Shawarwari Ga Gwamnatin Tarayya Kan Hanyoyin Ciyar Da Najeriya Gaba A Fannin Kimiyya Da Ƙere-Ƙere (3)

Kafin zuwan turawan mulkin mallaka ƙasar nan, al’ummar wannan ƙasa na amfani da ne da hanyoyi daban-daban da suka ƙirƙira a fannin ƙere-ƙere.  – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 30 ga watan Yuni, 2023.

290

Wasu Ƙa’idoji Shida (2)

Sifa ta biyu, idan ƙasa ta ƙasa haƙo (ba sarrafawa ake nufi ba) albarkatun da Allah ya mata daga ƙarƙashin ƙasa, sai ta dogara ga wasu ƙasashe masu taimaka mata da kayayyakin aiki da kuma ma’aikatan da za su yi mata wannan aiki, to, ita ma ba za a sanya ta cikin sahun ƙasashen da suka ci gaba ba.  Idan muka dubi wannan sifa, sai muga cewa daram ta zauna a kanmu.  Ba ma harkar mai kaɗai ba, hatta injinan haƙo albarkatun ƙasa irin su zinare da azurfa, duk ba mu da su. Galibin masu aikin kuza a Najeriya da hannunsu suke yi.  Kai, hatta injinan haƙa rijiyar burtsatse daga wasu ƙasashe muke sayowa.

Sifa ta uku, idan aka wayi gari galibin manoma a ƙasa suna amfani ne da hannunsu (fartanya da garma) wajen nome ƙasar da suke shuka akai, to, ba za a ce wannan ƙasa ta ci gaba ba.  Idan muka dubi wannan ita ma, sai  muga daram ta zauna a kanmu.  Watakila mai karatu ya ce ai akwai masu amfani da katafilun noma a gonakinsuAmma mutum nawa ne?  Galibin manoman Najeriya da ƙarfin tuwonsu suke noma abin da ake ci.  Wannan har a babban birnin tarayya ma haka abin yake; duk ɗaya ne, wai makaho ya yi dare a kasuwa.

Ma’auni na hudu, idan ƙasa tana dogaro ne da wasu ƙasashe wajen sayen ɓangarorin mashina ko injinan sarrafa kayayyaki ko albarkatu da take amfani dasu, to nan ma ba za a ce ta ci gaba ba.  Ai mun gama da wannan, tunda har ta kaimu ga sayen waɗannan kayayyaki daga wasu ƙasashe, ai dole ne mu koma gare su idan sun lalace. A taƙaice dai, Najeriya ba ta iya ƙera bangarorin manyan injinan da take amfani da  su wajen sarrafa arziƙinta.

Sifa ta biyar, idan ya zama galibin kayayyakin da ƙasa ke sayarwa a kasuwannin saye da sayarwa na duniya nau’in arziƙin da ta ciro ne daga ƙasa kai tsaye, ko ta noma kaɗai, ba wai sarrafaffu ko ƙerarrun abubuwa bane, to nan ma za a ce bata ci gaba ba.  Wannan a fili yake.  Tabbas muna fitar da ƙarafa, da alminiyon, amma ɗanyensu; domin kamfanonin da ke sarrafa su sun kwanta dama.  Don haka, galibin hajojinmu basu wuce ɗanyen mai ba, sai albarkatun noma, da wasu abubuwa.

- Adv -

Sifa siffa ta shida kuma ta ƙarshe, suka ce idan ƙasa ta kasa ƙera makaman da za ta kare al’ummarta dasu, sai dai ta siyo daga wasu ƙasashe, to, nan ma ba za a ce ta ci gaba ba.  Wannan ke nuna mana cewa, hatta kayayyakin kare ƙasa, sai mun siyo.  Kuma haka ne.  Amma ba wannan bane aibun, aibun na farawa ne daga lokacin da muka kasa yin wani ƙoƙari wajen ganin mun samu ‘yancin kanmu dangane da abin da ya shafi ƙera abubuwa irin wannan.

A ƙarshe dai, kamar yadda bayanai suka gabata, na tabbata Mai Girma Shugaban Ƙasa zai fahimci cewa lallai har yanzu da sauranmu.  Domin cikin waɗannan ƙa’idoji ko sifofi guda shida da muka zayyana, babu guda ɗaya da ƙasarmu ta ketare shi; duk sun zauna daram a kanmu.  To daga ina matsalar ta faro ne?

Tarihin Ci Gaban Najeriya a Fannin Ƙere-ƙere

Haƙiƙa a bayyane yake cewa kowace al’umma na da hanyoyin da take bi wajen ciyar da kanta gaba a fannin ƙere-ƙere.  Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar fasaha da hazaƙar da Allah Ya hore wa ɗan adam.  Kafin zuwan turawan mulkin mallaka ƙasar nan, al’ummar wannan ƙasa na amfani da ne da hanyoyi daban-daban da suka ƙirƙira a fannin ƙere-ƙere.  Muna ƙera kujerun da muke zama a kai daga bishiyoyin da Allah ya hore mana a dazuzzukanmu.  Muna ƙera akushi, da masaƙai, da takalma, da zabba, da na ɓarza hatsi, da dai sauransu.  Sannan muna da maƙera inda muke sana’anta abubuwan da muke buƙata wajen noma da kiwo da zamantakewa.  Maƙeran namu ma kala biyu ne; akwai “Farar Maƙera”, inda ake “Farar Kira”.  A wannan maƙera ne ake ƙera tukwanen dalma, da farantan azurfa da zinare, da zabba, da dai sauran kayayyakin alatu da ƙyale-ƙyale.  A ɗaya bangaren kuma, akwai “Baƙar Maƙera”, inda ake “Baƙar Kira” don samar da ruwan garma, da fartanya, da sakatono, da magirbi, da sauran makamantansu. Dukkan waɗannan abubuwa muna ƙera su ne ta amfani da fasaharmu da kuma itatuwa ko bishiyoyi ko duwatsun da Allah ya samar mana a mahallin da muke rayuwa.

Wannan hanya ta ci gaban ƙere-ƙere, wacce turawa daga baya suke kira “Local Crafts”, ita ce hanyar da ta rike mu tun kaka da kakanni, kafin zuwan turawa.  Kuma a haka muka ta rayuwa, cikin kwanciyar hankali da lumana, da kuma wadatuwar zuci.

Da Turawan mulkin mallaka suka shigo ƙasashenmu, sai suka zo da wasu sababbin kayayyakin ƙere-ƙere da suka samar daga ƙasashensu, kuma da ƙarfi da yaji suka yi iya yinsu wajen ganin sun daƙushe ci gaban hanyoyin da muke amfani dasu a baya.  Misali, a Arewacin ƙasar nan, Bature ya same mu da maƙera mai cike da tsari, da masaƙa mai cike da hikima da fasaha; ga kuma mutane masu hazaƙa dake aiki a cikinsu.  Kasancewar dukkan ƙasashe masu mulkin mallaka suna yin haka ne don amfanin kansu da ƙasashen da suke wakilta, nan take suka fara ƙoƙarin ganin sun kashe waɗanann wuraren ƙere-ƙere a ƙasashenmu ta hanyoyi daban-daban, kamar yadda mai karatu zai karanta nan ba da daɗewa ba.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.