ta tanadar.  Sai dai kuma, mu a nan akwai ƙarancin gamewar waɗannan tsare-tsare a mafi yawancin ƙauyukanmu.

Don haka, ya kamata bankuna su ƙara buɗe rassa a ƙauyukan jihohin ƙasar nan, tare da samar da tsaro ta ɓangaren hukumomin gwamnati.  A jihohin arewa maso gabashin ƙasar nan akwai jihar da babu bankuna ma a wasu ƙananan hukumominta.  Musamman jihohin Yobe, da Barno, da wani ɓangaren jihar Jigawa.  A jihar Kaduna misali, akwai ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ba ta da banki ko ɗaya, sanadiyyar matsalar tsaro da ta addabi yankin.  Idan rassan bankuna ba za su samu a wasu wuraren ba, a samar da dillalan bankuna, wato masu POS kenan.  Wannan zai taimaka matuƙa wajen ƙara shigar da da dama cikin ‘yan Najeriya tsarin banki.

Kammalawa

A ƙarshe, dole ne a jinjina wa bankin CBN wajen samar da yanayin da ya dace tun shekarar 2012 don aiwatar da tsarin “Cashless”.  Duk da cewa an samu kuskure mai kama da ganganci wajen sauya fasalin takardun kuɗi, wanda hakan ya haifar da tsaiko da ƙunci na taƙaitaccen lokaci ga ‘yan Najeriya, sai dai fa’idan hakan a shekaru masu zuwa zai taimaka wajen samar da ci gaba a tsarin hada-hadar kuɗi a ƙasarmu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.