Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (7)

Ɓangarorin SoC

Daga cikin ƙananan ayyukan wayar salula akwai jirkita bayanan da wayarka ta ɗauko na bidiyo, zuwa asalin hoton bidiyon kai tsaye.  Kamar yadda na’urar Image Processing Unit ko IPU ke yi wajen sarrafa bayanan da waya ke ɗaukawa daga kyamara, zuwa asalin hotunan da wayar ta ɗauka.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 15 ga watan Satumba, 2023.

227

Ɓangarorin Babbar Cibiyar Sarrafa Bayanai (SoC)-2

Graphics Processing Unit (GPU): 

Wannan na’ura ita ce ke lura da sarrafa bayanan da suka shafi na’ukan manhajoji masu nauyi wajen sarrafawa, kamar manhajojin wasan wayar salula (Mobile Games), ko sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin ƙanƙanin lokaci.  Ita ce na’urar dake taimaka wa wayar salula karɓan umarnin masu amfani da manhajar wasa; ya Allah na gudun mota ne, ko wasan ƙwallo, ko na yaƙi, ba tare da wayar tana seɓi ko zafi ba saboda yunƙurin sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin ƙanƙanin lokaci.  Samuwar wannan na’ura akan injin wayar salula na cikin dalilan dake sa a samu wayoyin salular da suka fi kwamfuta ƙwari wajen sarrafa bayanai masu ɗimbin yawa cikin lokaci taƙaitacce.  Galibin kwamfutoci, idan ba kwamfutoci na musamman da ake amfani dasu a ɗakuna da cibiyoyin binciken kimiyyar likitanci ko sararin samaniya ta amfani da sabuwar ƙirƙirarriyar fasaha ba, wato Artificial Intelligence (AI), duk sauran na zuwa ne da na’urar CPU kaɗai.  Idan kana buƙata ne sai ka saya daban ka ɗora wa kwamfutar.

Image Processing Unit (IPU): 

Ɓangaren IPU na’ura ce dake aikin sarrafa bayanan da kyamararka – wato na’urar ɗaukan hoto da bidiyo – ke cafkowa, sannan ta mayar dasu zuwa hoto daskararre (Still Image).  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, a duk sadda ka ɗauki hoto da wayarka ta salula, wayarka na cafko bayanan surarka da na abin da kake ɗauka ne a matsayin rubutattun bayanai.  Da zarar ta gama tattaro bayanan, sai wannan na’ura ta Image Processing ta jirkitasu zuwa hoton da ka ɗauka, su bayyana maka yadda ka ɗaukesu kai tsaye.  Wannan aiki na faruwa ne cikin mafi ƙanƙantar lokaci – daga sadda ka ɗauki hoton zuwa lokacin da hoton ya bayyana maka akan wayarka.  Galibi ba ya wuce sakwan ko daƙiƙa guda ko ma ƙasa da hakan.  Iya gwargwadon ƙarfin kyamarar wayar.

Digital Signal Processor (DSP): 

- Adv -

Na’urar DSP ce ke da alhakin sarrafa bayanan da suka shafi lissafi da siginar bayanai da wayar ke tattarowa ta amfani da na’urorin hankaltar mahallin da wayar take.  A tare da cewa na’urar CPU na sarrafa bayanan da suka shafi lissafi, sai dai bayanai ne taƙaitattu.  Idan lissafi ne mai tarin yawa, na’urar CPU  ba ta iya aiwatar dasu cikin sauƙi da daɗin rai.  Wannan na’ura ta DSP ce ke aiwatar da hakan cikin ƙanƙanin lokaci, kamar yadda na’urar GPU ke yi wajen abin da ya shafi sarrafa bayanai masu alaƙa da fuska da ɓangarorin manhajar wayar salula masu ɗauke da launuka ko hotuna masu inganci sosai.  Kowace wayar salula na zuwa ne da na’urar hankaltar mahalli da yanayi, wato: “Sensor”.  Wannan na’ura aikinta shi ne lura da yanayin da wayar take ciki, ko mahallin da take ciki, ta hanyar tattaro bayanai daga mahallin da wayar take, ko yanayin da wayar take; a tsaye ne ko a kwance.  Bayani kan waɗannan nau’ukan na’ura na nan tafe in Allah Ya so.

Neural Processing Unit (NPU): 

Wannan ita ce na’urar dake aikin sarrafa bayanan da suka shafi ƙirƙirarriyar fasaha da ake cusa wa na’urorin sadarwar zamani, wato: Artificial Intelligence (AI), kamar yadda na bayyana a baya.  Akan samu wannan na’ura ne a manyan wayoyin salula na zamani masu tsada.  Hakan nan, wannan na’ura ce ke taimaka wa wayar salula iya tantance murya, ba wai a lokacin kira ko amsa kira ba, a a, a lokacin baiwa wayar salula umarni ta hanyar murya nake nufi.  Kamar yadda na sanar ne a baya, fannin AI ya ƙunshi koya wa na’urorin sadarwar zamani ne iya fahimta da hankaltar abubuwa – tsakanin murya ko sauti, da rubutu, da hoto, da bidiyo.  Wannan na’ura ta NPU ce ke taimaka wa wayar salula gudanar da wannan aiki.

Video Encoder/Decoder: 

Daga cikin ƙananan ayyukan wayar salula akwai jirkita bayanan da wayarka ta ɗauko na bidiyo, zuwa asalin hoton bidiyon kai tsaye.  Kamar yadda na’urar Image Processing Unit ko IPU ke yi wajen sarrafa bayanan da waya ke ɗaukawa daga kyamara, zuwa asalin hotunan da wayar ta ɗauka.  Idan ka kunna kyamarar wayarka don ɗaukan hoton bidiyo, kana matsa alamar ɗauka, wayarka za ta fara tattaro bayanan hoton da kake ɗaukawa kai tsaye.  A yayin da take tattaro waɗannan bayanai masu ɗauke da siffofin abin da kake naɗewa, wannan na’ura ce aikin jirkita waɗannan rubutattun bayanai zuwa hoton bidiyon da kake gani.  Wannan aikinta na farko kenan, kuma shi ake kira: “Video Encoding”, wato naɗo bayanan tare da jirkita su zuwa hoton bidiyo.  Aikinta na biyu kuma shi ne, jirkita hoton bidiyo zuwa rubutattun bayanai don aikawa dasu ga wata na’ura  ko mahallin sadarwa kamar Intanet, ko kuma aikawa zuwa wata ma’adana – irin su filash ko katin memori, misali.

Modem: 

Na’urar Modem ce ke sadar da wayarka ga siginar rediyo don baka damar aiwatar da sadarwa na murya, ko aikawa da karɓan bayanai ta hanyar Intanet, ko iya fahimta da ma’amala da dukkan wata na’ura ko ma’ada da za a iya maƙala mata don aiwatar da sadarwa ko don sarrafa bayanai.   Ma’ana, da wannan na’ura ne wayarka ke iya samun yanayin sadarwa, wato: Network na kamfanin wayarka.  Sannan ita ce na’urar dake taimaka wa wayarka wajen aiwatar da sadarwa tsakaninta da wata waya ‘yar uwarta, ya Allah kai tsaye ne – ta hanyar fasahar bulutud – ko ta hanyar siginar Intanet ne.  Ita ce kuma har wa yau ke taimaka wa wayarka ta salula iya gane an jona mata wata ma’adana – kamar katin memori, ko ma’adanar filash misali – don karɓa ko aika bayanai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.