Kowa Ya Debo Da Zafi: Labarin Pablo Escobar (3)

Na rubuta wannan labari ne a shafina na Facebook, a shekarar 2016.

264
  1. Pablo bai kai wannan matsayi ba sai da ya taka abokan gabansa wajen sana’ar, inda yake aikawa ana kashe su daya bayan daya. Pablo ya sha tayar da bam a wurare don cinma manufarsa. Wannan ya jawo hankalin hukuma ta fara binsa.  Daga nan ya fara kashe ‘yan sanda.  Ya salwantar da jami’an ‘yan sanda sama da dubu daya, tare da ma’aikatan gwamnati.  Alkalai kuwa ba’a magana.  Da zarar shari’arsa taje kotu, zai sa a nemi alkalin, ya tallata masa ka’idarsa mai take: “Plata O Plomo,” (yaren Spain ne) ma’ana: “Azurfa ko Dalma.”  In baku gane ba, ko dai alkali ya karbi cin hanci ko kuma dalmar bindiga na jiransa.  Da haka ya kashe alkalai sama da 350.  Shi ya kashe dan takaran shugaban kasa kafin zaben 1989.  Ya taba tura yaransa suka shiga ofishin alkalin dake rike da bayanan wadanda hukuma ke son aikawa dasu kasar Amurka idan aka kama su, suka fasa ofishin, suka kona dukkan takardun dake cikin wurin baki daya.  Akwai sadda Kotun Kolin kasar Kolombiya na kan sauraron wani kara da ake yi kansa, nan take ya aiko yaransa suka hargitsa kotun, suka kashe dukkan alkalan guda tara dake sauraron karar.  Shari’ar da ba a karasata ba kenan, sai gobe kiyama a gaban Allah.

 

  1. Wannan sa-in-sa da ya fara da hukuma ya fara samar masa da bakin jini. Kuma ya tabbatar idan ya shiga hannu, to, za a mika shi kasar Amurka ne. Domin ta dade tana nemansa, ganin cewa kashi 80 cikin 100 na koken dake shiga kasar daga kamfaninsa ne.  Shi kuma, a duniya babu abin da ya tsana irin ace za a aika dashi kasar Amurka. Yana cewa: “Da inyi minti guda a kurkukun kasar Amurka, gwamma ina kabari a kasar Kolombiya.”  Wannan tasa yayi ta kokari, ta amfani da kudi da bibiyar ‘yan majalisar kasar, akan su soke wannan doka dake baiwa kasar Kolombiya damar aika masu laifi irin nashi zuwa kasar Amurka.  Da abin yaci tura, yace wa hukumar kasar, in suka soke wannan doka zai biya wa kasar Kolombiya bashin da ake binta, wanda ya kai dalar Amurka biliyan goma ($10,000,000,000.00)!  Hukuma taki.

 

- Adv -

  1. Duk da ta’addancinsa, Pablo mutum ne mai son iyalinsa. Duk inda ya buga, ba ya mancewa dasu. Idan hukuma ta sa shi a gaba, ba ya barinsu a gida, dasu yake yawo.  Akwai sadda yake wajen buya daga jami’an tsaro, sanyi ya addabi ‘yarsa karama, nan take ya debo dalar Amurka wajen miliyan biyu ya kona, don ya jiyar da ita dumi daga sanyin dake damunta.  Dala miliyan biyu wajen Naira miliyan dari uku da casa’in da hudu kenan (N394,000,000.00)!  Har zuwa lokacin da karshensa yazo, bai taba yarda matsalolinsa sun shafi iyalinsa ba.

 

  1. Hankalin gwamnatin kasar Kolombiya ya tashi matuka, har wasu kasashe suka fara daukanta nakasasshiya, wacce mutum daya ya gagareta. Wannan ba karamin bakanta mata rai yake ba.  Kuma ga shi sai ci gaba yake da kashe mutane, musamman jami’an gwamnati.  Wadanda suka tsira kuma dalilin bai wuce dayan dalilai biyu; ko don tsoron dalmarsa, ko kuma saboda cin hanci na kudade da yake basu.  Don ya taba gaya wa wani abokinsa cewa:  “Shi harkar safaran miyagun kwayoyi fa ya ginu ne kan cin hanci da rashawa.  Kawai ka samu wannan ka bashi cin hanci, ka sake samun wancan ka bashi, sannan ka hada baki da wani ma’aikacin banki mai hazaka, ya karkato maka kudadenka cikin sauki.”   Allah sa kun fahimci abin da yake nufi a nan.

 

  1. Da Hukuma ta ga abin ya ci tura, sai ta fara lallabar Pablo; don Allah, tace masa, ya yarda a kamashi, a rufe shi, ko da rufewa ce irin ta jabu. Su dai ya daina abin da yake yi ko kasar ta samu kima a idon duniya.  To sai aka yi dace, daidai wannan lokaci kuma an samu wata kungiyar ‘yan daba, wadanda a cewarsu suna wakiltar sauran mutanen da Pablo yasa aka kashe ne, don daukan musu fansa.  Sunan wannan kungiya dai shi ne: “Los Pepes” (People Persecuted by Pablo Escobar).  Da yaga su ma a kullum nemansa suke yi, sai ya amince da tayin gwamnati na ya yarda a kama shi, a rufe, amma da sharadi.  Mece ce sharadin?  Yace wa hukuma, idan za a rufe shi, shi ne zai gina gidan kurkukun da zai zauna, sannan yaransa ne za su rika gadinsa, ba jami’an tsaron gwamnati ba, sannan a duk mako, za a rika barin iyalinsa suna zuwa duba shi, a kalla sau uku.  Nan take gwamnati ta amince wa sharuddansa.  Illa dai ta kara da cewa, zai kasance a wannan kurkuku ne na tsawon shekaru 5.  Tirkashi!  Shi kanshi wannan yarjejeniya sai da aka yi wajen watanni 6 ana tukawa ta karkashin kasa, kafin aka cinma matsaya.  To ina batun mika shi ga kasar Amurka?  Ai tuni ya samu damar toshe wa jami’an Majalisar Canza Tsarin Mulkin kasa (Constitutional Conference members) baki, wanda hukumar kasar ta kafa a shekarar 1990, har suka soke wancan doka daga sabon tsarin mulkin kasar.

 

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.