Gaskiya da Gaskiya (13): Idan Bera da Sata…(3)

Sai mun gyara halayenmu da dabi’unmu da alakokinmu da junanmu sannan kasa za ta gyaru. Wajibi ne kowa ya kamanta daidai cikin ayyukansa.

198

Mu fara da aikin ofis a Arewacin Najeriya.  

Abu ne sananne cewa aikin gwamnati, kamar yadda muke kiransa, aiki ne mai mahimmancin da malaman addini ke ganin ya kamata a samu musulmi da yawa a ciki, saboda tasirinsa wajen gina al’umma da saita mahangar rayuwa.  Ni kaina sai da na fara aikin gwamnati na fahimci tasirinsa.  To amma, duk wani ma’aikacin gwamnati a Najeriya ya san abubuwa ba su tafiya daidai.

Kafin a dauke ma sai ka san wani, ko da kana da takardu cikakku da suka sa ka cancanta.  Manyan ma’aikata ne da komai a hannunsu.  Raina kan baci ganin yadda ake kwamacala wajen kwangila, da yadda ake daukan wanda aka ga dama, da yadda ake diban kudi babu hisabi, da kuma uwa uba, yadda aka mayar da abin wani makami na yaki a siyasance.  Kason da gwamnati ke baiwa hukumomi ba duka ke zuwa taska ba.  A bangaren jiha, harkar “dibi-da-kanka” ake yi, balle a koma karamar hukuma.  Akwai kananan hukumar da idan kaso yazo, “kasa-mu-raba” ake tsakanin manya.  Kudin hutun idan ma ka rubuta, sai a kusan wata 6 baka samu ba.  Shugaban hukuma na iya karkatar da kason da aka turo wa hukumar zuwa taska na musamman da zai rika samun kudin ruwa (Interest Returns), sai  bayan kwanaki 90 ko 180, in ya ga dama ya cire ya karkato dashi zuwa hukumar don yayi amfani.  Kana iya samun Daratka a jiha ko karamar hukuma yana da ma’aikatan bogi (Ghost Workers) sama da 200 shi kadai!  A duk wata shi yake karbe albashinsu.  Wannan kadan ne daga bangaren shugabannin da muke zargi.

- Adv -

Amma ko kadan mukan mance cewa mu ne masu share musu fage wajen aiwatar da dukkan badakalar da suke yi.  Duk wata cuwa-cuwa da ake yi a hukumomin gwamnati, karamin ma’aikaci ne ke shirya ta.  Mai biyan albashi a karamar hukuma ya kusan fin kowa kudi. Domin ya ga dama ya rage naira dubu daya daga albashin kowane ma’aikaci idan yazo biya, kuma ba abin da zai faru. A wasu wuraren ma, kashiya ya ga dama ya biya ka rabin albashi, yace rabin sai wata mai zuwa. Shiru kenan, wai malam ya ci shirwa.  Idan kayi kwangila, kudadenka ba za su fito ta dadi ba sai ka bayar da “abin sayan goro.”  Kwanakin baya wani dilar motoci ke sanar dani cewa wani Kanuri yazo da wata motarsa mai kyau da kimarta ya kai naira miliyan biyar, amma a miliyan biyu da rabi ya karyar da ita.  Da suka tambaye shi dalili,  yace wasu kudadensa ne suka makale a wata hukuma na kwangila, zai fanshe su.

Karfe nawa muke zuwa ofis?  Sadda nake bin kudaden mahaifina na fansho bayan rasuwarsa, karfe tara na safe kan same ni a hukumar da nake zuwa, a Abuja fa, ba jiha ba, amma sai karfe 11 galibin ma’aikatan ke zuwa.   Da kashin farko na kudaden suka fito, sai da na ba da “abin sayan goro” domin in banyi haka ba, akwai kashi na biyu da yafi tsoka, bazan same shi ba.  Ofisoshin fansho a halin yanzu sun zama ramukan cuta da almundahana.  Ba ruwansu da maraicinka.  Kuma kananan ma’aikata ne ke wannan badakala.  Da yawa cikin ma’aikatan kananan hukumomi sai karshen wata suke zuwa ofis, domin lokacin ne ake biyan albashi.  Ba mai zuwa da wuri, sannan da zarar karfe 2 zuwa 3, sai kowa ya kama hanyarsa.  Wani dan uwa daga Jihar Kebbi yake cewa, babu wadanda za ka ga suna lazimtar ofis sosai sai kashiya, idan akwai kudi, da sauran manya.  Yace min akwai kashiya da aka masa karin girma, nan take ya rikice yace don Allah a bar wannan karin girman bai so; a mayar dashi matsayinsa na da.  Saboda bazai iya barin badakalar da ya saba ba.

Galibin kananan ma’aikata a hukumomin gwamnati suna da “malamai” masu musu addu’a, amma galibinsu ko karatun da ake yi a masallaci basu zama balle su saurara.  Basu san addini ba amma suna da malamai.  Idan aka tashi rage ma’aikata, maimakon su koma ga Ubangiji wajen neman zabi, sai aje a ta yanka raguna, ko a ta binne su da rai, don a tabbata a wurin da ake cuwa-cuwa.  Jama’a, abin da yawa.

Yanzu da irin wannan dabi’ar muke zagin shugabanni?  Bayan mu ne masu shirya musu duk tsiyar da suke yi?  In karkare mana, babu wata badakala da wani babban ma’aikacin gwamnati ke yi, wanda wani karamin ma’aikaci ba ya yi.  Sai wanda Allah ya tsare.  Waye abin zargi, tsakanin mu dasu?

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. […] .IRPP_button , .IRPP_button .postImageUrl , .IRPP_button .centered-text-area { min-height: 86px; position: relative; } .IRPP_button , .IRPP_button:hover , .IRPP_button:visited , .IRPP_button:active { border:0!important; } .IRPP_button { display: block; transition: background-color 250ms; webkit-transition: background-color 250ms; width: 100%; opacity: 0.7; transition: opacity 250ms; webkit-transition: opacity 250ms; background-color: #141414; box-shadow: 0 1px 2px rgba(0, 0, 0, 0.17); -moz-box-shadow: 0 1px 2px rgba(0, 0, 0, 0.17); -o-box-shadow: 0 1px 2px rgba(0, 0, 0, 0.17); -webkit-box-shadow: 0 1px 2px rgba(0, 0, 0, 0.17); } .IRPP_button:active , .IRPP_button:hover { opacity: 1; transition: opacity 250ms; webkit-transition: opacity 250ms; } .IRPP_button .postImageUrl { background-position: center; background-size: cover; float: right; margin: 0; padding: 0; width: 30%; } .IRPP_button .centered-text-area { float: left; width: 70%; padding:0; margin:0; } .IRPP_button .ctaText { border-bottom: 0 solid #fff; color: #FFFFFF; font-size: 13px; font-weight: bold; margin: 0; padding: 0; } .IRPP_button .postTitle { color: #ECF0F1; font-size: 16px; font-weight: 600; margin: 0; padding: 0; width: 80%;display: inline-block;float: right; } .IRPP_button .ctaButton { background: #1ABC9C; color: #FFFFFF; border: none; border-radius: 3px; box-shadow: none; font-size: 14px; font-weight: bold; line-height: 26px; margin: 18px 14px 18px 14px; moz-border-radius: 3px; padding: 12px 0; text-align: center; text-decoration: none; text-shadow: none; webkit-border-radius: 3px; position: absolute;float: left;padding: 5px 3%;width: auto;left: 0;top: 8px; } .IRPP_button:hover .ctaButton { background: #16A085; } .IRPP_button .centered-text { display: table; height: 86px; padding:0; margin:0; padding-left: 0px!important; top: 0;width: 100%; } .IRPP_button .IRPP_button-content { display: table-cell; margin: 0; padding: 0; padding-right: 10px; position: relative; vertical-align: middle; width: 100%; } .IRPP_button:after { content: ""; display: block; clear: both; } Blogging Vs Vlogging – Wanne Yafi Kawo Kudi da Kuma SaukiREAD Source :- https://babansadik.com/gaskiya-da-gaskiya-13-idan-bera-da-sata-3/ […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.