Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (17)

Kamfanin Apple

A farkon lokacin da kamfanin Apple ya fara ƙera wayoyin iPhone, ya ƙera su ne da matakin mizanin ma’adana kashi uku.  Na farko su ne masu ɗauke da 16GB.  Sai masu biye musu da 32GB. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 24 ga watan Nuwamba, 2023.

223

Wayoyin Apple

Kamfanin Apple, wanda marigayi Steve Jobs ya kafa shekaru sama da 40 da suka gabata, shi ne yake ƙera wayoyin iPhone da sauran na’urorin sadarwa nau’in tablets masu suna iPad.  Bayan waɗannan, kamfanin na ƙera nau’ukan kwamfutoci guda biyu masu ɗauke da nau’in babbar manhajarsa mai suna Mac OS.  Nau’in farko kwamfutocin kan tebur ne, wato Desktop, masu suna iMac.  Sai nau’i na biyu mai suna MacBook, wadda nau’in laptop ce.  Amma kamar yadda na faɗa a farko ne, kamfanin Apple ne ke ƙera wayoyin salula nau’in iPhone, da dukkan zubinta.  Waɗannan na’ukan wayoyin salula ana ƙera su ne a mataki uku, ta la’akari da farashinsu.  Ga bayaninsu nan kamar haka:

iPhone Mini ko iPhone Regular

Kashi na farko ya ƙunshi nau’in iPhone mini ne, kamar yadda kamfanin Apple ya kira su a farkon zamanin da ya fara ƙera su.  iPhone mini su ne masu ɗauke da mafi ƙarancin siffofin nau’in iPhone ɗin da aka fitar a kowane lokaci ne, wajen girman fuska – sikirin – da mizanin masarrafa, da nau’in kyamara, da sauransu.  A taƙaice dai, ita ce ‘yar autar iPhone a kowane fitarwa ko zubin iPhone ne aka samar.  A farkon fitan iPhone ana kiranta da suna “mini” ne, wato “ƙarama”.  Amma daga kan iPhone 7 aka cire wannan laƙabi.  Sai dai aka bar sunan kawai.  Don haka, idan kace kana buƙatar iPhone 8, ko iPhone X misali, baka bambance ba, za a ɗauka kana nufin mafi ƙanƙantar ce.  Shi yasa wasu kan bambance a yanzu su kira ta da suna “iPhone X regular”, misali.  Wannan laƙabi ba kamfanin Apple bane ya baiwa wannan nau’i na iPhone, a a, jama’a ne.  Kamar dai yadda mutane kan sanya wa motoci sunaye da suka sha bamban da asalin sunan da kamfanin motar ya bata.  Kamar “Honda Hal”.  Ko “Honda Henessy”.  A rubuce ba za ka taɓa ganin wannan sunan a kamfanin da ya ƙera motar ba.

Dangane da farashi kuma, ko shakka babu wannan ita ce mafi ƙarancin farashi kuma mafi rahusa daga cikin dukkan zubin iPhone na kowane lokaci ne.  Saboda ita ce mafi ƙanƙanta wajen girman jiki.  Mafi ƙarancin faɗin fuska, wato sikirin kenan.  Mafi ƙarancin ma’adanar RAM.  A wasu lokuta ma mafi ƙarancin masarrafar sarrafa bayanan waya, wato: “Processor” kenan.  Ita dai mafi ƙarancin komai.  Abu ɗaya ne kawai wannan zubin iPhone ta haɗa da sauran ‘yan uwanta.  Wannan abin kuwa shi ne girman mizanin ma’adanar waya, wato “Internal Storage”.

A farkon lokacin da kamfanin Apple ya fara ƙera wayoyin iPhone, ya ƙera su ne da matakin mizanin ma’adana kashi uku.  Na farko su ne masu ɗauke da 16GB.  Sai masu biye musu da 32GB.  Sai kuma mafiya girman ma’adana, wato: 64GB.  A hankali, ta la’akari da ci gaban ƙere-ƙere a fannin sadarwa na zamani, da yadda galibin bayanan jama’a ke komawa kan wayoyin salula sanadiyyar dogaro dasu da ake yi wajen gudanar da rayuwa, sai kamfanonin ƙera wayoyin salula – ciki har da kamfanin Apple – suka ɗaga mizanin ma’adanar wayoyin salula ya zama mafi ƙaranci a yanzu su ne masu zuwa da 64GB.  Ɓangaren RAM kuma suna zuwa da mafi ƙarancin mizanin 2GB.  Amma wayoyin iPhone na yanzu kanzo da mafi ƙarancin ma’adanar waya ne a mizanin 128GB.  Ɓangaren RAM kuma 4GB mafi ƙaranci.  Wannan shi ne mizanin ma’adanar iPhone da kowane ɓangare ko kashi ke zuwa dashi.

Farashin wannan kashi na wayoyin kamfanin Apple yana farawa ne daga dala 700 ($700).  Kwatankwacin naira dubu 600 (N600,000) zuwa 700,000 (N700,000) kenan a Najeriya.

- Adv -

iPhone Pro

Wannan shi ne kashi na biyu na zubin iPhone a kowane lokaci aka fitar.  Misali, akwai iPhone 8 Pro.  Akwai iPhone XR, wacce ke matsayin iPhone 8 pro kenan.  Kalmar “pro” na iya ɗaukan ma’anar “Professional” ko kuma laƙabi ne kawai na martaba da kamfanin ke baiwa wayoyin dake matsakaitan mizani. Haka akwai iPhone 11 pro.  Da iPhone 12 pro.  Da iPhone 13 pro.  Da iPhone 14 pro.  Sai ta ƙarshe, wato iPhone 15 pro.  Waɗannan su ne matsakaita wajen girman fuska – sikirin – da girman mizanin ma’adanar RAM, da kuma matsakaicin mizanin masarrafar bayanai, wato “Processor” kenan.

Farashin wannan kashi na wayar salula kuma na farawa ne daga dala 800 ($800) zuwa 1,000 ($1,000).  Kwatankwacin naira dubu 750,000 (N750,000) kenan zuwa miliyan ɗaya a Najeriya.  Wannan kiyasi ne.  Ya danganci nawa canjin dalar Amurka yake a Najeriya.

iPhone Pro Max

Sai kashi na uku, wato “iPhone Pro Max”.  Wannan ita ce zubin wayar iPhone da ta ɗara sauran zubin wajen komai da komai.  Ta fi su faɗin fuska, wato sikirin kenan.  Ta fi su mizanin ma’adanar waya wajen sarrafa bayanai.  A galibin lokuta ma za ka samu tana ɗauke da wasu siffofi da sauran ba su dashi.  Wanna ita ce kankat, kamar yadda Bahaushen zamani ke siffata abin da yakai ƙololuwa wajen matsayi.  Wannan yasa tafi sauran tsada.  Galibin zubin wayar iPhone Pro Max dai farashinta na farawa ne daga dala 1,000 ($1,000) – kamar naira miliyan ɗaya kenan a farashin kasuwar dala na bankuna a Najeriya – zuwa dala 2,000 ($2,000).

Bayan waɗannan nau’ukan wayoyin salula guda uku, akwai wasu lokuta da kamfanin Apple ya ƙera wasu wayoyi da ya kira masu sauƙin farashi.  Waɗannan su ne nau’in wayoyin iPhone SE.  Karo na ƙarshe da kamfanin ya ƙera ire-iren waɗannan wayoyi dai shi ne bayan farfaɗowa daga matsalar korona.  Duk da kiransu masu sauƙin farashi, farashinsu na farawa ne daga dala 450 ($450), kwatankwacin naira 450,000 (N450,000) kenan.  Ta la’akari da tsarin farashin kamfanin Apple, tabbas waɗannan su ne mafi sauƙin farashin wayoyinsa.

Tambayar da mai karatu zai min a nan ita ce:  shin, kamfanin Apple na da wayoyi masu rahusa ne?  Domin cikin duk farashin da na faɗa a baya, babu wanda talakan Najeriya zai iya saya a ciki.  Domin mafi ƙarancin farashinsu shi ne rabin miliyan ɗaya.  Amsar wannan tambaya ita ce, ta la’akari da waɗanda aka ƙera musu wannan nau’in waya, kashin farko su ne na talaka.  Kashi na biyu, su ne na masu matsakaitan samu.  Sai kashi na uku da aka ƙera don masu hannu da shuni.  Wannan shi ne hasashen.  Amma a aikace galibin mutane a ƙasashen da suka ci gaba suna iya mallakar kowacce daga ciki, saboda tsarin sayan waya a bashi da suke dashi.  Wannan tsari shi suke kira “Contract”.  Amma a ƙasashe talakwa ba a cika samun wannan tsari ba.  Shi yasa ba a sa wayoyin iPhone cikin sahun wayoyi masu sauƙin farashi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.