Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (16)

Bambancin Kamfanoni (2)

A yau za mu ɗora bayani kan yadda farashin wayoyin salula ke bambanta sanadiyyar bambantar kamfanin dake ƙera su.

225

Bambancin Kamfani (2)

A makon jiya munyi bayani ne cewa, manufofin kamfanonin ƙera wayar salula na duniya na karkasuwa ne zuwa kashi uku, ta la’akari da farashin wayoyin.  Kashin farko su ne wayoyin masu ƙaramin ƙarfi.  Waɗannan su ne wayoyi masu rahusa, kuma masu ƙarancin farashi idan an gwama su da waɗanda suke sama dasu.  Sai kashi na biyu, wato masu matsakaitan farashi kenan.  Su ne na tsakiya.  Sai kashi na uku, wato wayoyin ‘yan alfarma, wanda suka kasu kashi biyu; da waɗanda ake ƙerawa don masu hannu da shuni ko masu sha’awan wayoyi masu tsada.  Ko don saboda yayi ko kuma don ribatar fa’idoji da tagomashinsu.  Sai kuma waɗanda wasu ke sa wa a ƙera musu – kamar hamshaƙan masu arziƙi ko shugabannin wasu ƙasashen.

A yau za mu ɗora bayani kan yadda farashin wayoyin salula ke bambanta sanadiyyar bambantar kamfanin dake ƙera su. Dangane da wannan ɓangare, akwai abubuwa da dama da za mu duba dangane da kamfanonin dake ƙera wayoyin salula da dalilan da suke sa su zama masu tsada ko araha, bayan waɗancan dalilai da muka zayyana a makon jiya.  Ga kaɗan daga cikin kamfanonin ƙera wayar salula na duniya da tsarin farashin wayoyinsu na salula, da kuma dalilan dake sa su zama masu tsada ko araha, bayan waɗancan dalilai na gama-gari da muka zayyana tsawon makonni ko ince watannin da suka gabata.

Wayoyin Tecno, da Infinix, da iTel

Wayoyin salula kan yi araha ko tsada ta la’akari da tsarin kamfanin da yake ƙera wayar.  Kamfanonin da suka shahara wajen ƙera wayoyin salula masu araha musamman ga ƙasashe masu raunin tattalin arziƙi dai su ne kamfanonin ƙera wayar salula na ƙasar Sin. Kashi 70 cikin 100 na wayoyin salular dake jerin kamfanonin Tecno da Infinix da iTel ke ƙerawa masu araha ne.  Dalili kuwa shi ne, daman don mutane masu ƙaramin ƙarfi ake ƙera su.  Kashi 20 daga cikinsu ne na masu matsakaita ƙarfi.  A yayin da ragowan kashi 10 kuma na ‘yan alfarma ne.  Su ma sai daga baya ne kamfanonin suka fara ƙera wayoyi masu tsada.  Amma asali mafi akasarin wayoyinsu duk na masu ƙaramin ƙarfi ne.

- Adv -

Asalin kamfanin da ya mallaki waɗannan kamfanonin ƙera wayoyin salula dai shi ne kamfanin Transsion Holding Company dake ƙasar Sin.  Bayan waɗancan kamfanoni da ya mallaka, har wa yau shi ne ya mallaki kamfanin Oraimo wanda ke ƙera kayayyakin wayoyin salula – irin su na’urar caji, da fuskar kariya ta wayar salula (Screen guard), da batiri, da na’urar sauraron sauti da sauransu.  Sannan shi ne ya mallaki kamfanin Syinix dake ƙera firiji, da sauran kayayyakin amfanin gida na dafe-dafe da sauransu.

Mahangar wannan kamfani wajen ƙera wayoyin salula shi ne sauƙi.  Wannan ita ce manufar kamfanin baki ɗaya.  Domin wayoyin a asali yana ƙera su ne shigowa da kuma sayar dasu a ƙasashen Afirka da Asiya da wani ɓangaren Kudancin Amurka (Latin America).  Waɗannan nahiyoyin duniya su ne aka kiyasta cewa sun fi sauran nahiyoyin duniya talauci da raunin tattalin arziƙi.  Dalilin da yasa wayoyin suke zama masu araha, yana da alaƙa ne da abubuwan da kamfanonin ke zubawa a ciki.  Akwai kamfanonin kasuwanci na ƙasashen duniya, musamman waɗanda ke ƙasar Sin, masu son a tallata musu hajojinsu ta hanyar wayar salula.  Waɗannan kamfanoni ne ke biyan wani kaso na kuɗaɗe don a tsofa tallar hajojinsu a cikin waɗannan wayoyi na salula.  Kuma hakan ne ke sa a rage farashinsu ga masu saye a waɗannan nahiyoyi da na zayyana.

A taƙaice dai, manufar waɗannan kamfanoni ita ce samar da wayoyin salula masu sauƙin farashi ga ƙasashe matalauta.  Don haka, duk da cewa a halin yanzu abubuwa sun yi tsada musamman sanadiyyar taɓarɓarewar darajar Naira, idan ka gwama farashin wayoyin waɗannan kamfanoni na ƙasar Sin – Teco, da Infinix, da iTel – da na wasu kamfanoni irin su Gionee, ko Samsung, za ka ga bambanci mara misaltuwa a tsakaninsu.

Wayoyin Samsung

Kamfanin Samsung na daga cikin manyan kamfanonin ƙera wayar salula a duniya.  Asali kamfanin ƙasar Koriya ta Kudu ne (South Korea).  Bayan wayar salula, kamfanin na ƙera talabijin, da kwamfuta, da ma’adanar wayar salula da na kwamfuta, da sauran kayayyaki na nau’urorin sadarwa na zamani.  Kamfanin Samsung na cikin kamfanonin wayar salula dake ƙera dukkan nau’ukan wayoyin salula guda uku da bayaninsu ya gabata a makon jiya.  Yana ƙera masu sauƙin farashi, wato Budget Phones.  Yana ƙera na masu matsakaitan ƙarfi, wato Mid-range Phones.  A ɗaya ɓangaren kuma yana ƙera masu ɗan karen tsada, wato Flagship Phones.  Kamfanin Samsung na da wayar salula guda ɗaya da farashinta yakai Naira Miliyan ɗaya da ɗoriya, musamman a yanzu ma da farashin dala yayi tashin gwauron zabo.

Sai dai kuma, saboda shahara da kuma daɗewa a fagen ƙera wayoyi a duniya, wayoyin Samsung masu ƙarancin farashi sun ɗara na kamfanin Tecno ko Infinix.  Da wahala a yanzu ka samu wayar Samsung sabuwa ta ƙasa da naira dubu casa’in, musamman wacce aka ƙera cikin shekaru biyu da suka gabata.  Galibin wayoyin Samsung na masu ƙaramin ƙarfi suna farawa ne daga naira dubu ɗari zuwa ɗari da saba’in ko tamanin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.