Kowa Ya Debo Da Zafi: Labarin Pablo Escobar (2)

Na fara rubuta wannan labari ne a shafina na Facebook, a shekarar 2016.

395
  1. Bayan dukiya ta zauna da gindinta, Pablo ya sayi wani ƙaton fuloti mai girman murabba’in kilomita 20 don gina gidansa na kansa, a ƙauyensu mai suna: Antioquia. A wannan wuri ya gina gidansa mai ɗauke da mashaya, da filin ƙwallo, da gidan dabbobi (Zoo), da ƙorama don amfamin iyalinsa da abokan hulɗ Shekarar 1982 bata ƙare ba sai da yayi takara kuma yaci zaɓen shiga Majalisar ƙasar Kolombiya. Saboda samun shiga ma, yana cikin tawagar gwamnatin Kolombiya wajen rantsar da sabon shugaban ƙasar Spain, Felipe Gonzalez, a wancan lokaci.  Ka ji kitso da ƙwarƙwata.  Duk wannan ya faru ne a lokacin da hukuma bata gama fahimtar haƙiƙanin Pablo Escobar ba.

 

  1. Daga nan ya fara shahara a duniya. Kasuwancinsa na miyagun ƙwayoyi ya yaɗu daga ƙasar Amurka zuwa ƙasar Meziko, da ƙasar Puerto Rico, da ƙasar Dominikan, da Venizuela, kai abin har zuwa ƙasar Spain. Bayan koken ɗin ƙasar Kolombiya, Pablo ya nausa ƙasashen Bolivia da Peru, don ƙara samun nau’in koken mai inganci, wanda yafi na ƙasar Kolombiya.

 

  1. Haɓakar wannan sana’a ƙazamtacciya ta zama sanadiyyar mayar da Pablo Escobar shahararren mai kuɗi, mai dukiya, hamshaƙin mai abin hannu ba ƙarami ba. Ya mallaki mulki, irin na zalunci. Da kuɗi irin na haram.  Wannan ya mallaka masa hanyoyin ciyar da manufofinsa gaba masu muni da ƙazamin sakamako ga talakwa, da jami’an tsaro, da hukumomin gwamnati, kai, da ma gwamnatin ƙasar baki ɗaya.

 

- Adv -

  1. Ka’idojin Pablo Escobar na gine ne cikin manufofin da yake zartarwa a duk sadda ya samu hali a rayuwarsa. Sadda yake karami ya sha gaya wa abokansa cewa babbar manufarsa ita ce ya zama shugaban kasar Kolombiya. Wannan yasa a kasar, bayan ya tumbatsa ya fara taimakon talakawa da haramtacciyar dukiyarsa, ake kiransa da lakabin: “Robin Hood.”  Ya kuma samu wannan dama ne sanadiyyar habakar kasuwancinsa haramtacce na fodar ibilis (Cocaine).  Kashi 80 na koken dake shiga kasar Amurka daga kamfaninsa ne.  Sai da aka wayi gari a duk yini yana shigar da tan 15 na koken cikin kasar Amurka. A wannan lokaci aka ce duk mako yana cin riban dalar Amurka miliyan dari hudu da ashirin ($420,000,000.00), kwatankwacin Naira biliyan tamanin da biyu da miliyan dari bakwai da arba’in kenan (N82,740,000,000.00)!

 

  1. Wannan ya tilasta masa sayan kananan jirage masu suna “LearJet” don daukan wannan kazamin kudi daga wuri zuwa wuri. Saboda yawan wadannan kudade, a duk mako ana sayan robar daure kudi (Rubber Band) na dalar amurka dubu biyu da dari hudu ($2,400.00) don daure kudaden kawai. Kwatankwacin Naira dubu dari hudu da saba’in da biyu da dari takwas kenan (N472,800.00). Babban yayansa shi ne akanta dinsa, wanda ke lura da kudade. Shi ne ya rubuta littafi na musamman bayan wannan dambarwa ta kare, mai suna: “The Accountant Story,” don bayyana hakikanin abubuwan da suka faru a lokacin.

 

  1. A shekarar 1990 Pablo ya zama daya daga cikin masu kudin duniya, kamar yadda mujallar Forbes ta tabbatar. Domin a lokacin an tantance ya tara zallar kudi da adadinsa ya kai dala biliyan talatin ($30,000,000,000.00), kwatankwacin Naira Tiriliyan shida (N6,000,000,000,000) kenan kudin Najeriya.  Daidai da kasafin kudin kasarmu na wannan shekara (2016) kenan.  Wannan, a cewar malaman tarihi, wadanda aka iya kididdigewa kenan.  Amma kudaden Pablo, a cewarsu, ya kai dala biliyan dari.  Tirkashi!

 

  1. Duk da wannan kazamin dukiya Pablo bai hakura da manufarsa na son zama shugaban kasar Kolombiya ba. Nan take ya fara taimakon talakawa.  Ya gina musu Coci, da filayen kwallo, da wuraren shakatawa, da kuma gidajen kwana.  Wannan ya jefa sonsa a zukatan talakawa musamman na jiharsu, har suka dauke shi a matsayin wani wanda yazo don cetonsu daga bakin talaucin da suke fama dashi sanadiyyar talaucin gwamnatin da bata gama farfadowa daga mummunar halin da ta fada cikin shekarun 1950s da ya haddasa mutuwar mutane sama da dubu dari da hamsin ba.  Nan take Pablo ya shahara, ya tumbatsa, ya zama wani gwarzo, a bangare daya kenan.  Sadda hukuma ta fara binsa don kama shi, zanga-zangar rashin amincewa aka yi a jiharsu.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Abdulrashid says

    Mu na godiya. Malam akwadai cigaba

    1. Baban Sadik says

      Sosai. Za su ta zuwa babu kakkautawa in sha Allah.

Leave A Reply

Your email address will not be published.