Kowa Ya Debo Da Zafi: Labarin Pablo Escobar (1)

Na buga wannan labari ne a shafina na Facebook, a shekarar 2016.

472

Pablo Escobar

- Adv -

 1. Shararren mai safaran miyagun kwayoyi ne, dan ta’adda, kasurgumin barawo, dan dagaji, mai son kai wa ga abin da yake so ta kowane hali. Wanda ya salwantar da rayukan gama-garin mutane sama da 4,000. Da jami’an ‘yan sanda sama da 350. Da alkalan kasar Kolombiya sama da 200.  Mai kudi ne, amma na haram.  Mai taimakon talakawa ne, amma da kudin haram. Shi ne dan ta’addan da a tarihin duniya yafi kowane dan ta’adda kudi a sadda yake raye.  Shi ne Pablo, dan Escobar, dan Hermilda Gaviria, wanda aka haifa a ranar 1 ga watan Disamba, 1949 a birnin Nuevo Loredo, cikin jihar Antioquia ta kasar Kolombiya.
 2. Mahaifinsa manomi ne mai karamin karfi, mahaifiyarsa kuma malamar makaranta ce. Galibin rayuwarsa ya yi ne a babban birnin jiharsu wato Medellin. Ya fara karatu a jami’ar Kolombiya mai suna: Universidad Autonoma Latinoamericana, amma abin bai dore ba.
 3. Ya fara shiga muguwar tafarkin rayuwa ne tun yana dan karami, inda ya fara yanke aljihun mutane a kan titi da kasuwanni, da sayar da kayan sata da tikitin tambola na bogi ga jama’a. Daga baya ya bige da sace motocin jama’a yana sayarwa. Da tafiya tayi nisa ya zama mai tsaron wani kasurgumin barawo a shekarar 1970. Ya kuma taba sana’ar garkuwa da mutane (kidnapping), inda aka kiyasta ya samu sama da dalar amurka dubu dari ($100,000.00) cikin harkar, a wancan lokaci kenan. Ya kure matakin marhalar shekarunsa 20 na farko ne da zama miloniya, sanadiyyar barance da yayi wa wani kasurgumin mai safaran miyagun kwayoyi na wancan lokaci mai suna Alvaro Prieto. Duk wannan ta’asa ya yi shi ne yana kasa da shekaru 20.
 4. Pablo Escobar ya shiga sana’ar safarar miyagun kwayoyi ne a shekarar 1975. A daidai wannan lokaci babu kungiyoyin safaran miyagun kwayoyi (Drug Cartels) kamar yadda ake dasu yanzu. Tun yana fasa-kwaurin kwayoyi (Darug smuggling) a cikin tsoffin tayoyin jiragen sama, har ya mallaki nasa jiragen.  Yakan shirya ne da direbobin jiragen sama, inda yake biyansu Dalar Amurka dubu dari biyar ($500,000.00) a duk sawu daya.  Idan kayan da nauyi ya basu fiye da haka. Don dai a haye masa da hajarsa zuwa kasar Amurka.
 5. Fara wannan sana’a ke da wuya sai mabukata a kasar Amurka suka yawaita. Daga nan ya kulla abota da wani kasurgumin dillali mai suna: Carlos Lehder, suka samar da hanyoyin shigar da koken zuwa kasar Amurka ta jihohin Fulorida da Kalfoniya, daga can kuma a karasa dasu sauran jihohin kasar.
 6. Cikin shekarar 1978 Pablo ya sayi wani tsibiri mai suna Norman’s Cay, mai tazarar kilomita 350 dake kudu-maso-gabashin gaɓar tekun Fulorida. A wani ƙaulin, babban yayansa mai suna: Roberto Theran Escobar, a cikin littafinsa mai suna: “The Accountant Story,” ya nuna cewa haɗin gwiwa suka yi da abokinsa wajen saye. A taƙaice dai, sun sayi wannan tsibiri ne tare da gidajen dake tsibirin, da tashar jirgin ruwa, da kuma Otal dake wurin duka, don gina ɗakunan sanyi na ajiyan Koken, wato: “Cocaine Refrigerated Warehouse.”  Da zarar an ɗebo koken, nan ake zuba su, daga can kuma a riƙa amfani da jiragen sama ana shiga dasu ƙasar Amurka; ƙasar da tafi kowace ƙasa amfani da koken a duniya.  Sun yi wannan aiki ne tsakanin shekarar 1978 zuwa 1982.
 7. Daga nan harka ta haɓaka. An ƙiyasta cewa a duk wata, Pablo yana aika tan 70 zuwa 80 na koken zuwa ƙasar Amurka.  A daidai tsakiyar shekarun 1980s abin yayi gaba; kusan duk jirgi guda na ɗaukan tan 11 na koken.  Sai da aka wayi gari kusan duk koken da ake sha a ƙasar Amurka, Pablo ne ke tura su.  Da kasuwa ta ƙara gaba, yayi hayan jirgin ruwan ƙarƙashin teku (Submarine) guda biyu, don ƙara ɓoye ta’asarsa wajen shiga da koken ƙasar Amurka.

Zan ci gaba.

- Adv -

You might also like
2 Comments
 1. Abdulrashid says

  Muna godiya sosai

  1. Baban Sadik says

   Allah saka da alheri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.