Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (12)

Ɓangarorin Kyamarar Wayar Salula

Fahimtar waɗannan ɓangarori zai taimaka wa mai karatu musamman kan yadda ake wayar salula ko kyamarar zamani (DSLR) ke ɗaukan hotuna abubuwan dake mahalli. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 20 ga watan Oktoba, 2023.

184

Ɓangarorin Kyamarar Wayar Salula

Kyamarar wayar salula – da kowace irin na’urar ɗaukan hoto da bidiyo na zamani – na ɗauke ne da manyan ɓangarori guda uku, kamar yadda na fara sanar da mai karatu a makon jiya.  Waɗannan ɓangarori dai suna tare ne a wuri ɗaya, duk da cewa a matakin ɗaukan hoto na ƙarshe, suna haɗin gwiwa da ƙwaƙwalwar ɗan adam wajen samar da abin da a ƙarshe za a iya kira da suna hoto; a zahiri ne ko a kan wayar salula ko na’urar ɗaukan hoton.  Fahimtar waɗannan ɓangarori zai taimaka wa mai karatu musamman kan yadda ake wayar salula ko kyamarar zamani (DSLR) ke ɗaukan hotuna abubuwan dake mahalli. Kuma kamar yadda a baya na sanar har wa yau, kyamarar ɗaukan hoto ko bidiyo na amfani da haske ne, wanda ke ɗauke da launin fari da baƙi, don rairayo surar abin da ake son ɗaukan hoto ko bidiyo ɗinsa.  Ko da kuwa hoton mai launi ne, asalin launukan da kyamara ke gani guda biyu ne; fari (white) da baƙi (black).   A halin yanzu dai ga bayani kan kowane ɓangare nan a taƙaice.

Tabarau (Lens)

Wannan ɓangare da na kira da suna tabarau ba wani abu bane face na’urar dake cafkowa da kuma sarrafa haske don samar da hoto.  A ɓanagren ɗan adam, shi ne ƙwayar idon da muke gani dashi.  A ɓangaren wayar salula kuma, shi ne wannan ɗan ƙwayan ido baƙi dake maƙale a bayan wayar salula da muke kira da suna kyamara.  A ɓangaren kyamarar zamani kuma, wato DSLR, shi ne wannan dogon na’urar da ake maƙala wa kyamarar daga gaba, wanda ake jujjuya shi a wasu lokuta, kafin ɗaukan hoto.  Shi ne abin da yafi komai daraja da matsayi a jikin kyamara.  Domin idan babu shi, to, babu  ɗaukan hoto gaba ɗaya.  Ba ma wannan kaɗai ba, ko abin da kake son ɗauka ma ba za ka iya ganinsa ba, idan babu tabarau a jikin kyamara.

Aikinsa shi ne haddade maka iya abin da za ka iya ɗauka, ta hanyar ganin abin idan ka kalla.  Sannan shi ne ɗauke da na’urar dake janyo hasken dake mahalli don baka damar ganin surar abin da kake son ɗauka.  Shi ne, har wa yau, ke iya tantance maka launukan abin da kake son ɗauka ko kake hangowa a cikinsa.  Shi ne har wa yau ke ɗauke da kafar da haske ke shiga.  Wannan kafa, kamar yadda na ambata a makon jiya, ita ake kira: Aperture.  Kuma wannan tabarau ne ke buɗe wannan kafa cikin ƙiftawa da bisimilla, don bai wa haske daman shiga, sannan ya rufe kafar.  Ba dukkan hasken dake mahalli ne yake ɗauka ba.  samfuri kawai yake yi na haske, don samun damar sawwara abin da ya hanga a mahalli.  Tazarar dake samuwa tsakanin buɗewa da rufe wannan kafa na shigan haske, shi ake kira Shutter speed a harshen turancin fasahar sadarwa.

- Adv -

Na’urar Janyo Haske (Lens Sensor)

Ɓangare na biyu shi ne na’urar janyo haske.  Tabarau ɗin kyamara na ɗauke ne da na’urar dake janyo haske don bashi damar sawwara hoton abin da ya gano a mahalli.  Kamar yadda mai karatu ya gani a makon shekaranjiya, Sensor dai na’ura ce dake iya tantance yanayin mahalli, ta hanyar “hankalta” ko “lura” da abin dake mahallin da wayar salular take.  A baya muka ce akwai nau’ukan na’urori irin wannan guda biyar a wayoyin salula ta zamani, masu baiwa manhajojin wayar daman aiwatar da ayyukansu, ta hanyar hankaltar yanayin da wayar take.  Daga ciki muka ce akwai na’urar dake iya tantance ƙarfin haske ko rauninsa a mahallin da waya take.  Wannan ita ake kira: Ambient Light Sensor.

To, irin wannan na’ura ce aka tsofa a cikin tabarau ɗin wayar salula.  Shi yasa ake kiranta da suna: Lens Sensor.  Daga sadda ka buɗe manhajar ɗaukan hoto a wayarka, nan take wannan tabarau za ta buɗe, garau.  Tana buɗewa sai wannan na’ura ta hankalci hasken dake mahallin, ta jawo shi zuwa cikin tabarau ɗin kyamarar.  Hasken na shigowa ta wannan kafa mai suna Aperture, sai tabarau ɗin ya gutsiri iya yawan hasken da yake buƙata, sannan ya rufe kafar, don sarrafa abin da ya ɗarsano zuwa sura ko hoton abin.  Dukkan wannan na faruwa ne cikin ƙasa da daƙiƙa ɗaya daga sadda ka danna maɓallin ɗaukan hoton.

Na’urar Sarrafa Hoto (Image Processor)

Wannan shi ne ɓangaren ƙarshe na kowace irin kyamara.  Daga sadda ka danna maɓallin ɗaukan hoto, haske ya shige cikin tabarau, abu na gaba shi ne sarrafa wannan haske mai ɗauke da launukan abin da aka ɗauka, zuwa hoton da muke gani.  Aikin wannan na’ura na farawa ne daga sadda haske ya shige ta kafar da tabarau ya bashi don samun isa ga na’urar.  Idan akwai duhu a mahallin, hoton zai fito da duhu.  Haka idan hasken wajen na da kaifi, nan ma hoton zai fito fari fat, ya wanke kusan dukkan launukan dake tattare da surar abin da aka ɗauka.  A taƙaice dai, iya daidaiton haske iya yadda launukan hoton suka fito raurau.  Iya yadda haske yayi ƙaranci iya yadda hoton ya rasa surarsa ta asali.

Waɗannan dai su ne manyan ɓangarorin na’urar ɗaukan hoto, ko kyamara, a taƙaice.  Abu na gaba shi ne bayani kan nau’ukan kyamara, da siffofin kyamara, da kuma yanayin ɗaukan hoto, wato Camera Modes kenan.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.