Sakonnin Masu Karatu (2013) (12)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

93

“Assalaamu Alaikum Baban Sadik, ina fatan ba za ka gaji dani ba. Na yi karatu na ne a fannin fasahar “X-Ray”, amma kwanakin baya na ji wani likita a gidan rediyon BBC yana cewa, ma’aikata a fannin X-Ray ba su dadewa a duniya saboda mummunar illar sinadaran hasken lantarki, wato: Radiation.  Shin, mece ce gaskiyar wannan al’amari?  –  Ali Fancy, Garko, Kano: 08171748500.”

Malam Ali Fancy barka da warhaka. Amsar wannan tambaya za su samu ne daga bangarori biyu; na farko kan munanan illolin da ke dauke a cikin nau’in hasken X-Ray, wannan shi ne nau’in hasken da ke cikin fasahar na’urar gano cuta mai suna “X-Ray Machine.”  Bangare na biyu kuma shi ne neman tabbacin ko ma’aikata a wannan fanni suna fuskantar takaitacciyar rayuwa sanadiyyar illonin da ke cikin wannan sinadari na haske.  Amsa tambaya ta biyu kam sai kwararre kan harkar lafiya, kamar yadda ka ji wancan likita ya amsa.

Dangane da abin da ya shafi munanan illolin sinadaran kimiyya da ke cikin wannan nau’i na haske, lallai akwai su da yawa. Kamar yadda in kana tare da wannan shafi, ka ji bayanai cikin kasidar “Haske da Yadda Yake Samuwa,” da kasidar “Makamashi da Dukkan Nau’ukansa,” da kuma kasidar “Hasken Leza da Tallafinsa ga Fannin Likitanci.”  Har wa yau a cikin kasidar “Asali da Tarihin Makamin Nuiliya a Duniya” ma bayanai masu gamsarwa sun bayyana.  Sinadaran da ke dauke cikin wannan nau’in haske dai suna da illa matuka, ba wai ga ma’aikatan kadai ba, hatta ga wadanda ake haskaka jikinsu don gano illolin rashin lafiya da ke addabarsu. Duk da fa’idar da ke tattare da wannan fasaha ta “X-Ray” wasu daga cikin masana suna ganin illolin da ke cikinta sun zarce fa’idar, musamman ma ga jarirai, da mata masu juna biyu, da dai sauran masu lalura.

- Adv -

Kamar yadda rahoton babban taron koli na hukumar lafiya ta kasar Indiya ta tabbatar a shekarar 2008, wannan sinadari da ke cikin hasken X-Ray na dauke ne da manyan illoli ga jikin dan adam ta bangare biyu. Na farko shi ne zahirin jiki, inda hakan ke haifar da cutar sankara na jini, wato “Blood Cancer” ko “Leukemia.”  Wannan na cikin manyan cututtuka da idan har ta kama mutum ta ci shi, a karshe sai an masa dashen bargo don samar da sabuwar jini ga jikinsa. Rashin hakan kan iya salwantar da rayuwarsa, iya gwargwadon yadda cutar ta ci shi. Bangare na biyu kuma shi ne, muddin wannan sinadari ya shigi mace mai juna biyu, hakan na iya shafan jaririn da ke cikinta; ana iya haifarsa a karshe da wasu nau’ukan cututtuka masu illa, ciki har da cutar zuciya.

Wadannan kadan ne daga cikin illolin da ke cikin wannan sinadare da ke dauke cikin hasken nau’in “X-Ray.”  Don haka shawara a nan ita ce: ka je wajen likita don neman karin tabbaci, da kuma neman hanyoyin kariya, kamar yadda yake cikin ka’ida a ce tun a makaranta an karantar da ku wadannan hanyoyi.  Da fatan ka gamsu.


Salaamun Alaikum, Allah Ya kara basira Baban Sadik.  Yau kam na ganka zahiri kana bayani a Sunnah TV, kamar yadda muke karanta bayananka badinan a AMINIYA. –  Adam Umar, Abuja.

Wa alaikumus salam, Malam Adam, ina godiya matuka da addu’arka da na sauran ‘yan uwa da nayi ta samu ta shafin Facebook. Hakika hukumar talabijin tauraron dan adam ta Sunnah TV sun gayyace ni inda aka dauki shiri na musamman da za a ci dauki nauyinsa har na tsawon shekara guda, mai take: “Hanyoyin Sadarwa na Zamani.”  A kan sa shirin ne a kowace ranar Litinin, tsakanin karfe 10 zuwa 11 na dare, a maimaita ranar Talata.  A halin yanzu ana shiri na hudu kenan, kuma shirin zai ci gaba. Bayanai ne kan kwamfuta, da Intanet, da sauran hanyoyin sadarwa na zamani. Akwai masu sauraro a zauren shirin, wadanda ke yin tambayoyi kan bayanan da muke yi (ni da Malam Salisu Hassan Webmaster, sai mai gabatarwa).  Nan gama ana sa ran baiwa masu kallo damar rubuto tambayoyi da za a rika amsawa a duk mako in Allah ya yarda. Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.