Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (9)

Na'urar Sensor

A yau in sha Allah za mu yi bayani ne kan na’urar tantance yanayin da wayar salula ke ciki, na zahiri ko yanayin tsayuwanta ko yanayin mahallinta ko abin da take yi. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 29 ga watan Satumba, 2023.

223

Na’urar Tantance Yanayi (Sensor)

Makonni uku da suka gabata mun shagala ne da bayanai kan na’urorin dake ɗauke cikin cibiyar sarrafa bayanai na wayar salula, wato: “Mobile Phone Chipset”.  Wannan ɓangare, kamar yadda mai karatu ya karanta, na cikin manyan dalilan dake haddasa bambancin farashi tsakanin wayoyin salula, musamman na wannan zamani namu.

A yau in Allah Ya yarda za mu ci gaba da bayanin ragowan ɓangarorin dake haddasa bambancin farashi dai har wa yau.  Fa’idar kawo waɗannan bayanai shi ne taimaka wa mai karatu sanin waɗannan dalilai, da kuma fahimtar abubuwan amfani masu tasiri wajen ma’amala da wayar salula, da kuma tanadi don mallakar wacce mai karatu ke ganin za ta taimaka masa wajen cinma burinsa a rayuwa, mai alaƙa da wayar salula ko sadarwar zamani.

A yau in sha Allah za mu yi bayani ne kan na’urar tantance yanayin da wayar salula ke ciki, na zahiri ko yanayin tsayuwanta ko yanayin mahallinta ko abin da take yi.  Abin da wannan ke nufi shi ne, kowace wayar salula na zamani, iya girma ko ƙanƙantar mizaninta, tana ɗauke ne da wata na’urar dake iya sanar da ita ko alamta mata yanayin da mai wayar ke ta’ammali da ita.   Misali, idan ka kwantar da wayarka ta salula (Landscape mode), wannan na’ura na iya sanar da ita cewa an kwantar da ita.  Haka idan aka kira ka, sai ka amsa, da zarar ka yi yunƙurin kai wayar zuwa kunnenka don saurare da magana da wanda ya kira ka, wannan na’ura na sanar da wayarka ne cewa kana son amsa kira ne, ita kuma nan take sai kulle fuskar wayar.  Haka nan idan kana ƙoƙarin gano bigiren inda kake ta hanyar manhajar taswira (Map application), nan ma akwai na’urar dake sanar da wayarka  abin da kake son yi, kuma nan take za ta fahimci haka, sai ta taimaka maka wajen aiwatar da aikin, idan akwai halin yin hakan.

Wannan na’ura ita ake kira: “Sensor”.  Daga asalin kalmar “Sense” ne, wacce ke nufin “Iya fahimtar wani abu ko wani mahalli ta amfani da kafar shaƙa (hanci), ko fahimta (ƙwaƙwalwa), ko ji (kunne), ko gani (ido) da dai sauransu”.  Yadda kake iya fahimtar yanayin da kake ciki na tsayuwa, ko zama, ko kwanciya, ko ƙoƙarin tuna wani abu ko karatu da dai sauransu, haka ma wayar salula an sa mata ire-iren waɗannan ɗabi’u don ta taimaka maka wajen gudanar da rayuwarka da cinma burinka.

Wannan na’ura na tantance yanayi dai nau’uka biyar ne.  Ma’ana, sun sha bamban wajen aikin da suke gudanarwa a wayar salula.  Sannan akwai su birjik a wayoyin salula na zamani; iya girman waya, iya yawansu.  Amma duk yawansu, gaba ɗaya idan ka tara su suna ƙarƙashin waɗannan nau’uka ne guda biyar.  Misali, a wayar salulata nau’in Samsung Galaxy A24, akwai na’urar tantance yanayi ko senso guda 34.

- Adv -

A halin yanzu ga na’ukan waɗannan na’urori nan, wanda na san da yawa cikin masu karatu za su iya fahimtarsu kai tsaye.

Na’urar “Accelerometer”

Wannan na’ura tana girke ne a wayar salula, kamar yadda Allah ya gina ɗabi’ar fushi da fara’a a jikin ɗan adam.  Kuma aikinta shi ne lura da yanayin da wayar salula ke ciki wajen tsayuwa ko kwanciya.  Wannan shi ake kira: “Orientation mode”.  Ma’ana, idan wayar a tsaye take (Portrait mode), manhajojin dake buƙatar amfani da tsayuwa ko kwanciyar wayar salula suna iya gane a tsaye wayar take ko a kwance, kuma nan take sai su aiwatar da abin da aka gina su don aiwatarwa.  Misali, manhajar buɗewa da kallon hoton bidiyo na cikin manhajojin dake amfani da wannan na’ura ta Accelerometer.

Idan ka buɗe manhajar kallon bidiyo (Video app), manhajar za ta yi nazarin bidiyon da ka buɗe, idan a kwance aka ɗauki hoton bidiyon (Landscape mode), nan take wannan na’ura za ta sanar da manhajar, daga nan sai ta buɗo bidiyon a kwance.  Ko ka riƙe wayar a tsaye (Portrait mode), hoton bidiyon a kwance zai bayyana.  Haka idan hoton bidiyon a tsaye aka ɗauke shi, kana iya kallonshi a tsaye yadda yake, sannan idan ka kwantar da wayar salularka, nan take wannan na’ura za ta sanar da manhajar bidiyon cewa “Yanayin wayar ya canza zuwa kwanciya”, kuma ba tare da ɓata lokaci ba za ta bayyana maka saƙon bidiyon a kwance.

Haka nan duk wani abin da ke da alaƙa da jijjiga ko girgiza, wannan na’ura ta Accelerometer na taikamawa wajen aiwatar da ita.  Misali, akwai manhajar sauraren waƙoƙi (Music application) wacce idan kana son waƙar ta dakata, jijjiga wayar kawai za ka, nan take waƙar za ta tsaya.  Haka idan aka kira waya, akwai tsarin dake baka damar kife fuskar wayar, nan take ƙarar wayar zai katse.  Duk da wannan na’ura suke amfani.

Ba hoton bidiyo da manhajar sauraren waƙe ba kaɗai, hatta manhajar wasanni na wayar salula (Mobile games application), duk suna amfani da wannan manhaja ne wajen aiwatar da ayyukansu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.